da ta iso wurin ta sakar masa nata sanyayyan murmushi da yake motsa zuciyarsa. ta durƙusa a gabansa ta gaishesa.
Ya amsa yana kasa ɗauke ido daga dogayen yatsunta da ta rufe fuskarta da su, murmushinsa na ƙara faɗaɗuwa. sai da yay gajeriyar ajiyar zuciya sannan yace,"Barka da fitowa gimbiyar Amir, sarauniyar da ta kafa fadarta acikin zuciyar Amir, kazalika uwar ƴaƴan Amir".
ta ƙara rufe fuskar da hijab ɗinta, wani daɗi na ratsata. Yay ƴar dariya yana jin tana ƙara burge shi saboda wannan kunyartata.
yace,"duk da an hanani ganin fuskar hakan ba zai hana ni faɗin kinyi kyau sosai, matsalar guda ɗaya ce dai da bana so".
ya ƙarasa maganar amon muryarsa na sauyawa, tai saurin buɗe fuskarta, so take ta kallesa amma ta kasa, ta sauke idanuwanta a ƙasa da rashin jin daɗi tana jan yatsunta tace,"wacce irin matsala ce?, mecece matsalar da baka so?, a shirye nake da gyara ko menene saboda kai?".
ya murmusa kuncinsa sannan yace,"Kunya! itace matsalar kuma itace bana so, amma a iyaka tsakaninmu banda wani daban, sai dai na san ba zaki iya dainawa ba balle ki rage, tunda ba tun yau ba nake roƙon alfarmar a rageta ko ya ya ne saboda tana ƙwarata, amma kamar ma ba'a jin me nake cewa...ni kuma tsakani da Allah ina so ake a bani damar ganin cikin idanuwan gimbiya, ina sonsu, so me yawa ba kaɗan ba".
Fillo na murnushi ta ƙara ƙoƙarin sake rufe fuskar sai taga ya haɗe hannayensa alamar roƙo yace,"dan Allah Fillo nah, ki tausayawa zuciyata, ki tausayawa idanuwana".
haka dole ta haƙura da rufe fuskar, ba zata iya saka ƙwayar idonta a cikin nasa ba, amma ba zata hanasa ganin fuskarta ba, dan haka ta ɗago kai yanda zai kalleta sosai, amma bata iya barin idonta a buɗe ba ta kullesu.
sai da Amir ya ɗauki kusan minti ɗaya yana kallon fuskarta ba tare da ita tai magana balle shi da ya shiga shauƙi. da yana da dama, da yana da yanda zaiyi da yau Fillo bata ƙara kwana a gidan nan ba, da yau Fillo a gidansa zata kwana, kusa da shi, kusanci sosai irin kusancin da zai ɗorata a saman ƙirjinsa ya dinƙa faɗa mata kalaman da zasu mantar da ita duk wani kalar ƙalubale da ta fuskanta a rayuwarta.
"ina sonki, ina miki so me tsanani, ƙaunar da nake miki ba mai fasaltuwa bace, bana fatan na rasaki Halimatu, bana fatan Allah ya kawo abinda zai rabani da ke, ke ɗaya ce tal a ƙurya da wajen zuciyata. please ki so ni ko da kwatankwacin yanda nake sonki ne, domin idan babu ke tare da ni Allah babu makawa sai na zama gawa".
tai saurin ɗago ido ta kalli raunanun idanunsa. "ina sonka ai kaima kasan da wannan, kuma ba zamu rabe ba insha'Allahu, matarka ce ni har a aljannah insha'Allahu". haka ta faɗa, kuma hakan ke maimaituwa a cikin ransa, maimaituwar kuma ke haifar da jin daɗi tare da shi.
da taga kamar yau bai da niyyar suyi karatun muryarta a sanyaye tace,"yau ina da aiki a cikin gida".
take annurin fuskarsa ya ɗauke, ya haɗe rai ɓacin rai na ziyartarsa. ya miƙe kawai ba tare da yace mata komai ba ya nufi inda suke zama suyi karatun, baya son wannan aikin nata ya tsane shi. ko wannan karatun da ya tsira yi mata, yayi hakanne dan ya daƙile mata zuwa aikin shi yasa ya saka da safe zasu ke yi, amma ashe na banzar yayi, kamar mayu sun liƙe ita zata ke musu aikin, yanda baya so tai aikin haka baya so Kaka tayi, to amma baida yanda zaiyi, shi ba me ƙarfi ba ne, idan ita ya nemi hanyar hanata bai isa ya hana Kaka tayi ba, to amma me yasa ba zasu nemi wata yarinyar da ta dinga yi musu ba?, su bar masa Fillonsa ta huta kamar a baya.
Fillo ta ƙaraso jiki a sanyaye ta shimfiɗa masa dardumar, sannan ta shimfiɗa ɗankwalinta ita kuma ta zauna akai, har sanda ta zauna shi yana tsaye kamar ba zai zauna ba, ita dai bata ɗago ta iya kallonsa ba, saboda hawayen cikin idonta zasu sami nasarar zubowa, ko kaɗan bata son ganin ɓacin ransa, musamman ace itace sila.
sai da ya zauna sannan tace da shi,"kayi haƙuri, dole ce tasa ba dan muna so ba mu kanmu. aikin nan shine rufin asirinmu, kana gani Kaka daɗa tsufa takeyi jikinta na ƙara saki, ba zata iya ɗawainiyar da tayi a baya ba, ni kuma da ta riƙe ni bayan banda kowa dole na taimaka mata a yanzu dana kawo ƙarfi, tana buƙatar taimakona. kuma yanzu idan banyi aikin nan mun sami kuɗin ba da me kake so Kaka ta kaini gidanka Amir?".
ya tsayar da ƙwayar idonsa akanta yace,"ni ke nake so ba abinda za'a kai ki da shi ba". ta girgiza kai tace,"a'a Amir, duk da bamu da komai, kuma ni ɗin ba kowan kowa bace, amma ina so na wuce gori a ko ina ne. kuma baya nan ina so ko bayan ran Kaka na kalli wani abin da zan gani naji daɗi, na san nima an tafi an bar min gado".
yace,"shikenan, bismilillah". ya faɗa yana mata alamar ta fara karatun.
tasan maganarta bai masa daɗi ba amma dole ta faɗa, kuma gaskiyar kenan. ba'a san gawar fari ba, kuma ba fata take ba, amma idan Kaka ta mutu, shi kuma ta aure shi shima ya faɗi ya mutu rabo bai samu a tsakaninsu ba, wa take da shi kuma me zata kama?, gwara tai duk kalar wahalar aiki tayi su sami