NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 50 of 323

in tai tambayar da zata mata sai ga Khalil ya ƙaraso wajen, yana zuwa yace,"ɗauko mayafinki". kamar zatai kuka tace da shi,"Hamma Khalil ai naji sauƙi". baice komai ba Hajiya Madina tace,"me ya samu ƙafar taki dama?". idanuwanta suka yi narai-narai tace,"gurɗewa nayi ɗazu da zan sauko daga bene". Hajiya Madina tace,"ki dinƙa kulawa Fillo, je ki shirya kuje ya kaiki asibiti, duk ƙanƙantar ciwo bama barinsa sai anga likita". ba don tana so ba sai dan ba yarda zata yi, saboda bata son yi mata musu. a mota ta sami Khalil na jiranta, ta buɗe baya ta shiga, nan ma sai shine ya buɗe mata don bata iya ba. ƙamshin cikin motar daya gauraye da sanyin ac ya bata da wani daɗi, ta buɗe ƙananun ƙofofin hancinta ta zuƙe ƙamshin tana jin wani sanyi a ranta. Khalil nata bin waƙar turancin dake tashi a motar, ita dai tayi shiru sai bin titi take yi da ido tana kallon hanya, rabon da ta fito har ta manta, kullum suna wuri ɗaya idan ba wani taro za'ai a masarauta ba shine har da su ma'aikatan ake tafiya, Maijidda ma ta fita yawo itace Yami ke yawan aikenta, ita kam Kaka da ta aiketa ma gwara taje da kanta. a harabar asibitin yayi parking, tayi ƙoƙarin ganin ta buɗe motar da kanta, ta fito sannan ya sakawa motar key. "idan munje ki faɗawa likitan harda ciwon baki na damunki". ya faɗa da sigar zolaya, tai ƴar dariya bata ce komai ba, tabi bayansa zuwa cikin asibitin. wani babban likita ne ya dubata, sai dai tasha kuka sosai saboda matsa ƙafar da akayi, sunan Kaka kuwa ta kira yafi sau biyar. a wani pharmacy Khalil ya tsaya ya siya magungunan da aka rubuta masu yawa harda allurai. tunda suka ɗauko hanyar dawowa Fillo ke jin kanta na wani mugun sara mata, Khalil na kallon duk wani motsinta ta cikin mirrow, sai cije fuska take yi hawaye na sauka a saman kuncinta, bai ce mata komai ba don duk tunaninsa ko har yanzu kukan allurar ne. ita kuwa kanta ke mata wani azababben ciwo, yayi mata nauyi kamar an ɗora dutse, ga shi sai take jin tsoron da bata san dalilinsa ba, ji take kamar ana tsoratata acikin kanta, kuma kamar kiranta ake ana tazo. tasa hannu ta damƙe zanin jikinta, daidai lokacin da Khalil yayi parking a compound. kusan tare suka fito daga motar, ya bata ledar drugs ɗin yana yi mata sannu. karɓa tayi tare da yi masa godiya sannan tayi masa sai da safe. ɓangarensu ta wuce bata wani biya ta yiwa Hajiya Madina sallama ba, tana tafe tana haɗa hanya saboda ganinta dake neman ɗaukewa gaba ɗaya, a yanzu ta manta da ciwon dake ƙafarta, ta ciwon kan kawai take yi. duk da uban hasken fitulu dake gauraye da harabar gidan amma ita wani duhu take gani na daban, ta damƙe kanta haka har ta kai ɗakinsu, kuma sai lokacin ne taji idonta ya washe, ta buɗi baki tai sallama cikin ɗakin. jin yanda tayi sallamar Kaka ta kafe ƙofar ɗakin da ido har ta shigo, tabi ta da ido har ta nemi wuri ta zauna tana jefar da ledan tulin drugs ɗin. sannan ta ƙara fashewa da wani kukan. Kaka ta katse lazimin da take yi tace,"ke Lafiya?". tayi shiru bata ce komai ba. Kaka ta ɗaga murya sosai,"kin san dai bana son shashanci ko Halimatu, menene ya faru?, wani kuskuren kika aikata?". ta ɗago tare da girgiza kanta alamar a'a. Kaka tace,"to menene?, wadda kuka baya yi mata wahala". bata yi magana da baki ba sai nuni ta yiwa Kaka da ƙafarta. Kaka ta kalli ƙafar da ta kumbura tace,"subhanallah garin ya?". da ƙyar ta buɗi baki tace,"nazo saukowa a bene na gurɗe". Kaka ta kawo hannu zata taɓa tayi ƙara tana janye ƙafa tana cewa,"Kaka akwai zafi fa...yanzu ma daga asibiti muke sun ƙara karyani shine kika ga ta kumbura haka, saura kaɗan na mutu Kaka". Kaka nayi mata wani kallo tace,"kice gata suka yi miki...to sannu sai ki daina kukan, ke idan ba'ai miki hakan ba kina zaton zuwa safiya za ki iya motsar kafar ne ma, Allahk dai ya sakawa Hajiya da alkhairi". sai sannan Kaka ta kai idonta kan ledar maganin da ta yasar can gefe, tace da ita,"ledar kuma ta mene?". tana shaƙar majina tace,"wai magani ne". Kaka tace,"wai kuma haka za ki ta shansa ba har sanda Allah zai kawo miki sauƙi". Fillo taiwa Kaka da maganin wani kallo ta wutsiyar ido, Kaka na ganin hakan ta miƙe ta ɗauka ledar tana faɗin,"jefar da magani a bola ai ba wahala yake miki ba, gwara na ɗauke nayi masa guri tun ba kisa anyi asarar kuɗi ba...dan na san kuɗi ne bana wasa ba aka kashe". Kaka ta shige cikin ɗaki da ledar maganin dan yi musu wajen ɓuya. kuma tana shiga aka saki wata uwar tsawa a tsakiyar kan Fillo, ta buɗa baki zata yi adu'a da ihu sai taji ta kasa, ta ya zata kwatanta?, wani irin ciwo take ji acikin kanta da ba zai kwatantu ba, ita ɗaya tasan azabar da take ji, ga gefen cikinta ma da takeji kamar ana caccaka mata allurai. kira kawai take ji acikin kanta, kira daga muryar da bata san ta ko waye ba, kuma muryar da bata taɓa ji ba. _"zo da nisa, maza zo da sauri"_. wannan kalmar ita ake ta faɗa mata, ta kai hannu ƙugunta ta damƙe wannan dunƙulallan asirin da ta ɗauko,
🏠