NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 6 of 323

lƙadarin waɗanda sukai aikin dama wanda ya saka su. Abunda ta ke son sani ayanzu shine waima waye Muhammad Turaki?, mene alaƙarsa da waɗanda suke neman ganin bayansa?, wanene shi acikin gidan nan?, me yasa tsawon shekaru takwas da ta ɗauka tana rayuwa acikin gidan nan bata taɓa ganin ko da gimlawar inuwarsa ce ba?, me yasa bata taɓa jin zancensa ba a inda ya dace a dinga ambatonsa?, me yayiwa masu son kassara rayuwarsa?. Bata da dukkan amsar waɗannan tambayoyin, sai kawai ta lumshe ido tare da hura iska a bakinta kamin ta furzar sannan ta sauke ajiyar zuciya. Bata manta da abunda ya faru ba a wajen, tsawon watanni biyar da suka wuce ba. Komai yana nan daki-daki acikin kanta, fuskokin mutanen da sukai aikin ne kawai ba zata iya shaidawa ba, dan a lokacin bayansu dakayan jikinsu kawai ta gani kamar yanda taga Muhammad Turaki a yau, amma ko muryarsu taji a yanzu zata nuna su ta rantse da Allah cewar sune. MUHAMMAD TURAKI, harufan sunan da manyan baƙi suka ƙara haskawa cikin idonta, sunan da yake ajikin wannan farar takardar da babu zanen komai acikinta saina sunansa da jan penti. Sunan da ta kasa karantawa a randa tai arangama da layar, kuma haka taita ajiyar takardar har sanda Amir ya shigo cikin rayuwarta, ya fara koya mata karatu har tazo ta iya haɗa harufan a wata takarda ta daban ta maimaita rubutun sunan, sannan ta iya karantawa. Ita dai bata san asiri ba, bata san ya ake yinsa ba, kuma bata san ya yake ba. amma zata iya rantsewa cewar aikin da waɗannan mutanen sukai asiri ne duk da bata ji sun ambaci wani abu da zai haska mata hakan ba, kuma babu tantanma asirin yana da alaƙa da sunan dake rubuce ajikin wannan farar takardar da aka maida ita laya. Abu guda kawai tasan da shi, shine idan har ta manta wurin da akai haƙan aka binne, to ba zata manta maganganun mutanen ba a lokacin da suke aikinsu. Aikin da suka gudanar a sanda ƙafafu suka ɗauke acikin wannan babban gidan da baya rabo da shiga da fice ako da yaushe, ranar da akai naɗin Yarima Abbas zuwa wani matsayi da bata san wane matsayi bane, taji dai labarin irin rikicin da aka sha akan naɗin a wajen Kaka da Yami. kuma zata iya cewa Allah ya nufeta da zuwa wajen ne saboda ta zama wata hanya ta tarwatsa mugun ƙudurin da ake shirinyi akan wani bawan Allah, tunda tsawon shekarun da ta ɗauka tana rayuwa cikin gidan bata taɓa zuwa wurin ba sai a ranar, lokacin kowa ya watse ana can masarauta ita kuma ta dawo dan ɗaukar ƙwaryar furar da ta dama zata bawa Amir. A lokacin bata san taya ma akai ta kai kanta wajen ba. Ita dai kawai ta ganta ne ta ɓullo ta cikin lambu, ta durƙusa ta ƙasa bishiyan ayaban ta fito, kuma tana fitowa ne taci karo da wasu mutane su uku suna kalle kalle dan tabbatar da babu kowa a wurin da alama basu da gaskiya. Bata kawo komai a ranta ba ta ɗau hanyar zata fito ta bar wajen sai kawai taji namijin cikinsu na cewa. _"nan wajen ne, tace daidai inda tafukan ƙafarsa zasu taka kamin ya kai ga shiga cikin lambun"._ _maganar ta fito ne daga bakin bafaden dake tare da wasu mata su biyu._ _"andai ƙi aji shawarata, amma ni gani nake yafi ace an binne acikin lambun gaban kujerar hutawan da yake zama...amma anan wurin zai iya ma tsallakewa ya wuce"._ _Ɗaya daga cikin matan ta faɗa._ _Ɗayar muryar ta amshe da faɗin,"ni sai da muka zo gudanar da aikinma sannan nake jin zuciyata ta cika da fargabar abinda zai biyo baya, sai nake ganin kamar ba zamu yi nasara ba asirinmu zai tonu"._ _Ɗayar matar dake tsaye kusa da ita ta wurga mata harara tana faɗin,"to kuwa mugun tunaninki ya ƙare akanki ke ɗaya...wannan ma ai baƙin ciki kike mana, kina jin irin uban kuɗin da Shugaba tai mana alƙawari amma shine kike wannan mugun fatan...mtswww gaskiya ba ki haɗu ba, to ni kam dai akan wannan ɗaruruwan kuɗin da naji babu kasadar da ba zanyi ba"._ _"zafa ki iya samun kuɗin kuma ki kasa jin daɗinsu. Tunda idan aka kama mu banu da wani mataimaki sai Allah dan ko ita shugaba sanin kanku ba zata waiwayemu ba gudun kar nata asirin ya tonu...ni kam ina tsoro sosai wallahi jikina na bani wani abun zai faru, dan ba lallai muyi nasara ba sai da mu faɗi"._ _A ƙufele ɗayar ta kuma cewa,"to zabiya uwar zancen ai sai kije ki faɗawa Jakadiya ke ba zaki iya wannan aikin ba saboda ga abunda kike gudu...kinga sai ta musanya ki da wadda take ganin zatai mata aikinta ba tare data ji wani ɗar ba...mutum da shegen son kuɗi amma sai uban tsoro"._ _Rufe bakinta kenan Bafaden ya washe haƙoransa da faɗin,"yo ta jewa Jakadiya da wannan zancen ai sai dai wata ba ita ba. Dan tun a wajen zata zama tarihi kamin ma maganar ta kai ga kunnen Shugaba. Da farko da aka kirawo ki aka tambayeki za ki iya baki ce ba zaki iya ba sai bayan da kika gama jin sirrinsu saboda rashin hankali. To wa kike tunanin zai barki da rai?"._ _"ni fa ba wani abu nace ba, hankalina ne kawai yau ɗin naji bai kwanta ba. Dan duk randa asirinmu ya tonu, ko ita Shugabar da muke taƙama da ita ba zata iya ƙwatarmu ba, ƙila ma ta ju
🏠