NOVEL SHARES -
wayewar gari insha'Allah da kanki za ki tashi bama sai an taimaka miki ba".
bata bar kukan ba tace,"to idan ban kai goben ba fa naje nace da Allah me?, ni dai dan Allah ka taimaka min na tashi na sauke nauyin da yake kaina". Yusuf dai da yaga zasu yi daru da ita kuma ba jin duk wani bayani da zaiyi zata yi ba kawai sai ya sakar mata allurar bacci.
baccin da bata farka a shi ba kenan ba har sai washegari da wajen ƙarfe goma, lokacin su Kaka sunzo, tana buɗe ido akan Kaka ta sauke wacca ke zaune kan kujera ta rafka uban tagumi. Maijidda kuma na tsaye jikin bango kana kallon fuskarta zaka san tasha kuka ta gode Allah, itama duk ta faɗa saboda tashin hankalin da suka shiga. Yami ce kawai me ɗan ƙarfin hali da take ta tausar Kaka akan ta daure ta saka abu acikinta tunda likitan yace zata farka. kuma kwana biyu Kakan banda ruwa babu abinda take sha, shima idan tasha ɗacinsa take ji.
"Yami ba zan iya sa komai acikina ba sai yarinyar nan ta farka, yau fa kwana huɗu kenan, faɗa mana suke tana raye, ni dai ina tantamar hakan, gwara kawai a faɗa min gaskiya a bar ɓoye-ɓoye aini musulma ce na yarda da mutuwa".
Yami dai tayi shiru bata ce komai ba, sai kallonta da ta maida kan Fillon, itama dai ta fara tantama akan maganar likitocin nan, ace kwana huɗu mutum bai farka ba kuma sannan ace yana raye?, to mene amfanin ɓoyewar?. sai kawai ta gyaɗa kai cikin ranta tana faɗin wataƙila kuma ba'a so a ɗora alhakin mutuwar tata ne akan Turaki shiyasa, tasan zasu iya komai tunda suna da uwar kuɗinsu.
Fillo da take jinsu a lokacin ta kira sunan Kaka, wani farin ciki ya baibayesu suka yo kanta. Maijidda tayi mata wata runguma har sai da ƙashin bayan Fillo ya amsa. kuma a sannane Amir yazo, tunda ya shigo ya kafeta da ido, kallonsa take shima kallonta yake, zuciyoyinsu na saƙa abubuwa iri ɗaya dangane da junansu. kalmar da Amir ya fara faɗa mata shine,"za ki iya yin sallah?". kai kawai ta ɗaga masa, Yami ta kamata ta sakko a gadon ta kaita banɗaki. lokacin data fito Amir kawai ta gani har sannan yana tsaye idanuwansa duk sun faɗa ciki, kana kallonsa zai baka matuƙar tausayi.
shi ya shimfiɗa mata sallaya, ya tayata saka hijabin, yace mata idan zata iya ramawa duk ta rama, idan ba zata iya ba tayi wasu ta bar wasu sai jimawa. tambayar da tayi masa shine,"kwana nawa yau?". "huɗu". amsar daya bata kenan. kuma tunda ta tayar da sallar bata tsaya ba sai data rama duka sallolin dake kanta, har lokacin Amir bai zauna ba yana tsaye.
tana idarwa kuma sannu kawai yay mata, zai fice a ɗakin tabi bayansa da kallo tace,"ina zaka?". "tafiya zanyi". amsar daya bata kenan ya fice daga ɗakin bai jira cewarta ba, jikinta yayi matuƙar sanyi, su Kaka suka dawo ciki ta tambayi Maijidda suka ce ta tafi raka Amir.
Yami ta zuba mata abinci ta ajiye a gabanta, har lokacin tana kan sallaryar ta miƙe ƙafafunta, da ƙyar tayi sallar, ƙarfin dauriya irin nata kawai. "na ƙoshi Yami". kalmar da ta faɗa kenan, kuma kafin Yami tace wani abu an turo ƙofar ɗakin an shigo, Dr Yusuf ne, suka amsa sallamarsa sannan ya umarci Fillo da ta koma kan gadon za'a ƙara saka mata drip.
gadon ta koma ta kwanta, yay mata wasu tambayoyi dangane da yanda take ji tana basa amsa, acikin drip ɗin ya zuba duk alluran da za'ai mata. yana gama saka mata kuma yace da Kaka,"idan ya ƙare a bata abinci taci". da haka ya fita.
sai yanzu su Kaka suka sami natsuwa, Yami ta zuba musu abinci suka shiga ciki, lokaci zuwa lokaci Maijidda na lura da ruwan daya kusa ƙarewa.
bayan wani lokaci hankalinsu ya karkata ga turo ƙofar ɗakin da akayi, ganin wanda ya shigo da sauri Kaka ta miƙe tana yi masa sannu da zuwa tare da amsar ledojin dake hannunsa.
Khalil ya shigo yana ta kallon Fillo, mamakin da kowa yake akanta shine taya akai ta fita acikin wannan daren?, kuma me taje yi a wannan dajin?. shi dai abinda zuciyarsa ke raya masa shine Turaki ne ya ɗauketa zai je ya cutar da ita, Turaki ne yay komai, har yau haka zuciyarsa ke faɗa masa.
*Plss Comment, Vote, and Share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_🤔zato dai zunubi ko da ya kasance gaskiya, ku daina ɗaukar hakki babu kyau ni gaskiya nake faɗa muku, ahh tou🤣, yo kowa ya tashi sai ya wani kama cewa Hajiya Madina kaza-kaza, banda ma dai neman magana yaushe kuka taɓa ganin ta cutar da wani daban balle Turaki da ya gama nannaɗe zuciyarta😒...to a daina gaskiya ban so, duk wanda naji ya ƙara taɓata zan hau bori😭😭..._
*18*
After long minutes sai ga Zaytuna itama ta shigo room ɗin, har lokacin Khalil yana nan bai tafi ba, yana zaune akan kujerar da Kaka ta ajiye masa.
yana kallon Zaytuna da mamaki yace,"from where?". bayan duk ta gaida su Kaka tare da tambayarsu ya me jiki tace da shi,"bamu jima da shigowa garin ba, so muna sauka a airpot mukai waya da Hamma yake ce min yana nan".
Khalil ya ƙara tambayarta,"ya Granny ɗin?".
tace,"tana lafiya, duk tana gaishe ku...da ta saka rigimarma sai munzo tare tana so taga Hammah".
yace,"All