kuma kamar wadda aka tsikara tayi zumbur ta miƙe ta fice daga ɗakin.
lokacin da Kaka ta fito daga ɗaki sai tayi tunanin ko ta shiga banɗaki ne, hakan yasa bata nemeta ba, har ta girgiza kai tana faɗar Allah ya kyauta raki irin na Fillo, bata san ya za'ai ba idan tazo haihuwa.
kuma sai bayan minti goma sai ga Maijidda ta shigo ɗakin neman Fillo, Kaka wadda har ta kwanta a lokacin tace mata,"yo aini nayi zaton wurinku ta nufa, ta shigo tana kukan ciwon ƙafa to nama zaci banɗaki taje, dana ji shiru kuma nace ƙila tayi wajenku".
Maijidda ta zauna tace,"bata je ba Kaka". ta faɗa muryarta na nuna rashin jin daɗi. Kaka tace,"ƙila can cikin gidan ta koma, yanzu ai zaki ganta tunda ba can dai zata kwan ba, yanzu haka tayi mantuwar wani abu ne shi yasa ta koma".
Maijidda dai tayi shiru bata ce komai sai ɓata rai ta ke, Kaka na kallonta dai bata tambayi ba'asi ba, saboda tasan kwanan zancen, akan dai Fillo ne da basa zama tare yanzu shine take ta yin wannan kumburin.
shiru-shiru Fillo bata dawo ba sama da kusan rabin awa, Maijidda lokacin itama har ta fara hamma. ta fara masifar ita wannan aikin bata sonsa sam, zata sa Yami ta nemi wata yarinyar akai musu a ƙyale mata ƙawarta.
Kaka tace,"to wai ke Maijidda iyaka akayi miki da shiga cikin gidan da ba za ki dinga binta ba ko me?, ba sai ma ku dinga yin aikin tare ba".
Maijidda tace,"ni bana son shiga wurin da za'ake min gani gani Kaka, tunda sun san basu ɗaukeni aiki ba ina zuwa za'a fara min tambayar yanda Uwata ta haifeni".
Kaka tace,"aiko dai kin yiwa Hajiya sharri dan ba haka halinta yake ba...zaman jira ne kuma sai kita zama karki yi bacci har sai ta dawo, waya san ma ko acan zata kwana tunda har ta kai wannan lokacin...to ni dai na kwanta sai da safe".
Maijidda dai tai zaune jugum tana sauraron radion Kaka dake kunne, har lokacin da gidan radion suka tashi a aiki. daga ƙarshe dai data gaji da jira ta tabbatar Fillo ba dawowa zata yi ba ta tashi ta rufe ƙofar ɗakin sannan tabi Kaka ɗakin ta kwanta itama a inda Fillo ke kwanciya.
ƙarfe sha biyu da minti goma sha biyar na dare a lokacin, motar Turaki akan hanyar da bai san ya akai ya biyo cikinta ba. hanyar tayi duhu dulum sai haushin karnuka dake tashi. gefe da gefen hanyar shukoki ne na masara da shinkafa da alama dai gonaki ne a wajen.
ya rasa me yake damunsa gaba ɗaya, shi dai yana zaune yaji kawai yana so ya fito yasha iskar gari, kuma da har ya wuce Lambu sai ya koma ya ɗauki key ɗin motarsa ya fito.
da farko gidan Mai Martaba yaso ya nufa, sai kuma zuciyarsa ta sauya masa ra'ayi, ya dinga bin titina yana sauka daga wannan zuwa wannan. tuƙin kawai ba dan ya san inda hankalinsa da tunaninsa yake ba, shine har ya shigo wannan layin da bai san ina motar ta kawosa ba, dan ba shi ya kawo kansa ba..
wuri ya samu yayi parking ya fito ya jingina da jikin motar yana fuskantar inda shukar shinkafar take, idonsa akan Shukar yake amma ba ita yake kallo ba, ba kuma tunani yake yi akanta ba, wucewar minti goma ya kalli agogon wayarsa yaga ƙarfe sha biyu da rabi a lokacin.
sai kawai ya buɗe motar ya koma ciki, ya kuma nausawa cikin gonar ba tare da tsoron daren ba.
driving ɗin yake with high speed kamar me shirin barin gari, ba ganin gabansa yake da kyau ba a lokacin duk da fitilar motar daya kunna. yasa hannu a rigar kujera zai ɗauki glasses ɗinsa sai ya tuna ɗazu da zai karanta jarida yasa Nihal ta ɗauko masa.
yay guntun tsaki kawai, jin komai yake babu daɗi, cikin kansa kamar babu komai, kamar ma ba'a cikin duniyar yake ba.
da hakan yasa hannu ya daki stearing da ƙarfi, horn ya kama nan wani Kare dake gefen wata bishiya ya tashi da gudu ya tsaya a tsakiyar hanya, ganin hakan yasa Turaki ƙara danna horn da ƙarfi, nan karen ya bar wajen da gudu. tsaki kawai yake jerawa, ya jera yafi ƙarfin ƙirgen yatsu, bai san meke damunsa ba, bai san meke masa daɗi ba, bai san me zaiyi ya samu salama ba.
kawai sai ya tsinci idonsa da haska masa wasu shafuka acikin al-qur'ani, da haka kuma zuciyarsa ta fara karanta abunda ƙwayar idonsa ke haska masa.
sannu a hankali yaji yana samun relief, nan ya kai hannu ya kunna alqur'ani, ƙira'ar Shuraim ta fara tashi acikin motar.
ba tare da ya sani ba, haka kuma ba tare daya ankare ba yaji ya daki abu. gabansa ya faɗi, bakinsa ya furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, duhun idanunsa ya washe lokaci ɗaya, yayi mugun taka burki babu shiri ganin yana neman bi ta kan abinda ya buge wanda bai san mene ba a lokacin, ƙarar taka burgin ya bada wani ƙara ƙuuuu, tunaninsa ɗaya ne wata dabbar ya kaɗe.
sai dai me zai faru?, a lokacin daya fito daga motar cikin hanzari sai kawai yaga mutum yashe a ƙasa cikin jini, macece, amma kamar ba mutum ba haka zuciyarsa ta faɗa masa.
saboda haka kamin ya kai ga tsugunawa gaban wadda yake da tabbacin ta riga ta zama gawa sai daya kalli ko'ina da ina, yaga babu kowa kuma babu alamun kowa, sannan ya tsuguna yana mai jin fargabar kai hannu ya taɓata.
bakinsa ɗauke da