NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 57 of 323

a kula da su, ko da ace sai dinga gutsirar naman jikinta ne, zatai ta haƙuri tana jurewa har Allah ya raya mata yaranta ta aurar da su, daga lokacin sai ta tafi ta bar masa gidan, ta bar masa Yasir tunda shi namiji ne, kuma tasan zai sami kulawa a wurin Yayansa Abdulhamid. Hayyo ya zuƙi sigarin hannunsa ya feso mata hayaƙin yace,"a fito min da tabarma". ta juya cikin parlon tana sa hannu ta goge hawayenta. Hamid na zaune ya kasa ƙarasa cin abincinsa saboda baƙin cikin da takaicin rashin kyan hali na mahaifinsa, ya kalli Yaya da tsananin tausayi, ya sauke ajiyar zuciya yana tuno da tasu mahaifiyar, itama haka tasha fama, dan zai iya cewa ma har yanzu Yaya bata ɗanɗani baƙar kuɗar da tasa mahaifiyar tasha ba a wurin Babansa. adu'a yake kullum, kuma yasan adu'arsu ta karɓu, lokaci kawai zasu jira sai dai idan ba'a raye, but dole-dole za'a zo time ɗin da mahaifinsu most regret all his past, lokacin da Allah ya shirye shi kenan. ya miƙe tsaye jiki a saɓule ya karɓi tabarmar da Yaya ta ɗauko, yana kallon yanda hawaye ke bin kuncinta zuciyarsa na tsinkewa. muryarsa can ƙasa gudun kar Hayyo ya jiyo shi yace da ita. "Yaya dan Allah ki bar kuka, komai lokaci ne kuma komai yana zama tarihi...kin san abinda zai kuma biyo baya idan yaga kina wannan kukan". ya faɗa tare da goge mata hawayen. tace da shi,"na gode Hamid". yace,"abincin nasa na kitchen ko?". ta ɗaga masa kai,"ehh yana ciki, cikin wannan filas ɗin daka siyo mana da azumi". Abdulhamid ya fice hannunsa riƙe da tabarmar. Hayyo na jingine da jikin bango yana ta zuƙar tabarsa cikin ƙwarancewa da jin daɗi. Hamid ya shimfiɗa masa tabar, Hayyo ya zauna har lokacin bai ko kalli Hamid ba. "sannu da dawowa Abba". kamar yanda ya tsammata dama babu amsa, dan shi zai iya cewa rabon da magana ta haɗasu da mahafin nasa tun azumi wata biyu kenan, haka ɗaya babu siɗi ba saɗaɗa, ko ya gaishe shi baya amsawa, hakana duk maganar da zai yi masa ba zai tanka masa ba. dan haka ya miƙe jiki a saɓule ya nufa soro inda ɗakinsa yake, ya ɗauko ƴar ƙaramar radio sabuwa ya dawo ya durƙusa gaban Hayyo. ya kamo gidan radiyon daya san nan ne zaɓin Hayyo, ya ajiye a kusa da shi. lokacin kuwa ana labaran siyasa, cikin ran Hayyo yaji daɗi sosai, dan shi a rayuwarsa daka masa kyautar kuɗi ma gwara ka basa radiyo, tana saka shi nishaɗi musamman idan labaran siyasa ake. amma ba zai taɓa nunawa Hamid yaji daɗi ba balle ma har wata adua ko godiya ta shiga tsakaninsu. jiya da shekaranjiya da bai saurara shirye-shiryen da yake ji ba duk jinsa yayi kamar mara lafiya, saboda tsohuwar radiyonsa taɓaci tun ranar da akayi wani mamakon ruwan sama, ta shige cikin ruwan daya cika ɗakinsa dalilin zubar da yayi. kuma babu kuɗi hannunsa dalilin ma da har ya ɗau wannan kwanakin babu ita. kuma yasan Hamid ya siyo radiyon ne saboda shi, tunda akan ƴan ƙanan yaran ya sauke ɓacin ransa na lalacewar rediyon, dan duk sai daya bi ya zane yaran, ko yau da safe da zai fita yaga shatin wayar daya tsulawa Maimuna a fuska bai baje ba, amma bai ko bi ta kanta ba tunda ƴaƴa ne da basa gabansa, su rayu ko su mutu babu abinda yay masa zafi, haka suyi lafiya ko rashinta ko a gefen yatsansa. ai yasha faɗawa ƴaƴansa da ku da shegu ɗaya na ɗauke ku, shi yasa bana wani ganinku da ƙima. zai fi muku ma ku nemi wani uban ko kwa ɗanji daɗi, amma a hakan dai Hamid yace masa a hakan kuma muke ƙaunarka Abba, muke alfahari da kai, duk tsanani ba zamu taɓa barinka ba, kuma zamu yi duk iyakar ƙoƙarinmu wajen ganin mun faranta maka, wajen ganin bamu saɓa maka ba. zamu maka biyayya, kuma zamu tsare mutuncinka. acikin radiyon aka sako waƙar ɗan ƙwairo, Hayyo ya kama bin waƙar yana buɗe flask na abincin da Yaya ta aje masa. kamar wanda yaga kashi daya ga shinkafar, amma a haka ya cinyeta tas. da yamma Yaran suka dawo daga makaranta, tunda sukai sallama suka ga Abban nasu a tsakargida suka kama raɓe-raɓe jikin bango. suna mugun tsoronsa, sunfi sakewa idan babu shi a gidan, idanma fita yayi sukan manta da shi. wataran Maimuna ta cewa Yaya ita gwara ma ace bata da Baba akan dai ta nuna Abba ace shine Babanta. a lokacin Yaya taita mata faɗa da cewar kata ƙara jin wannan zancen a bakinta, amma duk da haka Maimuna a makaranta bata amfani da sunansa, sai dai sunan Yayansu, Maimuna Abdulhamid haka ta ke using. *VISION APARTMENTS, Zurich, Switzerland.* a tsaye take a gaban windon parlon, windon dake ɗauke da manya manya gilasai, kalarsa ta haɗe da yanayin yanda hasken garin yake a lokacin. lokacin yammaci ne, yanayin garin na nuna cewa ruwan sama bai jima da ɗaukewa ba. sanyin danshin ruwan na ratsowa ya shigowa cikin parlon, wanda ya gauraye da sanyin ac da kuma ƙamshin dake cikin parlon. hakan ya haɗu ya bada wani sanyayyan ƙamshi me daɗi, kalar komai na parlon ruwan toka ne. sanye take da baƙin wando wanda ya ɗameta, hannayenta dake ɗauke da bangles acikin aljihun wandon, riga ce me ƙaramin hannu milk daga ciki
🏠