NOVEL SHARES -
ƴaƴa?, kaga kuwa ba zata ƙare rayuwarta haka bata nemi ta koma garesu ba, ku dai kuci gaba da bata kulawa da taimaka mata, Allah ya baku lada".
a tare suka amsa da,"amin ya Allah Daddy". shiru ya gifta a parlon, Yusuf na taraddadin yanda zaima Ammi maganar tafiyarsu. da Daddy yaga shirun yay yawa ya katse abinda zuciyar kowa ke saƙawa yace,"or do you need anything?".
Yusuf yace,"a'a Daddy, dama zamu tafi ne". yace,"ok ba anan zaka barta ba?". ya ɗan sosa ƙeyarsa da kunya yace,"ehhh Daddy". Daddy ya kaɗa kai yace,"alright to ku tashi haka dare nayi, amma dai ita da ka barna nan cikin ƴan uwanta ai yafi ka tafi da ita wani hotel".
Yusuf yace,"da yake zamu je asibiti ne da safe". Daddy yace,"to yayi, Allah bada lafiya. ku tashi haka".
Yusuf na kallon Ammi wadda ke zaune tana jinsu amma kamar ma hankalinta baya garesu, ta haɗe girar sama da ƙasa ta ɓata rai.
yace,"Ammi zamu tafi". yana faɗar hakan Nuratu ta ɗago ido ta kalleta, yanda taga Ammi ta taɓe baki taji kamar an soka mata kibiya a ƙirji. Yusuf ya miƙe tsaye ita kuma ta rissinar da kai tana cewa,"mun gode Ammi da Daddy, Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana me amfani".
daga haka suka fice daga parlon zuciyar kowannensu babu daɗi.
****
"kin tabbata ba kya jin ciwon komai?". Yusuf dake tsaye a gaban gadon Fillo ya faɗa, yayinda wata nurse dake kusa da shi ke riƙe da file.
Fillo tace,"bana jin ciwon komai Dr". ya jinjina kansa, ya karɓi file ɗin hannun nurse ɗin yay rubuce rubucensa.
ya ƙara cewa,"gobe da safe insha'Allahu zamu sallameki, Allah ya ƙara lafiya".
Fillo ta amsa da amin sannan ta ɗago ido ta kallesa, ƙwayar idonsu ta sarƙe ana juna, Yusuf yaji zuciyarsa ta girgiza, yasan akwai kamanni, amma bai taɓa zaton cewar akwai tsananin kamannin da suka kai irin haka ba bayan na wanda suke identical 2wins, a tare da wa zaisa kamannin yarinyar nan?, idon, fuskar, yanayin komai iri ɗaya ne, sai dai ya rasa iri ɗaya da na waye, tunaninsa da hasashensa ya gaza basa.
yayinda a wannan lokacin zuciyar Fillo ke ƙara faɗa mata tabbas tasan wannan fuskar ta Yusuf, sai dai ta kasa tuna aina ne, aina ta taɓa ganinta?.
_Comment ɗinku shine ƙwarin gwiwata, rashinsa shi yake sawa na hutar da kaina._
*dont forget to share, comment and vote.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*20*
bayan sati ɗaya jikin Fillo ya ƙara yin sauƙi sosai, yarinyar har wani fresh tayi hasken fatarta ya ƙara fitowa saboda kwanciyar da tayi a asibiti me kyau, da kuma irin cimar da take ci me rai da lafiya. na musamman Hajiya Madina ke yin lafiyayyan girki a kai mata, girkin da zai ji ganyayyaki masu ƙara lafiyar jiki da kuma hanta acikinsa, tunda aka kwantar da ita duk wani abinci da zata kai baki da hanta take yin lomarsa, fruite salad kam da bata taɓa shansa ba sai da ya ginsheta. kuma tunda suka dawo bata ci gaba da zuwa aiki ba sai Kaka ce ke yi, Hajiya Madina tace ta ƙara samun hutawa na sati ɗaya sannan sai taci gaba, har wannan lokacin kuma bata san Turaki ne ya kaɗeta ba, duk zuwan da yake yi akai akai zatonta halin karamci ne kawai irin nasu.
sa fiya ce yanzu dan ko takwas da rabi bata yi ba, Kaka na daga falo tana sauraren Shaik Ibrahim Daurawa a radio, Fillo kuma na ɗaki tana shiryawa.
Kaka tace,"wai ba zaki fito ki wuce ba ne?, kullum sai kin ɓatawa bawan Allah lokaci Fillo, Allah raina yana ɓaci da wannan abin naki".
daga inda Fillo take ta ɗan gwame fuska tace,"Kaka fuskar hijab ɗin ce fa ta yage shine nake ɗinkewa". Kaka tace,"uhm haka dai kike kullum da uzurin da zaki bayar, to ki bar ganin saurayinki ne Allah sai nace ya fara yi miki bulalar makara, wataƙila ki fi maida hankali akan karatun".
dariya kawai Fillo tai bata ce komai ba, amma har hangowa take wai Amir zai daketa, tana sonsa dan haka ba zata ƙi tsayawa ba amma shi ɗin tasan ba zai taɓa iyawa ba, ko wani me gangancin yaga zai gwada sai iyakar inda ƙarfinsa ya ƙare.
ta fito daga ɗakin sanye da hijab ruwan toka, hannunta kuma tana riƙe ne da qur'ani izu sittin ta rungume shi a ƙirjinta haɗe da dardumar sallah.
"na tafi Kaka". Kaka ta ɗago ta kalleta tace,"Allah ya bada sa'a, amma ku gama da wuri kinga Hajiya Madina tace ki koma aikinki yau, kya gaida Amir ɗin kice ina daɗa masa godiya Allah ya jiƙan mahaifa". tace,"tom Kaka". da haka ta fice.
daga can bakin gate wurin da ya saba zama ta gansa, a durƙushe a ƙasa da alama ya gaji da tsayuwa ne. bakinsa na motsi yana latsa counter dake saƙale a yatsansa, baƙin yadi ne a jikinsa mai taushi mara tsada wanda ya karɓi jikinsa sosai. ya kuma fito da kyawunsa na usulin bafulatani, sumar nan tasa kwantacciya ta fulani tai luff sai ƙyalli takeyi, da takalminsa da agogonsa dai-dai na me rufin asirin ubangiji.
tunda ya ɗaga ido yaga Fillo na tahowa zuwa gare shi kyakkyawan murmushi ya ɓalle a saman fuskarsa, zuciyarsa na ƙara cika da tausayi da soyayyar Halimatunsa, ruhinsa na ƙara buƙatuwa da ƙwaɗaituwar ta zama mallakinsa.
a lokacin