ta inda zata bi ta koma gida ba, saboda haka ta zube a wajen tana daɗa fashewa da matsanancin kuka, tsoro na ƙara cikata.
tana cikin hakan taji zuciyarta na biyo mata wasu ayoyi acikin alqur'ani da kuma wasu adu'oi dake cikin hisnul muslim, bakinta na karkarwa ta fara biyosu a fili. sai taji komai dake cikin kanta na washewa, haske na zuwar mata, mafita na zuwa cikin kanta. sai tayi zumbur ta miƙe, zuciyarta na faɗa mata ta bar wajen da sauri. tasa hannu ta toshe hancinta saboda warin hayaƙin, wani irin ɗoyi ne yake tashi aciki, tai azamar barin wajen da gudu amma sai taji ƙafarta guda ɗaya ta riƙe, sai sannan ta tuna da ciwon dake ƙafar. amma a hakan ta dinga jan ƙafar tana ɗaga waccan har ta bar wurin, kuma tana zuwa bakin wata ƙatuwar bishiya taji tushh abu ya fashe, bata tsaya ba taci gaba da tafiya, tsoro kuma na ƙara kamata, haka har ta shigo cikin wasu gonaki, ananne tsoro ya tsananta gareta saboda kukan karnuka dake tashi, bata san lokacin da ta kwasa a guje ba ta manta da ciwon dake ƙafarta duk da tana jin zafin ciwon na ratsata.
ta fito kan hanya kawai taga fitilar mota na haskawa, da fari kamar ba zata tsaya ba sai ta tsaya tana miƙa hannu don tsayar da motar, dole zata tsaya ta nemi taimako in ba haka bata san ina zatai ba, haka kuma bata san meke cikin wannan dajin ba, komai zai iya faruwa da ita. tana ta ɗagawa motar hannu, so take tai magana amma ta kasa, ga motar ita take tunkarowa, a wannan lokacin kuwa kan Turaki na ƙasa yana ƙaro volume na karatun qur'anin daya kunna, lokacin har ya ƙaraso inda take ba tare daya san da mutum a gabansa ba, a time ɗinne ta fahimci ko waye na cikin motar baya ganin gabansa, saboda haka cikin hanzari ta ɗaga ƙafarta da tayi mugun nauyi zata janye daga wurin, sai dai inaaa, kafin tai wani yunƙuri Motar Turaki ta daki gwiwoyinta ta kifo kan motar tasa.
ta san sanda kanta ya ƙwalu a jikin motar, ta san lokacin da ta silalo ta faɗo ƙasa, taga kuma lokacin da tayoyin motar ke ƙoƙarin bi ta kanta. take ta sallama da rayuwar, yau dai tasan babu abinda zai hanata bin Umminta, zata je su rayu tare harda Addarta, zata bisu shikenan sun bar Kaka ita ɗaya. tana kallon tayoyin motar na ƙara motsi suna tahowa zasu talitse kanta, sai dai daga nan, ji da gani da numfashinta duka suka ɗauke.
bata san me ya faru ba bayan nan, sai yanzu data farka, ta farka ta ganta acikin ɗakin asibiti, kan gadon asibiti, that means wanda ya bugeta mutumin kirki ne kenan?, shi ya kawota asibitin ko ya?, idan ba shi bane to wa ya tsintota daga cikin wannan dajin ya kawota nan?, ina Kaka?, ina Maijidda?, ina Yami?, ina Amir?, shin wanne hali suke ciki?. shin sun samu labarin inda take?, ko kuma suna can suna nemanta?, wacce amsa zata basu a lokacin da kowannensu yay mata tambaya?.
duk ba wannan bama, idan ta miƙe yanzu zata koma gida, ta san kuma amsar tarin tambayoyinsu, ba zata ɓoyewa Maijidda komai ba domin ita zata kawo solution. abun ɗaya ne kawai ke cikin kanta a yanzu itace sallah, sallolin da bata yi ba a wancan ranar na la'asar da magriba da isha. to kwana nawa kenan yanzu?, sallar kwanaki nawa ne akanta?, wa zai bata amsa?, don tasan ba lallai akan lokaci aka sameta ba balle ta iya ƙiyasta wasu kwanakin, kuma dole zata rama sallolin dake kanta.
ta kulle ido ta motsa ƙafafuwanta zata yunƙura ta tashi zaune sai taji tamkar zasu karye saboda sandarewa da kuma azabar ciwon da suke yi mata. kawai sai ta fashe da kuka, kuka sosai, likitan daya gama aikinsa ya tsaya akanta, tana jin yanda kallonsa ke shiga jikinta. baice komai ba har sai da ta tsaya da kukan dan kanta ta buɗe idon tana kallonsa, murmushi taga ya sakar mata tare da ce mata. "sorry".
muryarta na fitowa da sautin kuka tace,"dan Allah zanyi sallah". murmushi taga ya ƙarayi sannan yace,"za kiyi sallah amma ba yanzu ba, ki bari ko zuwa safiya ne". sai ta koma tana bin ko'ina na ɗakin da kallo, agogo take nema taga lokaci. tace da shi,"me yasa to ba zanyi ba yanzu?".
yana kallonta yace,"saboda ba za ki iya ba...". tun bai ƙarasa maganar ba ta kalle shi da idanunta da suka kawo ruwa ta katsesa da faɗin,"zan iya, Allah zan iya". tai maganar tana son fashewa da kuka.
Dr Yusuf yace mata,"to shikenan tashi ga banɗaki nan ki shiga, can kuma jakar kayanku ce sai ki ɗau hijab aciki ga abin sallah can". ta kalli inda yayi mata nuni, ta maimaita kalmar jakar kayanku acikin ranta, ta juyo ta kalle shi yana niyyar fita tace,"dan Allah wa ya kawoni nan?".
yace,"police da kuma wanda ya buge ki". ta maimaita kalmar a ranta kan tace,"dama ya tsaya?". yace mata,"ehh yana da imani shisa". hawaye na ƙara sauko mata a sanyaye tace,"Kakata fa?". ya juyo ya kalleta sannan yace,"kin fasa yin sallar ne?". ta girgiza masa kai tare da cewa,"a'a zanyi". ta faɗa tana so ta tashi amma tana jin ba zata iya ba, komai yayi mata nauyi kamar an danneta, kawai sai ta saka kuka.
Dr Yusuf ya dawo yana bata haƙuri da faɗin,"na faɗa miki ba za ki iya tashi ba, akan aikina fa nake, zuwa