fisabillahi ji wani abu, anyi shara kin ɗage min carpet salon dai ayi baƙo a tafi anayi da ni a duniya bana gyara wajena, alhalin ba haka nake ba, kai da gara wani can da baku haɗa komai da shi ba yazo ya ɓata maka...kuma ni dai gaskiya nake faɗa miki kwanciyar ƙasar nan illa zata miki, inda rabon kin haifo ɗan da sanyi yayi ƙatutu a jikinsa ne to".
ta ɗau mayafinta dake kan kujera ta fita daga parlon, ɗan ƙaramin durstbin na shara ta ɗauka a ƙofar parlon sannan ta wuce ta nufi can inda incilerator yake zata zubar da sharar sai mita take yi.
"yanzu ni ba abin na faɗawa Amadu irin cin kashin da ƴaƴansa suke min ba yaga kamar ina tukura musu alhalin nazo ina cin arziƙinsa, Zainabu ta ƙullace ni tace zan haɗa ƴaƴa da ubansu. gwara nayi shiru na haƙura watarana sai labari, amma tsakani da Allah ni ba daɗin hakan nake ji ba, kawai dai dan babu yanda zanyi ne, amma cuta kam ana cutata".
ganinta mai gadi ya taso da sauri. "Inna ina za ki haka da kanki?". ta tsaya tana gyara mayafi tace,"ni ko wa nake da shi da zai min bacin na ƙarfafa jiki naiwa kaina". ta ɗaga ƙaramin durstbin ɗin sharar tace masa,"kaga dai yanda kwandon nan ya cika ko?".
ya ɗaga kai yace,"na gani". tace,"to billahi ina faɗa maka ko dattina ɗaya babu aciki, bar ganin daga ɓangarena ya fito".
Mai gadin yace,"to fa garin ya haka kuma Inna?".
tace,"karka tsammaci aljanu ne, wallahi ko ɗaya basu da hakki, mutanene marasa tausayin tsoho. Ƴaƴan Amadu ne wallahi, haka suke zuwa su cika min ɗaki alhalin ubansu yayi musu nasu, to ba zasu zauna a nasu ba dole dai sai anzo wajena an ɗauki magana. ni kuma bana biye musu kasanni da haƙuri, ban iya ɗaukar magana ba saboda bana son tashin hankali. kuma dai naga gidan na ubansu ne arziƙinsu nake ci shi yasa na iya zamana da su banda haka kullum sai anji kanmu...yanzu fa ka duba ka gani wannan sharar daga safiya zuwa yammacin nan aka tarata, da ci banza ci wofinsu aka mayar min da ɗaki kamar bola. yo ni kuwa me zanyi wanda ya wuci Allah ya isa".
Mai gadi yace,"a'a dai Inna haƙuri za'a ci gaba da yi, banda dai Allah ya isan kinga ai jikoki ne".
tace,"yo abunda ba ni na haifa ba balle bakina ya bisu su gantale, barni nayi kayata ni dai kam ai Allah ya isar min kawai. kai ai baka san wani abu ba ma, Allah ya isa ai sun saba da ita, dan jiya yaron nan Aliyu ce min yay wai babu wajen shigar tawa, daga nan na sallama nace Allah ya isa kam yanzu na fara har sai tawa ta sami shiga... yanzu ka duba ka gani banda dai rashin tausayi ina uwar me ƙaton gidan nan da kai shara, ko da yake rayuwa ce kowa yay na gari kansa...haka zanta haƙuri har dai Allah ya kawon mafita, ko kai haka iyalinka ke Uwakka?".
Mai gadin yace,"a'a Inna". tace,"kaga inda arziƙi yake, banda gidan Amadu inda Ƴaƴan ba kyau matan ba kyau".
Mai gadin ya karɓi basket ɗin yace,"kawo na zubar miki, ai ba kyaje wurin can da kanki ba yamma tayi".
ta sakar masa tana faɗin,"kai da yake ai kasan darajar babba. na gode Allah yayi maka albarka ya raya maka iyali, yasa ka gama da duniya lafiya, Amadu na dawowa zansa shi yay maka kyauta wallahi. ni ko zamu koma kanon ma ai ba zan bari a tafi babu kai ba, wa zai so ya rabu da ɗan arziƙi irinka".
nan ya barta tana ci gaba da surfa mita, ta zubawa gate ido tana ta Allah Allah motar Yusuf ta shigo. Mai gadin ya dawo ya bata basket ɗin ta wuce tana ta ƙara gode masa.
tazo wucewa ta ɓangaren Ammi ta saki basket ɗin ya faɗi ƙasa, babu shiri ta saki salati tana ɗora hannu aka. "la'ila ha'illallahu Muhammadu Rasulillahi". Ammi ta dakata da shiga parlonta ta juyo tana kallonta. kamar ba zaita magana ba, yanda taga Inna Wuro ta ɗora hannu aka yasa dole ta magantu har tana dawowa da baya don ganin lafiya.
"me ya faru?". cewar Ammin tana bin wurin da kallo. Inna Wuro ta sunkuya ta ɗauki durstbin ɗin tace,"a'a babu ruwanki, yaushe rabon da magana ta haɗani dake, tunda azumi ya fita kika ƙulla gaba da ni, sai yanzu ne da kika ga ina neman cutuwa sannan za ki kulani, to gaskiya matsa daga kusa da ni bana son munafurci...duk wanda yay na gari dai kansa, ni ɗin dai wallahi ba abar banza bace nafi ƙarfin wulaƙancin bawa tunda ni na haifin me ƙaton gidan nan".
jin haka Ammi tai tsaki a ƙasan ranta tai wucewarta, dama tasan ba wani abin arziƙi ba ne, bai wuce abinta da ta saba. Inna Wuro ta bita da ido ta taɓe baki, bata ce komai ba ta wuce side ɗinta, cikin ranta sai masifa take yi Yusuf bai dawo ba har yanzu.
tana shiga ta tarar da Kursum ta fito daga ɗakinta. tai saurin ajiye durstbin ta cire mayafinta ta aje. tabi hannun Kursum da ido har tazo ta zauna, idonta akan bowl da Kursum ta ciko da alkaki tace.
"babu masifar da ta wuce haihuwar ɓeraye wallahi. to ni Safiyya mene marabar ƴaƴan Amadu da ɓeraye?, ka ajiye aje a ɗauke babu neman izini. to ba zan iya ba, Allah ya dawo da shi lafiya, ko ya min gidana daban ko kuma ya katangeni a gefe ɗaya, ba zance haɗa mana ƙofar shigowa ɗaya da ku...ban son fitina ban iyat