NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 70 of 323

azo, nai zaton ai ko ka zama tarihi da nake ta danna maka kira kana ƙin ɗauka. baka san ni ba wata tsiyar zance kayi min ba, idan ka manta na tuna maka ɗana me wannan ƙaton gidan ya tara abinda kai baka da shi, dan haka nafi ƙarfin roƙo a wurinka Yusuf". tasa ƙafa ta tura masa duka trollys ɗin gabansa tana cewa,"gasu nan, dama niyya nake na fita da su na ajiye su daga bakin ƙofa sai kuma Allah ya kawoka ka rage min aiki". Yusuf dai kallonta kawai yake yi, sai da tai shiru sannan yace,"kiran da kika min na mene?". jin yanda yay maganar ta ɗago ido ta kallesa ta taɓe baki sannan tace,"naga duk ka firgice kamar wanda ya tsarewa zaki. to ni dana kiraka ce ka ke me ya faru?, kasan dai haihuwa ba yanzu ba. gani nai nayi na Allah nayi na Annabi, to na gaji da rainon cikin da ba ni nayi ba, shi yasa na doka maka kira kazo kai awon gaba da ƙazamiyar matarka, ba zan iya da tofe-tofen yawu da amai ba, duk ta lalata min wuri da ƙarni. kai baka ji ba daka shigo?, ko da yake yanzu yarinyar can me aikin babarka tasa omo da turaren ƙamshi ta goge min ko'ina, wallahi da ba zaka iya shigowa ba daga bakin ƙofa zaka tsaya, amma matarka ai bata haɗu ba yasin, ciki sai kace akanki aka fara, sakan ɗaya biyu sai a tofar da yawu, can kuma sai dai kaji ana kyalayo amai". ta rufe ido ta dafe goshi tace,"wuwuwu abin dai ba kyan gani da kwatance". ran Yusuf idan yayi dubu ya ɓaci, idan da tasan muhimmancin aikin da tasa ya baro da bata masa haka ba. yaji kamar ya bige ta dan takaici, ya matsar da trolly ɗin gefe ya shige ɗakinta, yana shiga ya fito yana tambayarta ina Nuratun?. "yo ni ina nasan ma inda take, wannan dai fitsararriyar ƙanwar taka ita tazo ta ɗauketa bayan ta gama karta min rashin kunya...yo tsakani da Allah ina gani zan cutu kuma sai naƙi yin magana?, ƙarnin yawu da amai ne fa ke neman halaka ni. banda ma dai halin butulci irin na ɗan adam ina wani zai kallen ya gurza min baƙar magana, to akan Nuratu dai idan ba'a gode min ba ba za'a tsine min ba sai dai idan kuma son zuciya, wane zai iya ɗawainiyar da nai da ita, ce nake ita kanta ƙanwar Uwartata da aka kawowa ita guduwa tai ta barta ta wani fake da ta tafi umarah. haka nake hana idona bacci saboda yarinyar nan, tana bacci ina gefenta ina tofa mata duk kalar adu'ar da ta zo bakina gudun kar a haifi ɗa mara ƙafa, tunda naga alamar tana da mutanen ɓoye, Allah na tuba mene jinnu basa iya aikatawa sai dai Allah yay mana katangar ƙarfe da su kawai...ita dai waccen ƙanwar taka in kaje ka faɗa mata ɗibar albarkar da tai min taje dan kanta ni ba ramawa zanyi ba, kuma ba zanyi Allah ya isa ba tunda dai ina da hankali". Yusuf ya ɗauke idonsa daga kanta yaja trollys ɗin zai fice daga parlon kukan Inna Wuro ya dakatar da shi. ya juya yana kallonta da mamaki, kuka takeyi sosai tana faɗin,"wallahi karka daɗa karka raga ni ko zagin matarka banyi ba, kawai na gaji da ƙazantar ne na tofe-tofen yawu da amai shi yasa nace ta bar min wuri, kuma inda ace ta ban haƙuri ai zan haƙura, amma da yake butulu ce sai dai ta kalleni ta fashe da kuka duk dan wani ya ganta taja min masifa, nace to ta fita ta zauna daga bakin ƙofa idan kazo ba sai ka shigo min ciki ba tafiya kawai zaku yi, ashe taji haushi sai ta faki idona ta dannawa ƴar dabar gidan nan waya, ko minti ba'a ƙara ba sai gata kamar kububuwa ta faɗo parlon nan tana ta huci, da ace ban matsa baya ba da yanzu akan gawata kake tsaye, baka ga irin ɗiban albarkar da Yusra tai min ba, karka ji irin zagin da ta dinƙa surfa min Yusuf, harda kalar zagin da ban taɓa ji ba tunda uwata ta haifeni, wai akan matar Yayanta ba abinda ba zata iya ba, da zasu fita fa sai da ta bangaje ni, nai galantoyi zan kife a ƙasa bangon nan ya riƙeni, yo ka faɗa min ina zan manta da wannan cin mutuncin?, har da cewa fa idan an haifi yaron nan ba zan ɗauke shi ba sai dai kallo daga nesa, to dama ita ta haife shi?, matsalar ban iya haɗa husuma ba ne dana kai ƙararta gaban Amadu wallahi, amma duk da haka ka sanar mata inuwarta na ƙara gani a ɓangarena sai na buga mata duk abinda na raruma". Yusuf bai ce mata komai ba ya fice ya barta tana kukanta. sai da ƙyar Aliyu da ya shigo ya iya lallashinta tai shiru, amma har sannan bata bar maimaita maganar ba. Nuratu na kwance akan gado Yusra ta shigo ɗakin nasu, ta ajiye bowl ɗin dake hannunta akan dressing mirrow sannan ta isa gadon ta miƙar da Nuratu wadda duk jikinta yay weak, pillow ta saka mata ta jingina da shi, tukunna ta koma ta ɗauko bowl ɗin dake ɗauke da fruite salad da ta haɗa mata. "Anty please ki daure ki shanye wannan duka, kinga dai cikinki babu komai". Yusrah ta faɗa tana me cike da tausayinta. Nuratu ta karɓa tasa spoon ta fara sha, sai da ta kusa shanyewa tukunna ta ajiye, tunda ta tashi yau babu abinda ta iya ci, duk abinda tasa a baki baya zuwa cikinta yake dawowa, tayi amai yafi sau biyar, shi yasa Inna Wuro tace yau ba zata iya ba. Yusrah na waya da saurayinta da ta kalla ta ajiye bowl ɗin ta taso. "
🏠