NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 46 of 323

nanin mamaki ta ke kallonsa from head to toe, baki buɗe ta kasa rufewa, what would she call the situation she got into ?, tasan dai gefe ɗaya farin ciki ne ya lulluɓeta, to amma ɗaya yanayin fa?. idan tace ba ta kewarsa tayi ƙarya, idan tace bata yi murnar ganinsa ba tayi ƙarya, idan tace bata son ganinsa ta yaudari kanta. cikin wani irin emotions da ta ke jin kanta tayi saurin saka tafukan hannunta ta rufe fuskarta, murmushi kawai take yi, irin murmushkin nan me faɗi dake fallasa kyawun fuska, wani daɗi ne kawai ke ziyartarta, ji take yi tamkar an mata albishir da kujerar makka. tana son ganinsa, tana ta so ta kasance da shi amma babu dama, lokaci yayi mata ƙaranci tunda ta fara wannan aikin, rabon da ta saka shi a ido tafi sati uku, har Kaka ta gama ciwonta ta gama basu haɗu ba duk da cewar kullum sai yazo dubiya, sai dai idan ta koma Kaka ta bata sallahun saƙon gaisuwarsa daya bar mata. Allah ya sa ni sai yanzu da ta gansa take jin tamkar ta ɗauki shekaru bata gansa ba, kuma Allah ya sa ni a yanzu ji take yi kamar ta rungume shi don tsananin farin ciki, ta ya ya?, ta ya ya zata nuna masa irin jin daɗin da ta yi na ganinsa?. ta ramin yatsunta take hango fuskarsa da gaba ɗaya babu walwala, lokaci guda tasha jinin jikinta, wanne irin bayani zata yi masa ya fahimta?, ko me zata ce ba lallai ya gane ba, abu ɗaya kawai tasan yana ransa shine yanzu ta fifita aiki akansa. sai kawai jikinta yay sanyi, still hannunta na rufe da fuskarta tayi ƙasa da kanta tana jin kamar tayi kuka. bata yi aune ba taji faruwar al'amarin da bai taɓa faruwa ba a tsakaninsu ita da shi, hannunta ya ruƙo, wannan hannun nata da bai taɓa riƙewa ba tsawon lokacin da suka ɗauka tare, me zata yi yanzu?, zata sakar masa hannun ne ya sauke kamar yanda taga yana ƙoƙarin yi ko kuwa zata hana hakan?, domin gani ta ke kamar ba zata iya haɗa ido da shi ba, kunyarsa ta ke ji sosai, kunyar riƙe ma ta hannu da yayi, tana ganin tamkar sun aikata wani babban alfasha ne. idanuwanta suka ciko da ruwa, ta shiga ƙiftasu a hankali, dai-dai lokacin kuma da ya sauke hannun nata daga kan fuskarta, kallonta yake har yanzu, ya kasa ko da ƙiftawa, ji yake kamar ya ɗauketa, ji yake kamar ya sureta ya kaita duniyar da babu kowa aciki daga shi sai ita. a ƙoƙarinta na zame hannunta daga nasa ta ɗago ido tana kallonsa, kamar ruwa ta ke gani anasa idon shima?, kamar yana so yay kuka ne?, kamar rauni ne take gani a ƙwayar idon nasa?, kenan shima yayi kewarta har irin haka?. shi kuwa kallon da take yi masa gani yake kamar tana masa kallon tuhuma ne, me yasa yazo nan?, me yasa ya biyota?, me yasa bai tambayi izininta ba?, ai tun kamin yazo ɗin sai daya shiryawa amsa waɗannan tambayoyin, ya kuma san zata yi masa rangwame ko da zata hukuntasa. ya rumtse idanuwansa tare da ƙara riƙe hannunta sosai yana murzawa sannan yace,"kiyi haƙuri, na kasa ci gaba da jurewa shi yasa na biyo ki". cikin sanyayyar murya tace,"hannuna". sai taji yace,"ba kuma zan iya sa ki ba Halimatu, wallahi ba zan iya ba. dan Allah ki barni". ba tare da ta ɗago kanta daga sunkuyen ba ta raba hannayen nasu, sannan tace,"me yasa to baka tambayeni ba kafin...". bata ƙarasa ba ya katseta,"naga zan mutu shi yasa, kuma bana so na mutu ban mallakeki ba, ba kuma na so na mutu ba muyi sallama ba...ina ta son ganinki, ina ta so nayi magana dake, amma wannan aikin yabi ya toshe kowacce ƙofa, ita kuma zuciyata sai zafi take tana kukan rashinki, shisa yau nace babu abinda zai min shamaki da ganinki ko da ace fadar sarkin gombe kike aiki yau sai na shigeta na ganki, daga nan kuma nima sai na nemi taimakon a ɗaukeni aikin muke yi tare ina rage miki, ta yanda zanke samun ganinki ko da yaushe...nazo da complete takarduna, please kiyi min iso ko Allah zai sa a dace". ta kalleshi tana murmushi, da gaske yake babu wasa a maganarsa neman aikin yazo. ta kalli takardun ta ƙara kallonsa tukunna tace,"ni babu takardun komai aka ɗauke ni". yace,"arziƙin Kaka kika ci shine dalili". ta juya idanu sannan tace,"ko da babu Kaka ni banga ana ɗaukan me wanke-wanke da shara da takardu ba". yace,"kuma dama na iya wanke-wanke sosai ba". ta saki dariya sosai tana ɗora bayan yatsunta akan bakinta. yana kallonta har yanzu fuskarsa bata gama saki ba yace,"dariya na baki?, Allah da gaske na iya wanke-wanke, kuma ki tambayi Inna kiji, idan na wanke kwano har ƙyalli yake ya dawo kamar sabo, kuma na tabbata na fiki iyawa...saboda haka nasan idan suka ɗaukeni a kwana ɗaya zasu bani ɗaki a gidan nan, wataƙila ma ke su kore ki, kuma dama haka nake so dan wallahi bana ƙaunar wannan aikin". tayi wani murmushin tace,"kaga ni kuma ina sonsa, tunda da kuɗin muke rufawa kanmu asiri...yanzu haka ma Kaka ta kusa siya min ƙaramin fili da kuɗin da ake ajiyewa". ya ɗan kauda kai gefe sannan ya dawo yana ƙara fuskantarta. "sau nawa kike aikin ruwa?". ta juya idanu sannan tace,"ummm ya danganta, ina wanke kwanuka kuma zanyi girki idan Adda Zaytuna bata yi ba,
🏠