NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 47 of 323

sannan kuma in wanke banɗaki 6, shikenan". "shikenan!, wannan yawan aikin shi zaki kira da shikenan Halimatu?". ya maimaita kalmar da mamaki. ta ɗaga gira,"eh, ai babu wahala tunda ba ɗauda suke yi ba, nan da nan nake kammalawa na tafi ɗaki na huta...saboda haka ka bar damuwa watarana sai labari". yace,"balle ma kin kusa ki daina, very soon insha'Allahu...nayi mafarki na zama ɗangote". ta waro ido tana kallonsa, ya ɗaga kai yace,"da gaske, wai na koma Ɗangoten Gombe, na aureki mun bar ƙasar gaba ɗaya, muka ajiye Inna da Kaka a saudia mu kuma muka wuce London Honeymoon". tayi far da ido ta maimaita kalmar, "Honeymoon, kamar na taɓa jin wannan kalmar amma na manta aina". "zaki ma santa ne lokacin da mukayi aure, Allah Halimatu na aureki da Uwar kuɗina a yawon shaƙatawa kawai zamu ƙare rayuwarmu, wani banzan aikin gida duk ba za kike yi ba". tasa hannu cike da kunya ta rufe fuska,"ni fa yarinya ce nace ka daina faɗa min kalmar aure". yay mata harar wasa yace,"kin manta ɗazu kika zo duniyar...ai na tabbata a karatun aure babu wanda ba ki sani ba sai dai ki raina min wayo, sai kace ba aminiyar Maijidda ba". ta danne dariya tace,"me kake nufi da Maijiddan?". yace,"oho". haka sukai ta hira ba tare da sun san lokaci ya tafi ba, Fillo sam ta manta ma a inda suke, sai da mai gadi ya ankarar dasu. cike da kunyar mai gadin ta bar wajen dan idan ta biye ta Amir ba zasu tafi haka ba, yana faɗa mata wai yau subscription zai yi. bin ta yayi a baya yana ta murmushi, tsaye ya sameta a gate ɗin da zai shigar da kai ɓangaren ma'aikatan gidan, tana ta jan yatsun hannunta kamar yanda hakan yake sabonta ne. ya jingina da ƙofa yana kallonta yace,"wai kuɗi kike lissafawa a jan yatsun nan ko me?". idonta na ƙasa ta jinjina kai,"ehh kuɗin ɗangoten Gombe nake ƙirgawa". yay murmushi yace,"Allah ya amsa". itama tace,"amin". sannan ta kalli yanayin garin da magriba ta ƙarato tace,"muyi Sallama su Hajiya na kan hanya, kuma akwai sauran aiki gabana". yace,"aikin me?". tace,"Adda Samha ta bar min guga kuma tana da yawa, gata bata da sauƙi mafaɗaciya ce". "barkono ce ita?". tace,"kafi barkono in kaji ana faɗa". ya kalli agogonsa yaga har ƙarfe shida da minti goma, ya sauke numfashi sannan yace,"to sai yaushe?". daga yanda yay maganar sai yay mugun bata tausayi, itama ba dan tana so zasu yi sallamar ba, lokacin da bata fara aikin ba ai babu ruwanta da wani kallon lokaci, ko zasu kwana suna shan soyayyarsu babu mai katse su. "kawai zance banda lafiya kaga zan huta ranar". ya ɗan zaro ido waje yace,"a'a bana so kiyi ƙaryar ciwo, kawai dai zan ƙara dawowa". ya faɗa yana jan ɗan cif-cif ɗin gemunsa. "a'a ni kam ban yarda kazo ka ban kunya ba". ta faɗa tana kama gefen hijabinta. yace,"ohh kina jin kunyar kar suga saurayinki ba ɗan gayu ba kuma talaka ko?, alhalin ke me kyau ce". tayi saurin girgiza masa kai yanayin fuskarta na sauyawa,"ko kaɗan ba haka bane, dan Allah karka ƙara wannan tunanin Amir, ba zanji kunyar nunaka a koma ina ne ba wallahi, kai nake so ba gayunka ko kuɗinka ba, kuma so nake maka na tsakani da Allah". tayi naganar kamar zata yi kuka. "bance ki zubar min da hawayenki ba, kin san suna da tsada...na faɗa ne dan na zolaya, kiyi haƙuri". tai knodding kanta kawai, kamar ba zasu yi sallamar ba, sai da tayi da gaske tukunna sukai sallamar ta juya ta tafi, kuma tana cikin tafiyar ne ya dakatar da ita da tambayar me ya sami ƙafarta, dan a ɗazu bai lura ba sai yanzu. tace masa babu komai tsayuwar da sukai ne yasa ƙafar yin tsami, ba don ya yarda ba sai dan karya takura mata ya ƙyaleta. sai bayan isha'i mutanen gidan suka dawo, bata ma san sun dawo ba saboda lokacin tana ɗakin ƴan aiki zaune cike da kewar Kakarta, yanza basa yini tare ko kaɗan, da dare yayi sai safiya ta taho aiki. tayi zurfi cikin tunani taji wayar ɗakin na ƙara, tana ɗagawa taji muryar Zaytuna na cewa da ita,"kina ina ne?". tace,"laa Adda kun dawo, banji ƙarar mota ba". Zaytuna tace,"to kizo". ta ajiye wayar ta miƙe tana jan ƙafar dan sam bata so a gane ciwon dake ƙafarta. Boɗejo kawai ta samu a parlon, ta ƙarasa ta tsuguna ta gaisheta. sannan ta tashi zata hau upstairs, Boɗejo ta tsayar da ita. "kinga ke ƴar nan zo kai min idon baturen nan nawa ɗakin kwana na". Fillo ta rissina ta karɓa, Boɗejo ta kalleta tace,"ke kuma zuwan yaushe?". tace,"ban jima ba". "Allah sarki, to sannu Allah yayi miki albarka". Fillo tace,"amin". Boɗejo tace,"to ɗakin nawa kin sa ni ne?". Fillo ta girgiza kai alamar a'a. Boɗejo ta ɗora ƙafarta kan tumtum ɗin dake ƙasan carpet tace,"can ɓangaren ƙarshe nake kusa da su Turaki, nan suka wullani wallahi daga ni sai halina, kamar ba saurauniya ba ada". ta jefa wata choculate a baki ta ƙara cewa,"ai da mijina shine sarkin garin nan, to daya rasu ne kuma ɗana Habibu ya hau kan kujerar...kin ganni kamar ban haɗa jini da sarauta ba ko?, wallah bata dameni ba in faɗa miki ƴar nan, banda ma dai Allah ya ƙa
🏠