NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 54 of 323

na magana, kuma har lokacin jibgegen mutumin na shaƙe da wuyan turaki da hannu ɗaya, ɗayan kuma ya toshe masa baki da hanci, a taƙaice dai babu ta inda iska ke samun shiga lungs na Turaki. yana ji aka buɗe ƙofar baya, ya hangi siririn mutum ta cikin mirrow ya duƙa akan yarinyar, bai san waye ba dan baiga fuskarsa ba. har yanzu mutanen magana suke da junansu, kuma har yanzu ya kasa jin komai da suke cewa, ya rufe idonsa yana kokawa da cikinsa dake so ya fitar da iska. ƙirjinsa yake jin yana yi masa zafi, ji yake kamar zai mutu, fatansa ɗaya ne a lokacin, kar ya mutu a lokacin sai a hannun Maama, so yake ya mutu yana kallon fuskarta. wasu adadin sakanni suka wuce ta cikin kansa, a lokacin da ya gama saddaƙar da tafiyarsa lahira, a lokacin ne yaji words guda 22 sun shiga cikin kunnensa, kalmomin da suka fito daga bakin siririn mutumin dake riƙe da hannun yarinyar da ya kaɗe. _"yarinyar nan zata yi mana amfani, da sauran ranta. ni ko da ta mutu ma ina sonta a hakan, dole ne zan moreta saboda na kwaɗaitu da ita"._ furucin da mutumin yayi kenan, kuma furucin da ya sami nasarar shiga cikin kunnen Turaki har ya zarce zuwa cikin zuciyarsa ya dunƙule a waje ɗaya. ƙarfi da kuzarin da Turaki yake jin ya rasa na ƙwatar kansa shine yazo masa acikin giftawar sakan ɗaya, wasu manyan jijiyo suka bayyana a hannayensa da goshinsa, tamkar idonsa akan siririn mutumin yake, kuma kamar yasan abinda yake shirin aikatawa, dan haka kawai zura hannunsa yayi ta baya ya damƙi hannun mutumin wanda yake shirin ɗaukar yarinyar, sannan yasa ɗaya hannun nasa yana ƙoƙarin ya cire hannun ƙaton daga bakinsa. damƙar da Turaki ya yiwa siririn mutumin ta shiga ratsa jikinsa, mutumin ya ɗaga murya wajen cewa wanda ke riƙe da Turaki"gayen nan fa bai suma ba, ya riƙe min hannu kuma kamar ba zan iya ƙwacewa ba, bugawa shege bindiga akai". da maganar da yay, da ɗauko bindigar da ƙaton yayi, da samun nasarar da Turaki yay na cire hannun mutumin daga bakinsa, suka haɗe lokaci ɗaya da ƙarar jiniyar motar ƴan sanda dake tashi daga can nesa. babu shiri ƙaton mutumin ya saki Turaki ya falla da gudu zuwa motarsu, shima siririn ya fizge daga hannun Turaki ya falla zuwa motar, ashe basu biyu bane kawai, suna da yawa, kamin Turaki ya zuro ƙafarsa daga cikin motar ya fito tuni sun bar wajen sai tashin ƙurar motarsu. tsayawa yayi yana bin bayan motar da kallo, so yake yaga lambar motar ko zai samu wata shaida amma duhun dake cikin idonsa ya hana. can kuma tunaninsa ya dawo kan yarinyar, dan haka da sauri ya buɗe bayan motar, ganinta yasa shi sauke ajiyar zuciya. ya shiga tattaɓata yana jin kamar ko sunyi mata wani abu ne. ji yake ba zai iya cigaba da jira ba, barin wajen zai yi, idan shi ya cutu ba komai ba ne, amma baya so wani abu makamancin wanda sheɗanin can ke faɗa ya faru da yarinyar, dan haka cikin azama ya koma seat ɗin driver zai tashi motar, dai-dai nan kuma motar Khalil ta ƙaraso wajen, motar police na biye da su a baya, yayin da abulance ke bin bayan ta police ɗin. Khalil na yin parking Hajiya Madina ta fito daga cikin motar, ƙafarta ma ko takalman babu ta barsu a mota, a guje ta tsallaka side ɗin da motar Turaki take har tana bigewa da dutse, ko gabanta bata gani da kyau, burinta ɗaya ne a lokacin taga lafiyarsa, hawayen nata ma nema suke su tsaya da zuba saboda kamar sun ƙare. tunda ta fito daga motar ƙwayar idon Turaki ta tsaya cak akanta, kamar wanda aka sassaƙa haka ya kasa ko da motsawa, kallonta kawai yake, kallonta yake tana tahowa gare shi da irin tashin hankalin da bai taɓa ganinta aciki ba, da wannan tausayin na uwa shimfiɗe a fuskarta, da wannan tsoron na mahaifiyar da bata son rasa ɗanta acikin ƙwayar idonta, yana gani tayi tuntuɓen amma ya kasa motsin da zai fita ya tareta daga faɗuwar, alhalin kuma so yake ya fita ya rungumeta, amma ya kasa, ƙafafunsa sunyi nauyin da ba zai iya ɗagasu ba, sai kawai ya rufe ido wani hoto na can lokacin baya yana haska masa. Hajiya Madina na ƙarasowa ta buɗe motar hannunta sai karkarwa yake. "me babban suna". sunan da ta kirasa kenan a sanda ta buɗe motar ta gansa kamar gunki. kuma ganinsa a hakan sai idanuwanta suka haska mata hoton wani abu da ba zata iya jurar gani ba, haka ma zuciyarta ta ɗarsa mata faruwar wani lamari da ba zata iya ɗaukarsa ba. a hankali ta shiga sauke ƙafafuwanta har gwiwarta ta kai ƙasa, sai kawai ta kifa kanta akan ƙafafunsa ta fashe da wani gunjin kuka me taɓa zuciyar duk wani me sauraro, irin kukan da duk wani me rauni yaji shima sai yayi. sai a wannan lokacin ne Turaki ya iya motsa hannunsa ya kamata ya ɗagata, sannan ya fito daga cikin motar, ya kasa magana haka itama ta kasa, kuka takeyi shima hawayen yake, ya jata zuwa jikinsa yayi mata wata runguma, itama wata runguma tayi masa wadda take daban da tasa, har tsakiyar babban yatsansa yaji rungumartata, irin rungumar da rabon da tai masa ita tun yana yaro. likitocin dake cikin ambulance ɗin suka fito cikin hanzari,
🏠