NOVEL SHARES -
ddara da hakan ai bata faru ba, shi yasa ko ƴar izzar nan ma ta masu sarauta banda ita, sha'anina kawai nake ba zan iya takura kaina ba wallahi, ina dalili. me gidan nan aini ya biyo, idan kika gansa ba kyace Yarima ba, shi dai Habib ɗin dama da kin gansa kinga wanda sarauta ke yawo a jininsa, aishi wannan Yaron na gidan nan yayo, umm Turaki ba wallahi kam...sauran yaran Ibrahimu da Samir za ki gansu kamar ƴaƴan tsintuwa".
Fillo dai murmushi take tayi, taji sosai tsohuwar ta burgeta. "ba kya magana ne?". Fillo ta girgiza kai tace,"a'a ina yi Hajiya". Boɗejo tace,"auyo ni fa nace ai da an banu...ba ki da magana dai ina ce ko?, dama ai ba kiyi kama da sauran ƴan aikin ba iyayen zuba kamar tsohuwar kanya, wallah na faɗa miki su nan suke zubewa su sakani gaba inta basu labarin masarauta wai suna so, ita surukar tawa tayi ta jin haushina, itama wannan ƴar Samha taita ɓata rai wai ita ba haka ƴan sarauta suke ba, to ni dai basu isheni kallo ba ma dan bana bi ta kansu, ina dalili ka takura kanka akan wata banzar aba sarauta".
Fillo tayi murmushi me sauti still dai bata ce komai ba, haka kawai taji tana so ta ɗauki lokaci tare da tsohuwar suna hira. sai yanzu Boɗejo ta bata glass ɗin dake cikin box ɗinsa tace,"idan kinje sai kin kunna fitilar ɗakin dan ba lallai bane an kunna min, tunda me ta'adin Sameer baya nan can muka baro shi gidan Hakimi...akan mudubi kawai zaki ɗora min shi kinji ki riƙe da kyau kar ya fashe, na huɗu kenan da Habib yasa akayo min shi daga dubai, da yake acan ake duba min lafiyar idon".
Fillo tace,"to Hajiya". Boɗejo tana kallonta sosai tace,"a'a wallahi sunana Rumana ko kuma kice min Boɗejo kamar yanda jikokina ke kirana. ina wani batun Hajiya anan salon dai a ƙarawa mutum jin kai, ai da Hajjah suke ce min, Mai Martaba na rasuwa na rufe ido nace ko Rumana ko wani sunan, to shine fa baturen yaron nan ɗan gidan sarki Habib ya saka min Boɗejo, da ike shi ne jikana na farko, kai izza acikin yaron nan kamar ba zai taka ƙasa ba".
tana faɗar baturen yaro Fillo ta gane Yarima Abbas take nufi. "kema ɗakin kwanan masu aikin kike?". ta girgiza kanta,"a'a wurin Kakata nake". "can da nisa ne kenan?". "a'a Boɗejo nan ɓangaren ma'aikata, nan muke da zama".
Boɗejo tace,"auyo ce min zaki tsaffin bayina ne ku, to ai shikenan dama ce nake nan kike kwana nace to kizo ɗakina mu kwan tare dan sosai na yaba da hankalinki wallahi".
Samha ta faɗo ɗakin rai ɓace, tana jifan Fillo da wani irin kallo tace,"ke dan Uwarki ina aikin da na saka ki?". maimakon bata amsa sai kallo da Fillo ta bita da shi, cikin ranta tana maimaita dan uwarki, kalmar da ta jima bata ji an faɗa mata ba.
"ba magana nake miki ba?".
Fillo ta rufe ido tana jin zuciyarta na suya sannan ta buɗe tace,"Adda Samha ai nayi". "kika yi a gidan uban wa?. bance miki acikin trolly za ki jerasu ba, gobe da asuba zan bar ƙasar". sai taja tsaki tace,"ni ba'a taɓa bagidajiyar ƴar aiki ba sai akanki wallahi, to minti uku na baki kije ki kammala shiryan kaya tun ban nuna miki other side of me ba".
a sanyaye Fillo tace,"kiyi haƙuri don Allah, zan gyara yanzu". ta faɗa tana barin parlon, guntun hawayen dake maƙale a idonta ya sauko, a rayuwar nan ko mene zaka yi mata kayi amma karka sako mahaifiyarta aciki, bata so, bata so ko kaɗan.
kuma ɗazun sha'afa tayi gaba ɗaya, ta gama gugar sai ta zuba cikin wadrobe tana ta sauri saboda ƙafarta da ke mata zafi, amma tana ta alla alla kafin su dawo taje ta gyara.
Boɗejo ta kalli Samha tace,"ki dai dinga bin duniya a hankali, ni wallahi duk kece me ɗaukan duniya da zafi su dai su Zaytuna basu ɗorawa kansu wannan masifar ba...yo Samha kuɗin ubanki ɗin me?, shi ya bawa kansa?, to in gaya miki nan da kika ganni kafin Babana ya zama wazirin Sarki kika ganmu sai kin tsartar da yawu, to amma yau fa?, matar wa na zama kuma yanzu uwar su wa na zama?, kuma wane irin matsayi na taka?...to wallah kaɗan daga cikin ikon Allah kiga ƴan aikin nan da kike narkawa uwar tsawa kullu yaumin sun lula sama ke kuma kina nan ƙasa".
"wallahi ba amin ba, wannan ai mugun baki ne Boɗejo". Samhan ta faɗa tana wucewa ta haye sama.
a bakin side ɗin su Turaki, Fillo tazo wucewa zuwa part ɗin Boɗejo, Khalil dake balcony a tsaye yana waya idonsa ya sauka akanta, ya lura da yanda take ta ɗingisa ƙafa tana tafiya da ƙyar.
ya sauke wayar daga kunnensa ya kalli adadin minutes ɗin, sannan yace,"please hold on 2minutes". daga haka ya aje wayar nan kan table ya fito.
"Fillo". kiran sunan nata ya dakatar da ita daga tafiyar, muryar Kalil taji, amma ko da ta juyo maimakon ta gansa sai taga Turaki na tunkaro inda ta ke.
*Please comment, Share and Vote pls.*
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
_nace muku i love you ko na bar kayata?...kai aradu sai na faɗa ko me xaku yi sai dai kuyi😏, idan na faɗa sai na ruga da gudu yanda ba zaku iya kamani ba😝...nace ba *I LOVE YOU MY FANS* 🏃♀._
*15*
tunda taga Turaki ne ke tunkarota tayi ƙasa da kant