NOVEL SHARES -
uki nasu, anan tsakargidan suka shimfiɗa tabarma suka zauna suna ci, Yaya na faɗa musu idan suka ɓata wurin sai sun share. hakan yasa Hindu tace da Yayarta Maimuna,"ni dai kinga ban ɓata wurina ba ko".
wani saurayi da bai fi 26 years ba yayi sallama gidan, dogo ne sosai kuma ɗan siriri kamar sandar kara, fuskarsa kewaye da saje wanda ya haɗe da gemunsa, ga kuma gashin bakinsa shima da yaywa fuskarsa kyau.
yaran suka amsa sallamar tasa suna yi masa sunnu da zuwa, ya amsa musu sannan ya shiga ɗakin kishiyar mahaifiyarsa da sallama a bakinsa.
ta gama cin abinci tana siɗe yatsu lokacin, ya zauna kan kujerar parlon da duk taji jiki. ta kalle shi da tausayi tace,"an dawo?".
sai dai ya sauke ajiyar zuciya sannan yace,"ehh Yaya sannu da gida". tace,"yauwa, ya wurin ɗinkin naku?".
yace,"ɗinki babu daɗi Yaya, yanzu ma gudowa nayi saboda kaina da nake jin kamar zai fashe, jiya kwana nayi ban runtsa ba ina kan ɗinkin ƴan bikin nan".
tayi murmushi tace,"to ya za'ai, neman halal da wuya, wataran kuma za'aji daɗi da izinin Allah...amma dai ka kammala musu ɗinkin nasu ko?".
Hamid yayi gajeriyar dariya yace,"yanzu ma da su muka gama rigima ai, Suhaila na cewa ba zata ƙara kawo min ɗinki ba balle ranta ya ɓaci, kuma dan nace idan tayi haka ta burgeni shine tayi fushi ta tafi, inaga da kuka ma ta wuce".
Yaya ta miƙe tana cewa,"an dai ji kunya wallahi, budurwar taka ma sai kayi mata halinku na teloli".
gajeriyar dariya kawai yayi baice komai ba, Yaya ta miƙe tace da shi,"ka ɗauko abincinka kaci ka koma ka ƙarasa aikin mutane, bana son saɓa alƙawari Abdulhamid".
ta shiga ɗaki don shirya Yasir, shi kuma ya wuce kitchen ya ɗauko abincinsa. yana cin abincin ne ƙannensa da suka shirya zasu wuce makaranta suka zo suka ce da shi kuɗin makaranta.
yana kallon Maimuna yace,"har lokacin biya ya yi?". ta ɗaga kai alamar eh tare da cewar,"shekaranjiya da jiya ma duk sai da aka fito da mu, bamu shiga aji ba".
yace,"kuma dan shirme shine baku faɗa ba".
tace,"Kawu ai ban sani ba ko baka da kuɗi".
yayi mata wani kallo yace,"ina ruwanki da rashin kuɗina, karki ƙara yin irin haka".
tace,"to Kawu".
Yaya ta fito daga ɗaki tana cewa,"ba laifinta ba ne ni nace su bari ba yanzu ba".
yasa hannu a aljihunsa yace,"a'a Yaya to ai zuwan nasu baida amfani kenan tunda ko sunje ba barinsu ake suyi karatun ba, kuma ni ai na sami kuɗi kwana biyun nan".
tace,"to Allah ya ƙara horewa dai". ya ɗauki dubu uku ya bawa Maimuna ƴar shekara goma yace,"ungo ki bawa Malam Ado, kice na Yasir da Hindu ne, dan Allah suyi haƙuri su ɗaga ƙafa jibi insha'Allahu za'a bayar da naki".
ta duƙa ta karɓa suna yi masa adu'a, sannan Yaya tayi musu adua suka tafi. fitarsu babu jimawa mai gidan Yayi sallama, sallamar da ta hassada faɗuwar gaba a zuciyarsu Hamid.
"Shema'u! Shema'u". kiran da me gidan keta ƙwalawa kenan, Yaya ta miƙe jiki a sanyaye ta fita tana cewa,"sannu da zuwa".
yay mata wani banzan kallo yana zuƙar tabar dake hannunsa sannan yace,"sai yanzu kika ji kiran nawa ko amsawar ce ba ki ga damar yi ba?".
bai jira cewarta ba ya ɗora da faɗin,"mutuniyar banza da wofi kawai, to ki gama rashin mutuncinki wallah idan banga dama ba aljannah dai ba za ki shigeta ba, tunda a ƙasan ƙafata aljannar taki take, kuma har saina ɗaga miki za ki shiga...kuma indai don ta ni ne na rantse sai da ki zama ƴar kallo, kina ganin mata na tururuwar shiga ke kina daga gefe can".
*Pls Vote, Comment and Share.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*17*
Yaya dai tayi shiru bata tankawa maganarsa ba, idan ma tace zata basa haƙuri wani sabon cin mutuncinne zai biyo ba, to shirun shi yafi alkhairi, but down deep in to her heart zafi ta ke ji, wannan halin na mijinta bata so, ƙaddara dai ta riga fata, ta ɗauki aurenta da Hayyo matsayin wata jarabawa daga ubangiji, kuma tana roƙon Allah ya bata ikon cinyewa.
ta mayar da tarin ƙwallar da ta cika idanunta. ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗago ta kallesa tace,"a ɗauko maka abinci?".
Hayyo yayi mata wani kallon banza yace,"mayya kawai wadda kare ya cinye zuciyarta, indai haƙuri ne naga Halima ma, dan haka kema muna nan wannan kafirin haƙurin naki zai kaiki maƙurar da za ki bar gidan nan da ƙafafunki. yo guda nawa kuma akayi?, saki dai kike so saboda ki tafi da hujja to ni ba zan sakeki ba dan bana yinsa, musulmin ƙwarai ne ni sam bana son al'arashin ubangiji ya girgiza".
Yaya ta girgiza kai kawai tana me cike da takaici, ita kanta ta sa ni haƙuri yayi kaɗan ya barka ka zauna da Hayyo, sai dai darajar ƴaƴa, tun bayan aurenta da shi daya sami biyan buƙatar kansa ya fito mata da asalin halinsa wanda yake ɓoyewa a lokacin aure, ta kuma san asalin waye shi wanda yake ɓoyewa idan yaje neman aure.
tunda ta haihu ta bar zamansa ta koma zaman ƴaƴanta, ba zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta a wurin uban da bai san darajar ƴaƴa ba sam, ba zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta su gantale ba, gwara ko Hayyo zai kasheta ta zauna t