ina zuwa i will call you letter". ta faɗa tana aje wayar a gefen gadon.
"Anty Nuratu ai babu abinda kika sha, gaskiya ni dai ki daure ki ƙarasa shanyewa". Nuratu kamar za tai kuka tace,"na ƙoshi Yusra".
haka dai har sai da Yusra tasa ta ƙarasa shanyewa, a lokacinne Yusuf ya shigo, tana ganinsa kuma tasa kukan shagwaɓa, kamar wanda aka zarewa laka ya ƙaraso ya zauna a bakin gadon.
Yusra ta gaida shi ya amsa murya a ƙasa, ya janyo Nuratu jikinsa yana shafa kanta yana lallashinta.
ba tare da ya kalli Yusra ba wace,"what did she eat?". Yusra tace,"yanzu ta gama shan fruite salad". ya sake cewa,"ki gasa kaza ki kawon yanzu". "tom Yaya". ta faɗa tana fita daga ɗakin.
Nuratu kuka ta ƙara sawa tana faɗa masa,"Excellency ni na gaji da wannan cikin, plss remove it for me".
bai iya cewa komai ba ya rufe idonsa ya ɗora haɓarsa akan gashinta, hannunsa na kan cikinta yake bata haƙuri. ji yake da damar da zai mayar da cikin jikinsa da ya maida, tunda ta sami cikin nan bata huta ba, kullum a cikin wahalar laulayi take, ga shi yanzu aka fara ba'aje ko'ina ba, cikin ko 4 months bai kai ba.
"ki daina kukan nan please". ta ƙara narkewa a jikinsa tace,"ka kira min Umma". ya ɗauko wayarsa a aljihu ya kira Umman ta vedio call, idon Nuratu na kan wayar tana jiran ɗagawarta.
daga can ɓangaren Umma na kitchen lokacin ta ɗaga kiran, kallo ɗaya taima Nuratu ta hangi tarin kukan da idonta yasha ayau.
da tsananin tausayinta tace,"what's wrong Nuratu?". "Umma ki dawo dan Allah, ki dawo ki kaini a cire min wannan cikin bana sonsa, na haƙura da samun Bilal ɗin".
Umma ta sauke numfashi tace,"a'a Nuratu ba'a faɗar haka, babbar ni'ima ce fa Allah yay miki da ya azurtaki da samun cikin nan, wasu na nan basu samu ba suna cikin damuwa. adu'a kawai za ki Allah ya yaye miki wahalar laulayi ya kuma sa ki haihu lafiya. kar na kuma jin kince ba kya son cikin nan kinji ko".
Nuratu ta ɗaga mata kai alamar taji, tana kwance a jikin Yusuf har lokacin, ko kunyar Umman basa ji.
Umma ta kalla Yusuf wanda hankalinsa baya wajen, ta ƙara cewa. "am coming back next tomorrow insha'Allah, zuwa yamma in Allah ya yarda na dawo gida, ki daina kukan ya isa haka...irin wannan wahalar Mamanki tasha fama da ita lokacin da tana da cikinki, kamar ba zata rai ba, me ciki dama sai tai haƙuri ta jure".
sun jima suna wayar Umma na lallashinta da kwantar mata da hankali kafin su yi sallama. sai magriba Yusuf ya fito daga ɗakin su Yusra shi da matarsa, har lokacin Ammi bata san cewar suna ɓangarenta ba.
yasa Yusra ta kai kayan Nuratu motarsa, ba zai iya barinta a gidan ba tunda Umma bata nan, Inna Wuro kuma ta gaji, Ammi kuma ba sauraronta zatai ba, sisters nasa kuma kowacce na busy da study nata ba zai yiwu ya takura musu ba.
so is better ya tafi da ita can hotel ɗin da yake kwana su kwana for 2days ɗin da ya rage masa ya koma aiki kano, in yaso sai yasa wata nurse din ta ke lura da ita.
hannunsa riƙe da nata sukai parlon Daddy, sai da zasu shiga ya saketa, shi ya fara shiga sannan itama ta shiga. Daddy na zaune akan carpet lokacin, Ammi na kan kujera suna hira da shi, Daddy ne ya amsa sallamar tasu Ammi kam har ta buɗi baki zata amsa ganin Nuratu yasa tai shiru ta amsa a ciki.
daga baya suka tsuguna dukansu, bayan Yusuf ya gaida iyayen nasa Nuratu ma ta gaishe su, Daddy ne kawai ya amsa mata, jikinta taji yay sanyi tasa hannu ta goge hawayen da ya zubo mata a lokaci ɗaya, har ga Allah bata son wannan ƙiyayyar ta uwar mijinta, kuma duk duniyarta idan aka cire mahaifiyarta aka cire Umma babu macen da take so irin Ammi, ko da ace ba ɗanta take aure ba tana son Ammi saboda tana ɗaya daga cikin mata da suke burgeta.
Daddy ya kalle su yana smiling yace,"my daughter i hope there is no worries?". kan Nuratu a ƙasa a ladabce tace,"babu Daddy". yace,"to Allah yayi muku albarka, ya ƙara muku zaman lafiya da kwanciyar hankali, ya kuma rabaki da cikin jikinki lafiya". ita ta amsa a hankali Yusuf ya amsa da ƙarfi. Ammi dai tun amsa sallamarsu bata ce komai ba.
Daddy ya ƙara cewa,"ina mara lafiyar da kace kuna ruƙo a wajenku?". Yusuf yace,"tana can gida muka barota, There was a widow's nurse who took care of her zuwa mu koma gida".
Daddy yace,"but kana following situation ɗin da take ciki ko?". yace,"ehh Daddy, ko ɗazu ma munyi vedio call da ita, magana ce dai har yanzu bata yi amma she is getting better".
Daddy yace,"masha'Allah, Allah ya bata lafiya, amma har yanzu baka sa cigiyar ƴan'uwanta ba ne?".
Yusuf yay ɗan jim kamin yace,"ehh Daddy banyi hakan ba tukunna, saboda kaga ba mu san ma daga inda take ba, and if mukai mata zancen da ya shafi ƴan'uwanta da kuma inda ta fito, her mood was changing a lokaci ɗaya sai ta shiga state of frenzy, so thats the reason yasa muka daina mata maganar gaba ɗaya".
Daddy yace,"Allah ya kyauta, Allah masanin gaibu, but there must be something about her gaskiya, kuma ko menene lokaci zaizo da zata biɗi komawa inda ta fito, kace da dukkan alama tana da