NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 66 of 323

ake ma kamar ƙunƙuni take tana zaginsa. suna haka aka murɗa ƙofa, tana jin hakan gabanta yay mugun faɗuwa ta haye kan gadon gaba ɗaya a zabure, ta takure ƙafafuwanta tana shirin sakin kuka. muryarta na karkawa ta cewa Turaki,"tun ɗazu na cinye abincin dan Allah kuyi haƙuri". tana rufe bakinta sai taga ashe su Kaka ne ba Dr Yusuf ba kamar yanda ta tsammata. hakan yasa ta saki ajiyar zuciya tana bin Kaka da ido, taga fuskar Kakan a haɗe alamar ɓacin rai. "sannu fa me babban suna". Turaki ya tashi ya amsawa Kaka. "yauwa Kaka sannunku da dawowa. ya me jiki?". tace "da sauƙi...kayi zamanka mana". yace,"a'a Kaka dama ina niyyar tashi ai". tace,"ni dai daka zauna wallahi, bana jin daɗi idan kana ƙin zaman nan saboda mu". ya kalli tsohuwar da jin tausayinta a ransa, sosai suke kama da Fillo kawai dan ita ta tsufa ne. baya son musu da babba saboda haka dole ya koma ya zauna. bayan ya zauna Kaka tace,"muna daɗa godiya fa me babban suna, babu abinda zamu ce sai Allah ya saka maka da gidan aljannah. kai da iyayenka kuna kulawa damu Allah ya biyaku da alkhairansa". yace,"amin Kaka na gode". ta sake cewa,"Maijidda ce taje take faɗa mana abinda ke faruwa na za'a shiga da ita tiyata, shine muka taho. nace ai hakan ma wani gata ne akai mata". Yami tace,"Allah yasa dai ayi a sa'a". ya sosa girarsa leɓensa na fitar da murmushi yace,"ehh likitan ne dama ya bada shawarar hakan". karaf Fillo tayi saurin cewa,"a'a ba shi bane kaine ka fara faɗa masa. ni dan girman Allah Kaka kuyi haƙuri indai abinci ne zanke ci". Kaka tai mata banza, Yami tace,"to ai magana ta ƙare tunda har likitan ma yayi shirinsa. kiyi adu'a kawai Allah yasa ayi miki a sa'a, hakan ai gata akayi miki Fillo kinga yanzu cikinki ga dinƙa samun abincin kirki. magana kuwa kya dinƙa nuna abunda kike nufi da hannu". Yami na yin shiru Fillo ta fashe da kuka tana kifa kanta a gwiwarta, ta sani babu wanda zaiji tausayinta, kuma babu me jin kukanta tunda bata da uwa bata da uba a raye. Turaki ya ɗauke idonsa akanta, zai fita Kaka tace,"a'a me babban suna tunda dai sa hannunka ne a yin aikin nan to ka ɗan jira likitan yazo a ɗauketa a gabanka. mu ba jin maganarmu take ba,". tana faɗin haka suka fice su duka suka bar Maijidda a tsaye, itama sai ta fara hawayen. bayan fitar su Kaka ya jawo kujera sosai gaban gadon sannan ya zauna, ya aje wayarsa akan gadon, sannan ya sarƙe yatsunsa wuri ɗaya. yace da ita,"haƙura za'ai da farka cikin ko kukan za ki ci gaba?". kalmar farka cikin ita ke ɗaga hankalinta, tai saurin ɗagowa fuskarta tayi sharkaf. "dan girman Allah karka sa a farke min ciki, zan dinga cin abinci kullum, ai kana kallo ma cinye na ɗazu. dan son da kake yiwa Maama da Adda Zaytuna kace ba za'ai min ba". mamaki yasa kawai ya tsareta da ido, taya akai tasan yana ƙaunar mutanen nan guda biyu?, taya tasan zai iya yin komai akansu?, waya faɗa mata ana roƙonsa da su ya aikata abinda bai niyya ba?. ya sauke numfashi sannan yace,"an fasa". a hankali tace,"na gode, Allah ya kareka daga sharrin maƙiyanka". ta faɗa tana goge hawaye da ɗankwalinta daya zame. suka haɗa ido tayi saurin ɗauketa nata, ya kalli gashin kanta yace,"ɗaura ɗankwalin ki bani amsar tambayata". ta ɗaura ya ƙara cewa,"to ki cire tsoron ki nutsu". ta haɗiye wani irin yawu tana saita nutsuwarta. taji yace,"ɗago idonki ki kalle ni". tayi yunƙurin yin hakan amma sai ta kasa, yaci gaba da kallon siraran hannunta da suke ta karkarwa, sai kawai ya miƙa hannunsa ya haɗe hannayenta biyu ya riƙesu cikin nasa guda ɗaya, sai dai da mamakinsa duk da hakan basu bar karkarwar da suke ba kamar ma ƙaruwa abin yayi, cikin ransa ya ayyana duk yanda akayi wannan rawar da jikin nata yake yi bana lafiya ba ne. jin yanda ya riƙe hannuwan nata yasa ta kulle ido wani abu na wucewa ta maƙogoronta. kuma kafin ta buɗe idon taji yace,"me ya kaiki wannan wurin a wancan ranar?". ta buɗe ido ta sauke a saman sumarsa tana jin numfashinta na ƙoƙarin katsewa. **** Yusuf na zaune a office yana operating computer wayarsa tai ringing, ya kai hannu ya ɗauki wayar, yana duba sunan me kiran yaga Inna Wuro, ya katse tukunna yabi bayan kiran. Inna Wuro na ɗaga kiran ta maka salati,"innalillahii wa'inna ilaihi raji'una. Yusuf kana ina?, kaiwa Allah kazo da sauri babu lafiya". tun salatin farko data ja ya miƙe daga kan kujerarsa, tana cewa babu lafiya bai jira komai ba ya kai bakin ƙofa, yabar office ɗin cikin sauri hankalinsa a tashe. daga parlon Inna Wuro ta soke wayarta a gefen zani bayan kiran wayarsu da Yusuf ya katse. ta kalli Nuratu wacce ta tattare carpet ta kwanta a ƙasan tiles, sai yamutsa fuska take yi hannnunta riƙe da tulun ƙasa ƙarami da aka zuba yashi acikinsa, acikinsa take tofa yawu. "ina dalili, gwara ya baro duk abunda yake yi yazo aiwa tufkar hanci, ba zan iya rainon wannan cikin nasa me shegiyar ƙazanta ba. ba ni nai ciki ba dan haka ba zanyi wahalarsa ba, azo duk abi a dinga tofe min ɗaki da yawu yana ƙarni...yanzu fa
🏠