shin Mai Martaba zai tabbata akanka, kuma zaka fuskanci hukunci daga masarautar kano".
shirun bafaden ya haɗe da tayar da iƙama a masallaci, muryar Turaki ta fito da wani amo mai taushi zuwa ga Gimbiya Aisha yace,"zanje nayi sallah, ki jira na dawo zan duƙawa izzarki kamar yanda kike so, zanta baki haƙuri har sai kin ƙoshi". yana faɗin hakan ya wuce ya ɗauki hanyar masallacin cikin sauri, tafiyar da ba zaka ce sauri yake ba saboda nutsuwar da ta shimfiɗu acikinta.
Gimbiya Aisha tabi bayansa da kallo tana jin wani malolon abu na tsaya mata a rai, _ta jira shi ya dawo._, haka ya faɗa mata fa, waye shi?, me yake ji da shi?, aina ya samo wannan isar?, ina ya sami ƙwarin gwiwar saka idonsa cikin nata bayan yaji wacece ita?. ta rufe ido tare da haɗiye wani busashshen yawu na takaici, for few minutes ta kalla fadawan dake yin kamar zasu yi mata sujjada ta basu umarnin tafiya.
Fillo na kwance kan gado drip na shiga jikinta, drip na kusan huɗu kenan da aka saka mata a yau, daga safiya zuwa yamma.
saman room ɗin kawai take kallo, dan su Kaka duk sun tayar da sallah, Maijidda kuma ta tafi raka Amir. hankalinta yana cikin ɗakin amma tunaninta yana waccan ranar da komai ya faru, komai ɗin da har yay sanadin kwanciyarta a asibiti.
tunda akayi admiting nata sai jiya ta farka a kwana na uku, mutumin da idanuwanta suka fara gani a lokacin da ta farka likitan da yake dubata. kallo ɗaya tayi masa ta mayar da murfin idonta ta rufe.
ƙoƙarinta a lokacin shine ta motsa amma sai taji ta kasa motsa ko da yatsa. Wani irin ciwo jikinta yake yi masa tamkar wadda aka kwan ana duka. da ƙyar ta ƙara iya buɗe idon, jin eyelids nata takeyi kamar an danne su da dutse. ta ƙara sauke idonta akan likitan da har lokacin yake kanta yana gudanar da aikinsa, bata gani da kyau amma gani takeyi kamar ta san fuskar, tana kallo ya ɗauko allura ya zuba acikin drip ɗin dake saƙale. da sauri ta daɗa rufe ido ta juya fuskarta gefe tana sauke numfashi sama-sama acikin tsoro, giftawar second ɗaya ta daɗa buɗewa ta tsaida ganinta a saman rufin ɗakin. ba rufin ɗakinsu bane, aina take?, a hankali ta zagaye room ɗin da idanunta tana so ta fahimci ina ne nan inda take, kuma waye shi wannan mutumin da ta fahimci daga ita sai shine acikin ɗakin. Sai a lokacin tunanin abinda ya faru da ita ya dawo mata.
abinda ta fara fahimta shine nan asibiti ne kenan. but taya akayi tazo wajen?, lokaci ɗaya sai hoton fitowarta daga ɗakin Kaka ya haska mata acikin kanta da cikin idonta, a hankali ta mayar da idon ta rufe, nan take komai ya shiga haska mata daki-daki.
tasan ta fito daga ɗakinsu, kuma kai tsaye gate ta nufa da ta fito daga ɓangaren nasu, ta miƙi wata doguwar hanya tana ta tafiya ba tare da sanin ina zata je ba, ita dai kawai acikin kanta tana jin ana ce mata ci gaba da tafiya. kuma sai da tazo bakin wani ruwa ta waiga taga ba gini gaba babu gini baya sannan ta fahimci ta baro cikin gida ta kuma baro kusa da gida.
fargaba da tsoro suka nannaɗeta, me ya kawota nan ɗin kuma me tazo yi?, ta tsaya tana ta kallon ƙaton kogin, bata san me zata yi ba?, bata san me take kallo acikinsa ba?, a jikinta kawai take jin bata so ta koma gida, kuma zuciyarta na raya mata cewar bata yi sallar la'asar, magriba da isha'i ba, sai dai ba zata yi su ba, dan tun lokacin da ta ɗauke wannan abin daga ɗakin Turaki taji sallah ta fice a ranta.
saboda haka sai ta nemi waje ta zauna a gefen kogin, ta zura ƙafafunta cikin ruwan, kamar mahaukaciya kuma sai ta kunce ɗankwalinta ta ajiye a gefe, gashin kanta dake tuje waje guda ya barbaje. har lokacin hankalinta da tunaninta na jikinta amma kamar bata san tana yin komai ba. a gefen wajen ta kwanta inda tayi matashi da ɗankwalinta, bacci take so tayi amma ba zata iya ba, kamar shikenan idanuwanta sun daina rufewa da sunan bacci, tana ji kamar shikenan ta gama rayuwa a Halimanta, kamar zata koma wata sabuwar rayuwar ne.
tsawon lokaci taji kamar an mintsineta, hakan yasa ta miƙe zaune a zabure tana karkaɗa ƙafarta acikin ruwan kogin. cikin rawar hannu ta kwance gefen zaninta ta fiddo da wannan abin, ta tsaya tana kallon abun zuciyarta na cika da mamaki, lokacin data ɗaukosa yana da duhu amma yanzu taga yay haske. me kenan?, kafin ƙwaƙwalarta tayi lissafin komai iska ta kaɗa ta kore abin daga kan tafin hannunta ya faɗi ƙasa yana gangarawa gefe ɗaya, da farko tsayawa tayi tana kallon yanda iska ke daɗa kora shi zuwa gaba, daga bisani kuma sai ta tashi zata je ta ɗakkosa, sai dai tana zuwa dai-dai ciyayin da abin ya shige taga wuta ta kama a wajen, kuma ba'a ƙara ko sakan biyu ba hankalinta ya dawo jikinta baki ɗaya. dan haka take a lokacin wani tsananin tsoro ya kamata, ta dinga waige-waige a wajen, ina zata yi yanzu?, babu kowa a wurin nan daga ita sai bishiyoyi sai wannan ruwan.
bata san sanda ta fashe da kuka ba, wutar dake ƙara ruruwa ta kusa kamo rigarta tai saurin matsawa daga wurin, kuka takeyi sosai, "Kaka". sunan da take ta ambata kenan, ita bata san