NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 63 of 323

ah sarki Granny, insha'Allahu zan matsa masa akan muje, sai mu dawo a ranar tunda dai am sure ba zai kwana ba". Zaytuna ta cirewa Fillo drip nata daya ƙare yanzu, itama tana tambayarta yanda take jin jikin tana faɗa mata komai da sauƙi ƙafarce dai har yanzu. after five minutes Zaytuna ta yiwa su Kaka sallama saboda kiran da Baffa yake yi mata, tare suka fita da Khalil wanda yake ta mamakin yacca akai har yanzu Turaki bai shigo ba. bayan fitarsu Maijidda ta dafa shoulders ɗin Fillo tace,"mene damuwar?". tace,"me kika gani?". Maijidda tace,"na san dai ba ki da lafiya amma yanayin fuskarki ya nuna akwai damuwa a ƙasan ranki". Fillo ta haɗiye yawu tukunna ta ɗago ta kalla Maijidda sannan tace,"me yake damun Amir?". Maijidda ta tashi daga kujerar da take zaune ta dawo gefen gadon kusa da ita ta zauna, ta kamo hannunta ta riƙe acikin nata tace,"me kika gani?". Fillo ta dake ta hana kukan dake ƙoƙarin fitowa tace,"sannu fa kawai yace min, ina amsawa yasa kai ya fice". "kinyi masa wani laifi ne?". ta girgiza kanta,"a'a ni banyi masa komai ba. kuma ko da ace ma nayi masa ba zai min haka ba tunma daya ganni banda lafiya". Maijidda tace,"to kwantar da hankali ba abinda kika masa, kawai yana cikin damuwa ne akan lamarinki. yace ya kasa fahimtar me ke faruwa, yana ganin kamar mutanen ɓoye naso su shafeki ne tun a wancan ciwon da kika yi, amma wannan karon sai yaga kamar ma sun riga sun shigeki...baki gani ba wallahi yanda yake ta sadaƙa yana sauke miki alƙur'ani, anan fa yake kwana kullum baya tafiya, abinci sai Innarsa tayi da gaske". Fillo tai ɗan jim kafin tace,"to ai ni banda wasu aljanu, hasashensa ne dai kawai". Maijidda tace,"to aikuwa abinda kowa ke faɗa kenan". Fillo ta kalli su Kaka da suke can gefe suna maganarsu, hankalinsu baya kansu gaba ɗaya. murya can ƙasa tace,"Maijidda ina asirin da nace miki zan ɗauke a ɗakin Turaki?". idanun Maijidda a waje take kallon Fillo da al'ajabi, ai dama tunda hakan ta faru ta fara tunanin da wuya idan ba karambaninta ne ya bata damar ɗauke asirin data gaya mata zata ɗauke ba. ita kam ta fara tsorata da lamarin ƙawarta, ta bakin Amir aljanu sun shigeta domin mutum dai ba zai yi abinda takeyi ba. Fillo taja hannun Maijidda da taji tayi shiru,"kina da matsala wallahi, shi yasa wani lokacin da faɗa miki abu gwara shiru". bata bawa Maijidda damar magana ba taci gaba,"na ɗauke asirin harma ya ƙone". "shima ke kika ƙona shi?". ta girgiza kanta,"aa wallahi ikon Allah kawai, ba ki gani ba kamar tashin bom haka yayi tushhh, kinji yanda yake ɗoyi kuwa Allah kika shaƙa kayan cikinki sai sun kusa zubowa...kuma kin san me?". ta faɗa tana muskutawa ta gyara zamanta akan gadon inda ta juyo ta fuskanci Maijiddan. "ina ga wannan asirin ne yake hana Turaki Sallah, ai dama na faɗa miki naji Maama na kokawa da hakan. kinga nima fa tun sanda na ɗauko shi naji bana sha'awar yin sallah kwata-kwata...bari dai mu bar asibiti zan baki labarin komai". ita dai Maijidda tsuru tayi tana zubawa sarautar Allah ido, ta ɗanja baya kamar tana tsoron Fillo ne. muryarta itama a can ƙasa tace,"wani lokacin idan muna magana sai naga kamar bake ba, shi yasa bakina baya rabo da ayatulkursiyu...to Allah dai ya baki lafiya ya rabaki da su lafiya. insha'Allah sai anyi galaba akansu...". bata ƙarasa ba Fillo ta kai mata duka a kafaɗa ita kuma tayi saurin kaucewa tana dariya. "Allah ki bar wannan zancen Maijidda bana so, ba wasa bane wannan, wani yaji ai sai ya ɗauka gaske. ƴar wulƙanci kawai". Maijidda har sannan fuskarta da dariya tace,"yo daga miki abin arziƙi, adu'a fa Haliman Amir?, ina ga ma wannan dalilin Allah ya duba ya aiko Malam Amir gareki, kinga ai sa dinga cin ƙwal uwarsu a hannunsa, dan ba raga musu zai yi ba...waya sa ni ma yanzun ko ba ke bace". wannan maganar tasa Fillo zuro ƙafafunta zata sauko a gadon ta damƙeta, ita kuma tayi wajen su Yami tana ta dariya. Fillo tayi ƙwafa,"Allah kika ci gaba sai na bugo miki wannan ƙarfen". ta faɗa tana nuna ƙarfen da ake saƙale drip a jikinsa. Kaka dai idonta na kansu tun ɗazun, tana jin zuciyarta na washewa daga damuwar dake tare da ita, sai yanzu hankalinta ya dawo jikinta. ko babu komai tasan Fillo ta sami lafiya, abu ɗaya yayi saura, matsalar jinnu da suke tunani sun shafeta. Fillo ta rafka tagumi tana tunani Kaka ta miƙo mata abincin da bata ci ba ɗazu, ta ɗago tana ɗan yamutsa fuska, murya a narke da shagwaɓa tace,"Kaka na ƙoshi fa". Kaka tai mata wani kallo tace,"amsa kafin ranki ya ɓaci, kin farka za ki ɗora daga inda kika tsaya ko. wadda bata tausayin kanta kawai". Fillo na turo baki ta karɓi plate ɗin. "wallahi ki cinye shi kafin na dawo". Kaka ta faɗa tana kaiwa ƙofa. Yami ta miƙe tabi bayanta suka fita tare. a bakin ƙofar suka tarar da Turaki wanda jin zasu fito yay saurin matsawa daga jikin windon da yake tsaye a wajen tun ɗazu. suna ƙoƙarin durƙusawa ƙasa su gaida shi ya dakatar da su. "dan Allah Kaka bana son kuke tsugun
🏠