NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 65 of 323

dawo ki ƙara ci kije ki amayar haka har ki cinye shi". wannan karon ba ita ta kalle shi ba Maijidda ce, tana masa kallo ɗaya ta ɗauke idonta ta koma can kan ɗaya gadon dake cikin ɗakin, room ɗin 2patient ake admiting acikinsa amma ko da Baffa yazo sai ya biya kuɗin ɗaya gadon dalilin da yasa take zaune ita ɗaya kenan. jin an turo ƙofa Turaki ya kai idonsa wajen, Dr Yusuf ne ya shigo bakinsa ɗauke da sallama. duk da cewar tun ɗazu da Turaki ya baro masallaci yana office ɗinsa hakan bai hana su daɗa yin musabaha ba. as usual fuskar nan tasa da murmushin da baya yankewa. "ya me jikin ranka ya daɗe?". Dr Yusuf ya tambayi Turaki. "gata nan maganin gardama ya rage ku bata before ku sallameta". Dr Yusuf yay ƴar dariya yace da Fillo,"ya kike jin jikin naki?". tace,"naji sauƙi". yace,"to Allah ya ƙara lafiya. yanzu cin abinci yay miki saura shine zaki samu ƙwarin jikinki". tace,"to". ya juya ya karɓi file daga hannun nurse ɗin da ta shigo ɗakin yanzu, yay rubuce-rubuce sannan ya rufe ya bata. ya fuskanci Turaki yace,"insha'Allahu by wenesday zamu sallameta. komai normal babu wata matsala". Turaki ya kalleta ya kalli tuwon yaga ko rabin cinsa bata yi ba, yace da Dr Yusuf. "Allah ya kaimu. amma babu yacca za'ai a farke cikinta a dinƙa zuba mata abinci ta nan?, tunda bakinta nayi mata wahalar cin abincin". da murmushi a leɓen Dr Yusuf yace,"babu matsala sai ayi hakan. bari yanzu sai mu fara preparation ɗin shiga da ita ɗakin tiyata...sai dai kuma fa idan za'ai irin wannan aikin dole sai a ɗinke baki gaba ɗaya ya zamana mutum ya dawo baya magana, wurin da za'a yanka a cikin nan nasa shine zai koma yagar bakinsa, abinci da ruwa ne kawai za'a dinga zubawa a ciki". Turaki ya sosa girarsa sannan yaja kujerar dake kusa da shi ya zauna. "ayi abinda ya dace kawai Dr". sai ya kalla agogon hannunsa yace,"nan da minti nawa za'a shiga tiyatar?". Dr Yusuf yace,"in the next 5minutes, office kawai zan shiga na fito, ita dai yanzu a shiryata". Turaki yace,"alright a fito lafiya". Dr Yusuf ya fita Nurse na biye da shi, wacca take ta dariya ƙasa-ƙasa da zancen da akai, ta lura sosai maganar ta tsorata Fillo. Maijidda ma na gefe a tsaye, itama dariya take ƙasa-ƙasa farkon da akayi zancen farka ciki, saboda yanda taga Fillo ta tsure tana raba idanuwa, amma daga baya da taga kamar maganar da gaske ne sai tai jugum tana dai ta kallon Turaki ta gefen ido, tana kuma jin tausayin Fillo na tsarga mata. _"amma babu yacca za'ai a farke cikinta a dinƙa zuba mata abinci ta nan?"_ maganar ta Turaki ta daɗa maimaituwa acikin kanta. farko daya faɗa bata razana ba, amma da ta shiga bin fuskokinsu tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya sai ta tsorata ainun, dan ko ɗigo babu na alamar wasa a yacca fuskokinsu ke nunawa, hakan ya tabbatar mata lallai da gaske suke, farke mata ciki za'ai sannan kuma a ɗinke bakinta ta daina magana har a abada. idan da abinda yafi tashin hankali wannan maganar tasa ta shiga ciki, hangota take babu bakin magana kuma cikinta a yage, ta haɗe murfin idanunta da suke neman zazzagowa ƙasa, dan tunda aka fara maganar suke a waje. jikinta rawa yake sosai, ƙatuwar malmalar tuwon take ta kallo, lissafi take yi, lissafin yanda za'ai ta cinye shi acikin miniti biyar kafin a shiga da ita tiyatar da suka ce. ta ɗago ido ta kalli Maijidda dake kallonta, yanda take a tsorace haka Maijiddan ma. cikinsu biyun kowa ya kasa cewa komai, tsoron Fillo ɗaya ne! tace zata basa haƙuri ya sakar mata wannan uwar tsawar da bata so, dan taga kamar hakan yake jira, dalilin daya sa bakinta mutuwa kenan. Maijidda tayi sum sum ta fice zuwa kiran su Kaka, tana fita Fillo ta sakko a kan gadon ta wuce toilet, Turaki ya bita da kallo har ta dawo. ta koma gefen gadon ta zauna, ta saka hannunta da ta wanke ta fara cin tuwon tana kai ƙatuwar lomar data fi ƙarfin bakinta. kana gani kasan tura tuwon kawai takeyi, bata ko tsayawa ta gama cinye na bakin zata ƙara saka wani, tunda take bata taɓa cin malmalar tuwo me girman wannan ba, kai abincin kansa bata cin da yawan hakan, shi yasa Yami kullum ke mata tsiyar taƙi ci tana ta bushewa. yana zaune yana shafa wayarsa amma indonsa sam ba akan wayar yake ba akanta yake, tun lomar farko da ta kai baki. ba ƙaramin bashi dariya tai ba ya danna yana cije leɓe murmushinsa na fita saboda dariyar ba zata dannu duka ba, yanda take ta tura abinci cikin sauri, har yunƙurin amai tai amma tai maza ta maida shi, ga jikinta ma gaba ɗaya rawa yake kamar mazari. cikin mintunan da ba zasu haura uku ba plate ɗin ya zama babu komai, ta cinye tas sai nishi take yi, ta sauko taje ta wanke hannu ta dawo. ta kalle shi taga ma hankalinsa bai kanta, wayarsa kawai yake dannawa, kamar tai magana ta roƙe shi suyi haƙuri sai dai tayi shiru, ta kama yatsun hannunta sai jansu take kace tana lazimi. idanuwan nan da suke loko sai ƙifƙiftasu take. Turaki duk yana kallonta, har maganar da bakinta ke sonyi yana kallon yanda ɗan ƙaramin leɓen ke motsawa. shi gani y
🏠