sai ta ɗora rigar sanyi me kauri akai, irin rigar sanyin nan me gashi a hularta. hular ta rufe kusan rabin fuskarta. fara ce sosai, me kyan fuska, hancinta har baka, idanuwanta manya. jelar gashinta ta zagayo ta gefen wuyanta ta sauka akan kafaɗarta, hakan zai shaida maka kitso ne guda ɗaya tal a gashin nata.
kallon gilashin windon take tana ganin yacca sauran ruwan sama ke sauka akansa. sam ba haka taso ba, ba haka taso lamarin ya tafi ba, sai da ta rufe ido ta buɗe sannan tace.
"ba haka muka tsara ba, ba shirin da muka yi ba kenan. abunda muka tsara shine Turaki zai mutu a wannan ranar kuma a wannan lokacin cikin wannan dajin, lissafin da mukayi kenan, mun lissafa tarihinsa zai shuɗe ne cikin ƙanƙanan lokaci, zamu goge hotonsa da sunansa da duk wani abu daya dangance shi daga wannan zuciyoyin guda biyu...to amma me yasa komai ya rushe?, lissafin da mukai ya hargitse?".
da shi take magana, saurayin dake zaune akan kujera yana fuskantarta, fari ne shima, me kaurin jiki, me siririn saje. shekarunsa ba wasu masu yawa bane, ƙananun kaya ne jikinsa blue jeans and red t-shirt long slip, sai facing cap baƙa daya saka. tarin gashin girarsa ya kusa haɗewa, kallonta kawai yake tunda ta tsaya a gaban windon, har zuwa yanzu da take magana da shi.
"kina nufin laifina ne kenan?".
a zafafe ta juyo ta fuskance shi tana ɗage hular rigar sanyin ta koma baya ne. "ƙwarai laifinka ne, idan da ace ba lusaran mutane kaje ka samo ba me zai sa shirinmu ya ruguje?.". sai tayi shiru taja dogon tsaki sannan tace,"now what will happen next?".
har yanzu bai ɗauke ƙwayar idonsa a kanta ba, sai daya miƙe tsaye sannan yace,"shi zai kawo kansa garemu next ba sai mun wahalar da kanmu ba".
matashiyar budurwar tayi masa kallon baka da hankali sannan tace,"ta ya?". yay guntun murmushi yace,"rauninsa mana". tace,"like how?". ta faɗa fuskarta na nunawa da rashin fahimta.
"Mahaifiyarsa, Maama, Hajiya Madina. ita zamu ɗauke, ita ɗaya zamu ɓatar Turaki yazo garemu da kansa, da ƙafafuwansa ba'a mota ba, da wannan damar zamu yi amfani wajen ganin mun cimma burinmu akansa, burinmu kuma mafarkinmu na ganin baya raye".
kamar bata gamsu da hakan ba a yacca ya gani a fuskarta, hakan yasa yayo tattaki zuwa gabanta, ya zagayeta sannan ya tsaya a bayanta.
"karki ji komai, babu wata matsala...wannan karan babu kuskure ina da yaƙinin hakan...wancan matsalar da aka samu yaran sun ce unexpected suka ji syring ɗin motar police, banda haka tuni sun gama da shi. kuma kinga muma bamu tsammaci hakan ba, ba ki karanta min da cewar hakan zai iya faruwa ba, da tunda wuri za'a aiwatar da komai...Hajiya Madina itace matsalarmu a komai shi yasa ya zama tilas dole mu fara ɗauketa daga kusa da shi".
ta sauke numfashi tace,"kasan mene?, a rayuwa raunin Turaki mutum biyu ne, Hajiya Madina da kuma Zaytuna, saboda haka tunanina ya sauya. zamu fara gamawa da Zaytuna kafin zuwan komai...Zaytuna tana da saurin yarda, tana da saurin sakin jiki musamman ga talaka, dan haka na san ta inda zan ɓullowa lamarin...kaima bance ka tsaya da naka aikin ba".
tana faɗar haka ta ɗauki wayarta da ke kan center table, ta nufi hanyar bedroom tana faɗar,"gobe zan bar ƙasar nan".
"nima haka". shima saurayin ya faɗa yana me ɗaukar car key ya fice daga apartment ɗin.
****
ƙafafun Turaki suka fito daga parlon, sanye yake da wata dakakkiyar shadda aqua colour da tayi bala'in yi masa kyau, ɗinkin boda ne da aikin sama. kansa babu hula sai dai sumar kan tasha gyara sai ƙyalli take yi. duk ya rame, ya fige, fuskarsa ta ɗanyi duhu, idonsa yayi jaa kuma ya faɗa ciki kamar mara lafiya, saboda kawai saka abu a ransa da yayi, yarinyar nan daya kaɗe wadda tsawon kwana uku sai jiya ta farfaɗo, tun ranar da accident ɗin ya faru baya iya cin abinci, rashin bacci da kuma rashin kwanciyar hankali duk sun dabaibaye shi.
ya kalli agogon wrist ɗinsa yaga goma harda minti biyu.
"Khalil". ya kira sunan Khalil wanda ke daga cikin parlo, ya amsa masa yana faɗin,"gani nan fa". Turaki ya ƙara magana da muryar ƙorafi,"kai indai za'a fita tare da kai sai ka ɓata lokaci".
a time ɗin ne kuma Khalil ya fito, suka jera tare zuwa part ɗin Baffa, bakinsu ɗauke da sallama suka shiga parlon, Baffa yana zaune da mijin ƙanwarsa Falmata SS Ƙasim Kurfi.
Khalil da Turaki suka zauna ƙasa suka gaishe su. Alhaji Ƙasim ya shiga tambayar Khalil wurin aikinsa. after few minutes Baffa ya dubi Turaki yace,"ya jikin yarinyar da ka bige?".
kansa na ƙasa yace,"ban sa ni Baffa, amma dai jiya da daddare likitan yace ta farka after mun baro hospital ɗin".
Baffa ya jinjina kai, kamar ba zai ce komai sai kuma yace,"amma dai you supposed to go and check on her, kai ne sanadin halin da take ciki, so alhakin kula da lafiyarta ya rataya a wuyanka na faɗa maka hakan tun ranar dana dawo, bai kamata a tambayeka jikinta ba kai tsaye kace baka sa ni ba...idan ni ne kai ko asibitin ba zan ke iya bari ba".
Turaki yace,"dama can zan tafi yanzun". Baffa yace,"t