a min irin haka, ni fa jikanku ne, ku daina kallon wani matsayi da nake da shi, mutum nake kamar kowa".
Yami tace,"ranka ya daɗe kallon matsayi ai ya zama dole kam. kai ɗin ne dai ka fita daban da sauran da suke da irin matsayinka. kuma muna godiya a gareka bisa kyautata da mutumtawa, Allah ya haɗaka da mace ta gari".
Kaka ta matsa daga bakin ƙofar tana basa hanya. "ka shiga ciki yallaɓai bismilillah, ai tama farka tun ɗazu, jiki da sauƙi kam".
idonsa na kan handle yace,"to masha'Allahu, Allah ya ƙara lafiya...ina dai daɗa bada haƙuri Kaka".
Kaka dai bata kallonsa tace,"kai haba ranka ya daɗe wane mutum, aimu wannan tsautsayin abun farin ciki ne garemu. in banda haka ina ma za'a ganta?, da yanzu muna cikin tashin hankali".
bai ce komai ba ya kama handle ɗin ya buɗe ƙofar, su Kaka kuma suka wuce bayan sunce masa zasu je ɗaya ward ɗin ne zasu yo dubiyar wata Ƴar Ƙawarsu da aka yiwa aiki ta haihu ɗan yazo babu rai, yayi musu a dawo lafiya sannan suka wuce shi kuma ya shiga room ɗin.
Maijidda nata fama da Fillo kan taci abinci amma taƙi, bai maida ƙofar ya rufe ba, kawai ya tsaya yana kallon Fillo kamar ɗazu daya tsaya. yana kallonta ta window sanda suke abinsu ita da Maijidda. shi mamaki ta basa sosai bai yi tsammanin ma yarinyar na magana ba, da sakewa irin haka, zatonsa a tsorace take ko da yaushe irin yanda ya saba ganinta.
idanunsa suka nuna masa irin ramewar da ta ƙarayi, ƙasusuwan jikinta tsab zasu lissafu, idonta ya faɗa yayi loko kamar yanda yaga nasa yayi daya na duba madubi ɗazu.
basu san ya shigo ba sai da Maijidda ta miƙe tana faɗin,"kiran Amir zanyi na faɗa masa kinƙi cin abincin, shi kya ji maganarsa tunda kina sonsa". ta harareta tace,"ku kuma da banji maganarku ba bana sonku kenan?". Maijidda ta ɗaga kafaɗarta,"alama ta nuna hakan". Fillo tai shiru ta maida ƙafafunta kan gadon ta jingina da pillow, sai lokacin Turaki ya tura ƙofar ya rufe ya ƙarasa shigowa.
dukansu suka kai idonsu bakin ƙofar, gaban Fillo ya faɗi, taji wani tsoro ya kamata. ta wutsiyar ido yake kallonta, kuma yaga wannan tsoron a idonta wanda bai gani ba a ɗazu da take tare da ƴar'uwarta.
da sauri Maijidda ta aje abincin dake hannunta ta durƙusa tana gaishe shi, ya amsa muryarsa bata fitowa sosai. ta miƙe ta ɗauki kujera daga gefen gadon Fillo ta kai masa, amma sai bai zauna ba.
Fillo dai da bata san ma shi ya kaɗeta ba, dan ba'a faɗa mata ba. tana dai cike da mamakin waɗanne irin mutanene su, ita ba kowan komai ba garesu amma sai zuwa suke suna dubata, taji su Kaka sunce jiya da yau ne kawai Hajiya Madina da Baffa da Boɗejo basu zo ba, amma hatta Hakimi kansa sai daya zo, kuma shima Mai Martaba sai daya aiko iyalinsa suka zo. ƙwarai kirkinsu ya wuce tunanin mutum, kuma la shakka ba zasu taɓa faɗuwa a rayuwa ba sai da cigaba. ba tayi zaton ma Turaki zai iya zuwa dubata ba tunda wanda bai sonka baya sonka, no matter what happen to you ba zai nuna tausayinsa akanka ba.
zuro da ƙafafuwanta tayi daga kan gadon zata sauko ta gaishe shi, sai taji muryarsa kamar a saman kanta yace,"ki sauko kiyi me?". bata ɗago ta kalle shi ba tace,"zan gaishe ka ne". idonsa har lokacin na kanta yace,"waya farlanta miki hakan?". bata ce komai ba tayi shiru sai wasa da yatsun hannunta take ta duƙar da kai.
shi kam kallonta kawai yake, ta wani natsu kamar wadda taga mutuwa, kamar ba ita ta gama surutu ɗazu ba harda dukan wata.
ɗakin yay shiru Maijidda na daga gefe har yanzu a tsugune, ya maida kallonsa kan abincin da Maijiddan ta aje yace,"ki kawo mata abincin".
Maijidda ta ɗauko plate ɗin dake ɗauke da tuwon semovita da miyar agusi da naman ganda akai, ta miƙawa Fillo wacca tuni idonta ya cika da ruwa sai aikin ɓata fuska take.
da mamakin Maijidda babu tirjiya balle musu Fillo tasa hannu ta karɓa, kallon abincin kawai take ba don tana jin zata iya ci ba. bakinta babu taste ɗin komai hakan ne yasa ba zata iya cin komai ba, kuma bata ma jin yuwar.
wucewar daƙiƙa biyu Turaki yace mata,"wa kike jira yazo ya ci miki?". ba tsoronsa take ji ba, ita kawai yana yi mata kwarjini ne, ko bata kalle shi ba indai yana waje sai taji girman kwarjininsa ya cika wurin.
ba don tana so ba ta gutsiri tuwon da spoon ta kai baki, ta tauna ta haɗiye da ƙyar kamar me tauna magani, tana yin spoon huɗu sai ga amai ya yunƙuro, Turaki yay saurin ɗauke idonsa daga kanta ya kauda kai gefe yana jin zuciyarsa na tashi, Maijidda ta kamata suka wuce toilet, duka ta amayar da ɗan guntun abin da taci, ta wanke baki suka fito har sannan yana tsaye sai dai yanayin fuskarsa ya sauya.
sai sauke numfashi takeyi tana maida ƙwallar idonta, ta ƙasan ido take ta kallonsa, tana ce sannu yazo yi mata?, shi bai yi ba kuma bai tafi ba ya tsaya kamar wani sandar ba'are, Allah ya sani ji take kamar akanta yake a tsaye, da zata iya da ta buɗe baki tace masa ya tafi kawai.
a bakin gadon ta zauna. kuma tana zama taji ya ƙara cewa,"ki ɗauka ki ƙara ci, sai ki ƙara zuwa ki wani aman, ki