NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 52 of 323

tarin adu'oi yasa hannu ya juyo da ita daga kifen da take, jini duk ya wanke mata fuskarta, babu ta yanda za'a ganeta. ya janye gashin kanta daya baje akan fuskar. ya ƙara furta innalillahi sannan ya kama hannunta wanda yake a damƙe kamar ta riƙe wani abu, ya taɓa yaji artery ɗin wurin na motsi. ya sauke ajiyar zuciya, ji yayi kamar yayi hamdala a lokacin. kansa ya ƙulle da tunanin ma me zai yi, kuma tana ina zai fara, kuma me ya kamata yayi. yana riƙe da hannun tsawon wucewar wasu daƙiƙu sannan ya miƙe da sassarfa ya buɗe bayan motarsa, ya kunna fitilar motar sannan ya dawo ya ɗauketa ya sakata a motar, yarinya ce ba wai babba ba, hannunta guda ɗaya ya sauka akan kafaɗarsa, ya ɗauke yana kallon hannun nata da yake a damƙe. ƙwayar idonsa ya tsaya cak a kanta, wacece?, me ta fito yi a irin wannan lokacin?, daga ina ta ke?. zuciyarsa ta ƙara ɗarsa masa anya kuwa mutum ce?, sai yayi saurin ɗauke idonsa daga kanta ya sauke ajiyar zuciya. ya rufe bayan ya dawo mazauninsa yana ƙara volume na karatun daya kunna. yana kunna motar ya ɗauki wayarsa ya kira lambar Hajiya Madina, dai-dai lokacin daya hau kan titi ta ɗaga wayar. muryarta tattare da tarin bacci ta kira sunansa tana mai mamakin kiran nasa a irin wannan lokacin ƙarfe ɗaya na dare. daga ɓangaren da take ta miƙe zaune akan gadonta cikin faɗuwar gaba ta kunna bedside lamp. "Hammansu". ta kira sunansa cikin wani amon sauti da bata san tana da shi ba. a wannan lokacin Turaki kamar zai yi kuka, ya juya baya ya kalli yarinyar sannan muryarsa dake ɗauke da tashin hankali yace,"Maama na kashe rai". "what?, ban ji da kyau ba Hammansu". tayi maganar a ɗage tana durowa daga saman gado babu shiri. "Maama ban san ya akai ta shigo gabana ba, its like kamar jefota akai". a rikice yay maganar kamar yanda yake a rikice. Hajiya Madina da ta faɗa toilet tana wanke fuska don ta wartsake daga mafarkin da take tunanin tayi tace,"kana ina Hammansu?". yace,"ban san inda nake ba Maama, ina dai kan wani titi. har yanzu banga wani wuri dana sa ni ba, banga asibiti ba ko ɗaya Maama...kamar da sauran ranta ina tsoron karta ƙarasa mutuwa". muryar Hajiya Madina a ɗage tace,"wai wacece ne? kuma me kake so ka faɗa min?". ya ƙara juyawa ya kalli bayansa sannan yace,"accident nayi Maama, kuma ban san wa na kaɗe ba". tace,"na shiga ukuna, to da yaushe ka fita daga gida ban sa ni ba?, daka fita ma ina zaka je me Babban suna?". ya kulle idonsa sannan yace,"Maama duk ba wannan ba, bana so ta mutu ta sanadina, bana cikin hankalina wallahi ban san lokacin dana kaɗeta ba, na kasa fita daga inda nake, kamar ma na bar garin gombe gaba ɗaya". Hajiya Madina ta zube a gefen gadon da ta ke ta fashe da kuka. wucewar daƙiƙa biyu ta sauke numfashi tace,"ka nemi wuri kayi parking, ka kunna datarka...zamu bi location ɗinka yanzun nan...kai ta biya innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, zaka samu mafita kamin ƙarasowarmu insha'Allahu, take care kaji, kama kashe motarka kawai". yayi shiru bai ce komai ba. ta katse shirun da cewar,"Hammansu kana jina?". idanuwansa a rufe yace,"Maama idan ta mutu fa?". yay maganar da tsananin rauni. tace,"i beg you stop negative thinking, ba zata mutu ba da yardar Allah, gamu nan tahowawa". tana faɗar hakan ta kashe wayar, tabi layin Khalil da kira, kira na farko dana biyu duk bai ɗaga ba sai ana uku, cikin bacci ya kira sunanta. tunma bai ƙarasa faɗar sunan ba tace,"Khalil ta shi a barcin nan muna cikin tashin hankali, tayar da mota gani nan". Allah ya taimaka Khalil baida saurin bacci, yana jin haka ko tambayar ba'asi bai jira yi ba ya diro ya zira jallabiyarsa ya fita. Hajiya Madina ma zani ta ɗaura akan kayan baccinta sannan ta zura hijabi ta fito da warikan takalma, sai salati ta ke yi. *Please Vote, Comment and Share* *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _avoid any mistake plss🙏._ *16* *Shongom LGA, Gwandum, Yabayo village.* rubutun da map location ɗin ya zana kenan ajikin wayar dake riƙe a hannun Khalil. with high speed yake drving motar kamar zai tashi sama. adu'a yake cikin ransa Allah ya kaisu lafiya, idan ba haka ba za'a iya samun gagarumar matsala a wannan tuƙin nasa, saboda kukan mahaifiyarsa dake gigita hankalinsa da tunaninsa, da kuma tunanin halin da ɗan'uwansa, Yayansa mafi soyuwa a gare shi yake ciki. tunda suka taho kuka kawai takeyi, duk wata magana ta kwantar da hankali ya faɗeta amma taƙi tasiri a gareta, ya rasa me kuma zaiyi, yasan dai ba zata taɓa natsuwa ba har sai sun isa inda take da buri, to amma atleast yana so ta tsayar da wannan kukan nata ko dan ya samu yayi tuƙin nan lafiya. ya ƙara kallonta a karo na babu adadi yana jin zuciyarsa na tsinkewa, ya cine fuska ya wani daki stearing da mugun ƙarfi, kamar ya fasa ihu haka yake ji. shi amsar ma da yake so ya sani wai me ma ya fitar Hammansu a wannan salasainin daren?, shin ba ya shiga bedroom ɗinsa yayi masa gud night ba, ya tarar kuma lokacin har ya fara bacci. ya sauke
🏠