NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 7 of 323

ya mana baya"._ -Da Bafaden da ɗayar matar sukai tsaki a tare. "to idan kin shirya rasa ranki da kuma dubu ɗari biyar ɗin da za'a baki kina iya juyawa ki tafi, mu ki barmu muyi aikinmu...akan kuɗi da kika ganmu babu kasadar da ba zamu iya ɗauka ba"._ _suna rufe baki Bafaden ya durƙusa ya shiga haƙe ƙasar dake wurin, wanda bai tsaya ba har sai da yayi rami mai ɗan zurfi tukunna. Sannan macen da bata da tsoron ta ɗauko gorar ruwa acikin jakar dake hannunta ta juye ruwan acikin ramin. Sannan miƙa hannu ta karɓi wata baƙar leda a hannun ɗaya matar ta zira acikin ramin. Duk abunda suke yi suna yinsa ne cikin saurari-sauri gudun kar azo a gansu._ _Kuma bayan sun maida ƙasar ne sun rufe suka tsaya suna tattaunawa, wanda yanzu da suke maganar Fillo bata jiyo komai da suke cewa saɓanin maganganun da sukai a ɗazu duk ta ji su._ _Alokacin zuciyarta na faɗa mata ne ta tunkari inda suke dan su san wani fa ya gansu, amma ɗayan ɓari na zuciyarta na hanata aikata hakan gudun karta fito suyi mata illa, duk da bata ga fuskar ko guda acikinsu ba amma tasan ba mutane bane masu imani a zuciyarsu ba._ _Cikin gudu mai kama da sauri suka bar wajen, sai da ta tabbatar sun bar wajen sannan ta fito, sai dai ko da taje wurin juyin duniya ta kasa gane inda akai haƙan aka binne, dan babu wata alama ta ɓurɓushin ƙasa da zai nuna maka anyi haƙan ƙasa a wajen, wannan ya nuna mata sun ƙware a iya aikinsu, kuma ba yaune farau ba._ _Ta ɗau kusan minti guda tsaye a wurin tana tunanin abinyi sai kawai taji gabanta ya yanke ya faɗi, ƙirjinta kuma na bugawa sosai, zuciyarta na faɗa mata tai hanzarin barin wajen tun wani bai zo ya ganta ba, dan idan akazo aka kamata ta ina zata fara bayani?, waye zai wanketa daga duk wani kalar zargi da za'a ɗora akanta?, gatanta Allah gatan ta Kaka, bata mantawa da lokacin da ɗaya daga cikin yaran gidan yaci abinci yayta amai ba, akace ai mai aikin data kai masa abinci ce ta saka masa wani abun, idan har yanzu tunaninta na jikinta, to ai ba zata manta ba tsawon shekara guda da akai abun har yau mai aikin tana cikin kurku a kulle akan laifin da ba'a da tabbacin ta aikata shi._ _Saboda haka bata san lokacin da siraran ƙafafunta masu kama da sillan kara suka bar wajen ba cikin sauri kamin daga bisani kuma ta haɗa da gudu, sai dai a lokacin da ta ke shirin barin harabar wajen gaba ɗaya tai tuntuɓe da dutse, ta tsuguna domin ɗaukewa kawai sai tai tozali da laya da kuma wata leda baƙa daure a wurin, cikin kanta bata kawo tunanin komai ba tasa hannu ta ɗauki layar da ledar sannan ta janye dutsen daga wurin._ _A wannan lokacin kai tsaye ɓangarensu ta koma, ta zauna ita ɗaya dan kowa yana can masarauta anata hidimar bikin naɗi, ita kuma duk tsoron kar ta fito a ganta ita ɗaya acikin godan a fara yi mata tambayar tuhuma. A ranar ma haka dole ta kashe haɗuwarsu da Amir._ "wai tunanin me kike?". Maganar Maijidda ta dawo da ita cikin duniyar zahirin da ta bari tsawon daƙiƙu masu yawa. Kallonta kawai tayi ba tare da tace da ita komai ba. "Fillo kin san fa wurin nan ba wajen zuwanmu bane, ɓangaren masu gida ne. Amma kin kawo mu kin ajiye salon azo aganmu ace wani abun muke ƙullawa". "Maijidda wuta zamu cinnawa wajen nan". Maganar ta Fillo tasa Maijidda zaro ido waje tare da hanzarin miƙewa tsaye. Da yake ita sarkin tsoro ce tuni jikinta ya hau makyartata. Kuma bata kai ga ƙara magana ba, Fillo ta kai hannu ta ɗau ƙaramar galan ɗin petir ɗin da suka sato acikin gida ta shiga yaryaɗawa a wurin. Sai da ta juye shi tas sannan muryarta ta fito a hankali da cewar,"Maijidda matsa baya". Cikin tsoro ba tare da mamakin abunda Fillo zata iya aikatawa ba tace,"ke wai me yasa ba kya iya kallo matsalar da zata faru a gaba, ke kawai abunda yazo cikin kanki shi kike yi. Yanzu mene amfaninki na cinnawa wajen nan wuta? salon kija mana barin gida". "ai kin san dai ni ba mahaukaciya ba ce ko, duk abunda kika ga nayi ina da dalili...dan haka matsa da baya". "wai na matsa da baya kike cewa, ke kuma fa?, kina kallo fa petir ɗin da kika zuba yana da yawa, kina kunna wutar nan fa tasowa sama zata yi". "ni dai kija da baya kawai nace". Sautin muryarta ya fito cikin amo na ɓacin rai. Aiko babu shiri Maijidda taja da baya tai nesa da ita. Fillo kuwa tasa hannu a gefen zanen da bata iya ɗaurinsa ba har yanzu ta kunto layar da take ajiye da ita. tasa a tsakiyar tafin hannunta na dama tana ƙare ma ta kallo, kamin daga bisani ta shiga warware baƙi da jan zaren da aka naɗeta da su. Sau uku tana duba sunan dake jikin layar, ranar farko data fara warwareta ta kasa karanta rubutun dake jiki alokacin bata iya karatu ba, da rana ta biyu da karatun da Amir ke mata ya fara zama akanta ta ɗauko ta duba dan haddace yanda harufan jiki suke, da kuma rana ta uku da ta rubuta harufan a wata takarda ta daban tai compairing rubutunta dana jikin layar dan tabbatar da tayi daidai, kuma a ranar ne ta iya karanta hurufan dake jiki, harufan sunan MUHAMMAD TURAKI. To
🏠