NOVEL SHARES -
zaka so ka daina shaƙarsa ba, irin ƙamshin nan dake motsa zuciya ta faɗa cikin wani yanayi mai wuyar fassaruwa.
hasalima da ta ɗauko sai ƙamshinsa ya gauraye duka ɗakin, ya kore ƙamshin air freshner da turaren wutan da ta yiwa ɗakin.
tunaninta guda ɗaya ne a lokacin asirin na menene?, to dama asiri yana ƙamshi?, ai tayi zaton asiri wari yake yi?, anya wani bai ganta ba a lokacin da ta laɓe yasa suka faɗi wannan maganar domin a ɗana mata tarkon ɓera?.
ta tsorata da wannan tunanin, amma ko menene dai ba zata taɓa barin wannan dunƙulallan abin ya ƙara zama a ɗakin ba balle har Turaki ya kwana tare da shi.
saboda haka cikin hanzari ta yunƙura ta miƙe zata fice, kwatsam idanuwanta suka sauka akan takardun da suka faɗo ɗazu da zata shiga ƙarƙashin gadon tace sai ta fito ta mayar da su.
ta kama gefen zanenta ta ƙulle wannan abin da har yanzu zuciyarta taƙi yarda da cewar asiri ne, babu ko ɗigon tsoron zai iya cutar da ita, ta durƙusa ta kwashe takardun ta buɗe drower ta zuba su, sai dai cikin rashin sa'a wata takarda me duhu ta faɗo.
daga tsayen da take kawai ta tsaya tana kallon takardar, baƙa ce, duk da duhunta hakan bai hana hoton abinda ke jikin takardar bayyana ba.
dai-dai take gani ko kuwa gizo ne idanuwanta ke yi mata?, kalmar Tashin hankali dai tayi kaɗan wajen kwatance da halin da ta shiga a lokaci ɗaya.
ƙafafuwanta suka tafi a hankali gwiwoyinta na zubewa a ƙasa gaban takardar, waɗannan siraran yatsun nata na rawa ta ɗauko takardar, sai bayan ta ɗauko ne taga ashe harda wata ƙaramar takarda anyi stapling ɗinta ajiki.
ƙwayar idonta ta manne akan ƙaramar takardar dake ɗauke da sunan asibitin *As-Salam International Hospital*, Assalam ɗin kawai zuciyarta ta iya karanta mata banda international Hospital ɗin.
*Nile Corniche, Athar an Nabi, Old Cairo, Cairo Governorate 4220501, Egypt.* kamar haka address ya biyo bayan sunan asibitin, bin kowanne rubutu ta ke da ido ba don zata iya karantawa ba, har tazo inda ta ke da ilimin karantawar, karatun da ta samu daga wajen Amir, *NAME* zuciyarta ta faɗa, sannan ta ƙara faɗar sunan daya ke rubuce akan siririn dogon layin da aka zana dan rubuta sunan majinyaci, *MUHAMMAD TURAKI HABIB*.
ƙasan sunan kuma wani dogon layin ne da aka rubuta *KIDNEY FAILURE*. A duk cikin tarin rubutukan da takardar ke ƙunshe da su, suna uku zuciyarta ta iya karantawa, As-Salam, Name da kuma Muhammad Turaki Habib.
kuma ta ke zuciyartata tayi wani girgiza da karanta sunan nasa, ba kamar ranar farko ba da bata ji komai ba sanda ta karanta sunan nasa.
sai kuma ta maida idonta ga haƙiƙanin hoton dake jikin baƙar takardar, ta taɓa riƙe irin takardar nan, wasu shekaru baya da suka wuce, kamar haka ne ba zata manta ba, likita ya basu takardar dake ɗauke da hoton ƙodar da akayi.
_"tana ɗauke da ciwon ƙoda"._ ba zata manta ba haka likita yayi musu bayani a wancan lokacin.
allon ƙirjinta ya girgiza lokaci ɗaya, me hakan ke nufi kenan?, shima wanda sunansa ke rubuce ajikin wannan takardar yana ɗauke da irin ciwon daya kashe mata Adda?.
bata san lokacin da ta shiga girgiza kai da sauri ba, ai bata manta ba ta faɗa a baya, anyi an gama, ba zata ƙara rasa wani mutum da ya samu gurbin motsi a zuciyarta ba, kuma wannan alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta.
kuma shikenan sai ta shiga rera kuka, zaman durƙushen da bata tashi daga shi ba kenan har zuwa yanzu, tunda ta tuna irin baƙar wuyar da Addanta tasha kafin ta mutu, bayan sun gama sa rai da cewar ta sami lafiya, a wankin ƙoda na arba'in da huɗu(44) da akayi mata, ashe tsawon lokacin da ta ɗauka tana fama ciwon ajali ne.
Hawayen dake bin idanunta ya gangaro ya sauka akan takardar dake riƙe a hannunta, wadda ta tsirawa ido babu ko ƙifce. _"Mutuwa zai yi shima"._ wani ɓangare na zuciyarta ya faɗa mata hakan.
a lokacin idan ka ga Fillo zaka iya rantsewa hankalinta ya gushe gaba ɗaya daga jikinta, dalilin ambatar kalmar mutuwa da zuciyarta tayi mata, allon ƙirjinta ya ƙara yin wani duka a karo na babu adadi, wata tsawa ta ziyarci cikin kanta, tsawar da ta haɗe da kiran daya shigo ta cikin wayar ɗakin wadda ke manne ajikin bango.
_Idan Ayyukan da suke gabana na ɗaya daga cikin abinda ke hana ni yin typing, to tabbas rashin comment ɗinku shine maƙusin abinda ke saka na ɗauki tsawon lokaci banyi ba...ko dana zo yin typing ɗin ma sai naji banda wannan ƙwarin gwiwar, tunda ko da nayi babu masu tarbarsa hannu biyu, saboda haka ku daina ganin laifina, har da naku laifin...amma idan har kun gyara la shakka nima zan gyara...sai dai ban sa ni ba ko kunfi so aci gaba da tafiya a littafin kuɗin?._
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*14*
Fillo tasa hannu ta goge hawayen dake fuskarta, ta ɗaga kai tana bin wayar dake ringing da ido, tunani takeyi akan taje ta ɗaga ko karta ɗaga, ɗaya ɓari na zuciyarta ya rinjayeta akan taje ta ɗaga ɗin.
saboda haka ta yunƙura ta miƙe tsaye jikinta a mace, bata ma ko iya ɗaga ƙafa sai jant