NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 55 of 323

da gadonsu suka iso wajen motar Turaki, Khalil ne ya buɗe bayan motar, yayin da nurses suka janyo yarinyar suka ɗorata akan gadon suka yi ambulance da ita. cikin sanin makamar aikinsu wasu nurses ɗin suka shiga goge jinin da yake kan fuskarta, yayinda wasu daga cikinsu kuma suka shiga ƙoƙarin ganin sun saita numfashinta ganin cewar da ranta. duk aikin da suke gudanarwa akan idon Khalil dake tsaye hannayensa acikin aljihunsa, kuma tsananin mamaki ya wanzu a fuskarsa lokacin da suka gama goge fuskarta tayi tas, wa zai gani?, yana gani dai-dai kuwa?, ba yarinyar daya kai asibiti bace ɗazu, Fillo ce fa me aikinsu. sai kawai ya fuskanci wurin da Hajiya Madina da Turaki ke tsaye har yanzu, tana ta aikin tattaɓa shi da kallon ko'ina a jikinsa kamar wadda ta ɗauki tsawon lokaci bata gansa ba. Turaki yake kallo ba Maama ba, kallonsa yake yana recalling back wani moment da Fillo tace masa,"tsoronsa nake ji". haka ta faɗa masa jikinta na kyarma, sanda ya shigo kitchen zai ɗauki abu. tambayarta yayi kawai menene ya faru yaga kamar a tsorace ta ke, shine ta faɗa masa hakan, kuma ko da ya tambayeta me ta ke tsoro sai ta kalli ƙofar kitchen ɗin sannan tasa hannu ta goge hawayenta tukunna tace masa,"Hammah". "me yasa to?, yayi miki wani abunne?". tambayar da yayi mata kenan. amma amsar da ta ba shi ita ta ɗaure masa kai,"babu abinda yayi min amma yace zan cutu idan har ban bar inda yake da rayuwa ba, wai haka yaji zuciyarsa tana faɗa masa...kuma ni bana so mu daina wannan aikin saboda da kuɗin muke rufawa kanmu asiri, kuma ni wallahi Hammah Khalil banda mugun nufi, bana cutar da kowa sai ƙoƙarin ganin na kare wanda za'a cutar". abunda ta faɗa masa kenan tana hawaye, bai ce mata komai ba a lokacin, kawai ya ɗauki abinda zai ɗauka ya fice daga kitchen ɗin. kuma yana zuwa ɗakin Turaki ya maimaita masa abunda ta faɗa, Turaki bai mu sa masa ba, hasalima ce yayi masa. "Khalil haka jikina yake bani, haka zuciyata take faɗa min...kamar yanda nake jin Granny zata iya cutuwa idan muna rayuwa a wuri ɗaya, haka nake ji akan wannan yarinyar itama". Khalil ya sauke ajiyar zuciya sanda tunanin nasa ya katse, sukai magana da wani police sannan yayi tattaki ya ƙarasa wurin su Hajiya Madina. yana zuwa ya sanar mata cewar,"Maama DPO yace zamu wuce". ta haɗiye wani yawu sannan tace,"pack anything that is very important daga cikin motar nan ka kaisu cikin taka...sai a bar wannan anan, ko ta zama rabon wani ko kuma in Allah yayi azo a ɗauketa daga baya, tunda babu me drving ɗinta yanzu". Khalil na kallonta da tsananin tausayi yace,"wani police ɗin yay driving ɗinta, ko kuma ni na tuƙa, ku sai ku tafi tare da wani acikinsu". tana kama hannun Turaki ta riƙe tace,"a'a mu tafi dai taren, wani cikin nasu yaja wannan ɗin, sai ka faɗa musu key ɗin na jiki". da faɗin hakan taja hannun Turaki suka yi gaba, shi kuma Khalil ya shiga motar ya ɗauko wayarsa sannan yabi bayansu. hakan akayi, cikin police mutum ɗaya yay driving motar Turaki. sai da suka yi nisa a tafiya sannan Khalil yace,"Hammah kasan wa ka kaɗe?". Turaki bai ce komai ba, kuma sai a wannan furucin nasa Hajiya Madina tama tuna da wata halitta da aka buge, ta manta da wannan batun ta ɗanta kawai take, kuma tana ganinsa lafiya shikenan ta ƙara mancewa da batun gaya mata da yayi ya buge wani. tace da Khalil,"koma wacece fatanmu ta rayu, idan ta dawo hayyacinta sai ta faɗi inda take ko kuma akai sanarwa gidan radio". Khalil yace,"Maama ai wadda muke tare ce, Fillo ce". da maɗaukakin al'ajabi Turaki da Hajiya Madina suka waro ido a tare. tace,"wace kuma Fillo?". Khalil yace,"me aikinmu dai". Turaki dai bai ce komai ba, bai san ya zai kimanta yanda yaji maganar acikin kansa ba. Hajiya Madina tace,"me yasa kace itace Khalil?". ya sauke numfashi yace,"idan munje asibiti za ki gani Maama". *Taraba.* ɗan ƙaramin tsakar gidan share yake tass, sai simintin yay haske kamar sabo. daga ɓangaren yamma wata ƙaramar ƙofa ce ta langa-langa, inda yake nan ne kitchen. wata dattijuwar mata ta fito daga ɗaki wanda yake daga ɓarin yamma ta buɗe ƙofar kitchen ɗin ta shiga. ta sunkuya ta sauke tunkuyar daga kan gawayin da take girki da shi. tana saukewa sai ga ƙaramin yaro da bai wuce shekara bakwai ba yazo wajenta yana faɗin,"Yaya ki zuba min abincin kar mu makara". sunan da suke kiran mahaifiyar tasu da shi kenan Yaya. ta kalli yaron sannan tace,"to Yasir yanzu zan zuba maka, ai kaga sai yanzu na sauke". ta faɗa a sanda ta ke ƙoƙarin ciro farantan roba daga cikin kwandon wanke-wanke. ta shiga zuba farar shinkafa da mai da yajin a faranti daban-daban, tana ta jin labarin da Yasir ke bata na yacca ake duka a islamiyar tasu. bayan ta gama rabon abincin tace da shi,"kira su Maimuna su zo su ɗauka, wannan kuma riƙe namu ne ni da kai, ka riƙe da kyau". ya karɓi filas ɗin abincin ya wuce yana ƙwala kiran Maimuna da Hindu kuzo ku ɗau abinci inji Yaya. yana shiga ɗaki Yaran suma suka fito suka ɗa
🏠