NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 75 of 323

o bata dawo daga karatun da take ɗauka a wurin Amir ba ne shiyasa ma batai maganarta ba. ta zauna nan kusa da Kaka suna hira, Kaka tace,"ke ni fa tunda muka baro asibiti lissafin karɓar aikinmu ya kubce min, Yami bata ce miki komai ba?". Maijidda tace,"ku zaku karɓi na rana yau, amma naji kamar Yami na cewa ma yau ba za'ai girkin sadaqa anan ba, daga can masarauta za'a kawo". Kaka tace,"ohh ke haka ne fa, jiya Hajiya ta aiko a faɗa mana kinga na manta". suna hirar Maijidda na duba agogo tana kallon ƙofa da jiran shigowar Fillo, amma ganin har tara da rabi ta wuce bata shigo ba yasa tace da Kaka,"Fillo daga wurin karatun zata wuce aiki?". Kaka tace,"ai zatona faɗan ma dake akai da naga baki yi zancenta ba". Maijidda tace,"a'a ba muyi faɗa ba, me kika gani Kaka?". Kaka tace,"tun ɗazu fa ta dawo daga wurin karatun, tana shigowa ta shige ɗaka bata fito ba, Allah masanin fushin nata". Maijidda ta miƙe da azama tayi cikin ɗakin, tana shiga taga Fillo tsaye ta kifa kanta da bango, jikinta sai karkarwa yake yi. haka take ita, indai ranta ya ɓaci duk haƙuri da lallashin da za'a mata ba zasu yi tasiri ba sai tayi kuka ko kuma tayi masifa, idan ba haka ba ba zata huce ba, haka ba zata kwana a tsaye ne tana ta fizgar numfashi da karkarwar jiki, babu me iya controlling ɗinta. Maijidda ta kalli wayar hannunta dake ringing, tunaninta ko Dr Yusuf ne ya ƙara kira dan sau biyu yana yana kira a safiyar nan yana cewa ta haɗasa da Fillo tace masa bata dawo daga wurin karatu ba, to sai taga ma ba shi bane Amir ne. ta kalli Fillo ta kalli wayar, ya zatayi dole masifar dai akanta za'a juyeta ta sani, ai ba yau farau ba, tasan halin ƴar'uwarta, idan tana cikin irin wannan yanayin ko magana bata so ayi mata, ita kuma ba zata iya barinta haka ba tunda Kaka ba sauraronta za tai ba, in akai haka kuma Fillo da wartsakewa sai dai gobe. "Fillo wai menene?, wa ya ɓata miki rai?". Maijidda ta faɗa. Fillo tai shiru ba motsi balle amsa. ta ƙara cewa,"to kiyi haƙuri kinji, fushi fa na abokan sheɗan ne, ki zauna muyi kukan tare to, ni bana son ganinki a haka Allah". Maijiddan ta faɗa in breaking voice. nan ma dai babu amsa babu motsi. hakan yasa Maijidda ta dafata,"ni ce fa nake baki haƙuri Fillo, Hassanarki, Hussaina Hassanarki ce fa, ko kina so na mutu ma barki ke ɗaya?". Maijidda dai kamar me magana da gawa ko kuma gunki, ta yarfar da hannu kamar zatai kuka, ta ƙara kallon kiran Amir dake shigowa a karo na uku, ta dafa kafaɗar Fillo zata juyo da ita tana cewa,"kinga fa Amir ne ke ta kiranki, kar...". ai bata ƙarasa ba Fillo ta ɗago a harzuƙe cikin fusata tai wurgi da hannun Maijidda dake kan shoulders ɗinta, wayar Yami ta faɗi a ƙasa ta wargaje, ƙashin hannun Maijidda yay wata ƙara kamar an karya shi. a zafafe kuma cikin amon muryar da ya cika ɗakin Fillo ta ce mata,"dilla Malama ki rabu da ni, ki ƙyaleni, babu ruwanki da ni, ki matsa daga kusa da ni in ba haka ba duk abinda na miki ke kika jawa kanki". tana faɗin hakan kuma sai ta fashe da kuka, Maijidda cikin jin zafin hannunta ta matso ta rungume Fillo, sai suka durƙushe a ƙasan wajen, sosai Fillo ke kuka Maijidda kuma na tayata, Kaka dai na daga falo tana jinsu bata bi ta kansu ba. sai da aka ɗan ɗau lokaci sannan Fillo ta fara samun sauƙi cikin ranta, har daga ƙarshe ma ya zama ita ke lallashin Maijiddan. itama kuma a sannan sai taƙi yin shiru, taci gaba da zubar da hawayenta a kafaɗar Fillo. Fillo na shafa bayanta tace,"ke Hassana wai mene haka, ki daina mana". Maijidda tace,"to ai kece, na faɗa miki bana so kike bari Shaiɗan yana tasiri akanki akan fushi". Fillo tace,"to ba na daina ba, idan kuma ba zaki shirun ba sai mu ci gaba dan kin san dai ba zan zuba ido kina kuka ina zaune ina kallonki, zuciyata ba zata ɗauka ba". Maijidda tace,"nima ai baki saurareni ba a farko har ma kika ji min ciwo". ta faɗa muryarta na daɗa bayyana kukan da take yi. muryar Fillo ta karye tace,"to kiyi haƙuri, idan kuma ba zaki daina ba shikenan sai mu fasa auren miji ɗayan". sai a lokacin Maijidda ta ɗago suna gogewa junansu hawaye, Kaka na daga falo tace da su,"ke Maijidda kin san dake za'aje gidan sarki ko, ke kuma idan kinga dama ki fito kije kiyi musu aikinsu, in ba za ki ba kuma ki faɗa min sai na miƙe". Fillo tace,"to Hajiya Kaka gamu nan". sai da zasu fita sannan suka lura da aika-aikar da suka yiwa Yami, Maijidda tai salati tana rufe baki da faɗin na shiga uku. Fillo tace kin shiga uku ko mun shiga uku, yau akan akwalar wayar nan Yami ba sai ta cinyemu a ɗanyanmu ba. Kaka da ta jisu tace,"zan kuwa faɗa mata". hannu na rawa Fillo ta ɗau wayar tana haɗeta suka fito falo. "yanzu Yami sai tace mun cuceta mun datse hanyar da zasu ke gaisawa da bazawarinta". Maijidda ce ta faɗa, Kaka tai dariya, Fillo dai duk ta tsure sai ɗaure kyauraye takeyi, fatan ta ɗaya tana ɗora batirin wayar ta tashi. bakinta faɗi yake,"kece me Jidda ki kai magana da ƙarfi, da Kaka bata ji ba ai sai mu aj
🏠