NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 5 of 323

a kiran sunan, sunan da kusan kowa ke kiran Halima da shi acikin gidan idan ka ɗauke Kaka wadda ba ko da yaushe ta cika faɗa mata hakan ba, tafi kiranta da Halimatu. jin kiran yasata dakatawa daga tafiyar da take tana yatsina fuska har lokacin da Maijidda ta ƙaraso wajenta. "na rasa me ya shiga kunnenki ya toshe miki ji akan cewar bana son irin wannan kiran sunan na mafarauta". Halimatu ta faɗa tana ɗan hararta. "ke kuma gaki kullum acikin ƙorafi". "nayi ɗin". Halimatu ta faɗa tana sake ɓata rai. Maijidda ta taɓe baki tana cewa,"ke dai kika sani. daga ina kike? mene wannan?". ta jera mata tambayoyin tana ƙoƙarin amsar ledar hannunta. "daga inda kika aikeni Kaka". Maijidda tai gajeriyar dariya bata ce komai ba. wanda tuni har ta buɗe ledar ta ɗauko mangwaron ta fara gatsa. hakan kuma yasa Fillo jan tsaki tai gaba abinta, dan idan da abinda ta tsana a halin Maijidda shine cin abu ba tare data wanke ba, ita dai data ga abunda bakinta yake so ba ruwanta da tunanin wankewa zata afashi cikin baki. sun shigo tsakar gidansu suka ci karo da Masu aiki nata zubewa ƙasa suna aika gaisuwa da kirari. Halimatu ta ɓata rai sosai ta kama hannun Maijidda ta dakatar da ita daga tafiyar da suke. "lafiya?". Maijidda ta tambayeta. "mu juya dan Allah". "saboda me?". "ni wannan gaisuwar sarautar har ga Allah ba ƙaunarta nake ba. ko waye ma haka a ɓangarenmu oho". ta ƙarasa faɗa da jan tsakin ƙorafi tana ƙoƙarin juyawa. Maijidda ta fizge hannu tana cewa,"ai idan kinga na koma to tabbatarwa nayi ba wanda nake zato bane ya shigo wajen nan. haka kawai kiyi mana buƙulun ƴan silallan da zai bayar". "banza mayyar kuɗi, wallah idan ba kiyi wasa ba da wannan shegen son kuɗin naki za'a cuceki". Fillo ta faɗa tana barin mata wajen ta fice da sauri gudunma kar Kaka ta hango inuwarta ta ƙwala mata kira. tana fita ta nufi famfo ta wanke mangoro, ta dawo ta zauna kan wani ɗan tudu tana sha. kusan tsawon minti biyar tana zaune a wurin, kuma zaman na dole, duk gudun kartai gaisuwar da bata da niyya. a wajen Maijidda ta dawo ta sameta, ta zauna itama tana cewa,"kin gani, dubu biyu ce ya bawa kowa. kema ga naki na karɓo miki". kallo ɗaya taiwa kuɗin ta ɗauke kai, kuma tana juyawa gefe idonta ya sauka akansa, yana tafiya cikin takun isa, taƙama da cikar izza. duk tsayin zamanta a gidan bata taɓa ganin me kalar halittarsa ba, hakan yasa ƙananun laɓɓanta taɓewa kan ta dawo da kallonta ga Maijidda tace da ita. "waye wancan ɗin. tunda naga ke babu wanda baki sa ni ba acikin gidan nan saboda shegen shishshigi…cikin masarauta ma idan aka je yanda kike faɗar sunan jama'a kamar kece uwarsu". "kanki ake ji. yanzu amsar tambayarki zan baki ko na jira ki gama neman maganar?". Maijiddan ke maganar tana ta shan mangwaronta. "ki riƙe amsarki karki faɗa ai ba damuna yayi ba. dama naga ne ban taɓa ganin irin halittar bane acikin gidan nan tsawon zamana". "to sunansa Turaki". jin sunan da Maijidda ta ambata ya ƙwala ƙarar sautin wani abu acikin kanta, babu shiri ta miƙe a zabure tana gyara ɗaurin zanenta. "me kika ce?". "baki ji me nace bane hala? to nace Turaki ko". lokaci ɗaya idon Halimatu ya manne a bayan Turaki dake tafiya yana kusan kaiwa ga barin harabar ɓangaren masu aikin gaba ɗaya. a hankali kuma idonta ya rufe, cikin duhun idanunta na haska mata sunan Muhammad Turaki dake jikin farar takardar nan da babu zanen komai ajikinta sai na sunansa. "tashi muje Maijidda". "zuwa ina?". "ina wannan baƙar ledar dana baki ranar bikin gimbiya Safiyya?". "tana ɗakin Yami". "je ki ɗaukota da sauri. ki sameni a bayan tanki cikin lambu, ki taho da ashana dan Allah". _till we meet in the next page! Your Comment will make me to continue or stop._ dont forget to vote and share to other groups please🙏 *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *2* "Maijidda na kasa gane wajen". Fillo ta faɗa a sanda ta ke ƙarewa babban filin wurin kallo. Dukkan tunaninta da hasashenta ta ɗora shi a wurin na fiye da daƙiƙa biyar amma sam ta kasa ta fahimci inda akai haƙan ramin. Maijidda dake tsaye itama ta ƙarasa bakin kujerun wajen(resting chairs) ta zauna. Ta ajiye digar dake hannunta sannan itama tabi wajen da kallo cike da nazari da kuma son tunanowa. "wallah Fillo nima na kasa tunawa kin san an kwan biyu...amma wai ajiyar me kikai ne a wurin nan?". Fillo bata ce da ita komai ba, sai baki da ta zumɓura mata ta harareta kaɗan. ta zauna bakin tudun dake wajen tare da naɗe ƙafafunta, kamar wadda ta shiga ajin makarantar allo. Yatsanta manuniya akan leɓanta na ƙasa tana ƙarewa faɗin wajen kallo, da kuma tsirran ciyayin da suka firfito a ƙasar wajen. Cikin zuciyarta tana ayyana ya za'ai ta manta wajen nan, bayan tasan tsawon watanni biyar da aka ɗauko bata ko zo wurin ba, hoton gun na haska mata acikin idonta a duk sanda ta tuno, abu ne da bai shafeta ba amma ta kasa mantawa da shi acikin ranta. Ita dai tasan ta kuɗuri aniyar tarwatsa a
🏠