NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 43 of 323

kija layi kice kar na shata na haƙura dan dole na, bin zaɓinki dole na, yacca kike so nayi haka zanyi muddin hakan zai faranta ranki...". bai ƙarasa ba amon muryarta ya fito da faɗin,"aurenka nake son gani Me babban suna, ina so kayi aure tun ina da rai Hammansu, ka sani ina sonka fiye da numfashina, babban burina a yanzu shine naga aurenka, naga matar da zaka aura, naga jikana, naga kalar rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankalin da zaka shimfiɗa da iyalinka...Hammansu wannan auren da baka so shine mutumcin mutum, kuma shine ƙarshen jin daɗin rayuwa...ita rayuwa nan guda ɗaya ce Hammansu, haka ran ɗan adam guda ɗaya ne. lokaci tafiya yake baya jira, so kai enjoying rayuwarka tun lokacin bai ƙure ba, ya zamana kazo baka mori dukkan jin daɗin rayuwar ba...babu wanda aka yiwa alƙawarin kaiwa gobe a wannan duniyar, tsari kawai muke da hange, kuma zata iya yiwuwa mu matu a lokacin da muke ta shirin tsare-tsaren gobenmu, and that will be the end of us, ni kuma ina so mu tafi ne a lokacin da muka bar masu tunamu a kowacce daƙiƙa. da zarar ance babu kai shikenan duk wasu memories daka bari suma sun tafi, amma ɗa fa?, shi ɗaya ne memory da zaka tafi ka bari a kasa mancewa da kai, hakan yasa nake so kayi aure tunda sauran lokaci, auren nan daga zuriya mai ƙarfi irin zuriyarmu, *SARAUTA*, ta yadda zaka bar bayanka, wannan kawai shine burina akanka Hammansu". idanuwan Turaki a ƙasan carpet suke, amma ƙwayar idonsa wasu yatsu ta ke hangowa sirara da suke karkarwa kamar waɗanda ake girgiza su. ya haɗiye wannan yawun dake saman harshensa zuwa cikinsa, sannan ya rufe idonsa ya buɗe a lokaci ɗaya. laɓensa na sama dana ƙasa suka tale, harufan bakinsa suka fito da faɗin. "Aure! zanyi aure Maama, zanyi yanda kike so, kuma insha'Allahu sai na cika miki dukkan burinki akaina, kuma insha'Allahu ba za'a wayi wata rana da za'ace kin rigani tafiya ba, ni nake so na rigaki tafiya Maama, ni nake so, bana so ki tafi ki barni, rayuwar zata yi min tsanani, zan daina jin daɗinta kwata-kwata, zan dinga jinta ne kamar ana min feshi da ruwan dalma, dan Allah Maamaaaa". maganar yake da kakkaryewar kowanne harafi, kuma maganar tasa ta katse gaba ɗaya a sanda yaja sunanta wajen faɗi. lokaci ɗaya ya nemi ya fita hayyacinsa. sautin kuka kawai yake ji acikin kansa, wannan sautin kukan na yarinta dana jarirai, saboda haka yay saurin saka duka hannayensa ya toshe kunnuwansa, tare da kifa goshinsa akan ƙafafun Hajiya Madina dake zaune tana hawaye. har zuwa lokacin da ya daina jin ihun kukan acikin kunnensa sannan ya ɗauke hannunsa, ya shiga sauke numfarfashi, gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, kamar ma ya burkice ne, hannayensa masu rawa a yanzu suka damƙe zanin Hajiya Madina. a jikinta ta ke jin irin rawar da jikinsa yake yi, jikinsa na rawa amma ita a wannan lokacin tata zuciyar ce ta ke rawa, so take itama ta taya shi kukan, irin kukan da yake yi, so take ta taya shi ko yaya ne, ko da sau ɗaya ne. Zaytuna dake kusa da Boɗejo ta taso cikin kyarmar jiki, ta dawo gabansa ta durƙusa, sannan ta shige jikinsa gaba ɗaya itama nata kukan na ƙara ƙarfi, Turaki yay mata wata runguma da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma na riƙe ne da zanin Hajiya Madina da yake jin kamar a lokacin ƙwace musu ita za'ayi. wani tausayi ya ratsa zuciyoyin duk wanda yake zaune a parlon banda zuciyar mutum ɗaya dake ƙissima tarin abubuwa acikinta. lissafi take, lissafin yanda komai zai tafi, lissafin yanda komai zai warware, lissafin yanda baya ba zata taɓa gogewa ba, lissafin yanda komai zai tafi akan nata tsarin lissafin. **** Komai na ɗakin abin kallo ne, ko da ace baka san kuɗin kaya ba kallo ɗaya da za kai ma ɗakin da kayan da suke cikinsa zaka san cewa tabbas an narka dukiya wajen siyan kaya da kuma tsara ɗakin. ko da ace za'a ɗauki tsawon shekara 10 zuwa sama ba'ai renovating ɗakin ba, ba za'a gane cewar komai da yake ciki ya jima ba. lokacin da Fillo ta buɗe ɗakin zata gyara shi, tsayawa kawai tayi tana mamakin abinda za'a gyara, ina ƙurar da Hajiya Madina ta ke faɗi?, babu, infact irin ƙamshin dake tashi a ɗakin ko ɗakin da ake gyarawa kullum albarka, saboda haka ne tama rasa ta inda zata fara, gani ta ke sai dai ta ɓata ba dai ta gyara ba, dan komai tsaf tsaf, ɗakin yafi ƙarfin basirar gyaranta. amma a hakan dai ta gyara dole, tunda umarni aka bata, kuma sai bayan da ta gyara ne ta fahimci ashe da gasken yana biɗar gyaran. komai ya ƙara zama fes-fes, adon ɗakin dark blue and silver ne, kalar da ta burgeta kuma tasan ta dace da mamallakin ɗakin. a sanda ta gama gyara komai, sai ta shiga binciken abinda ta daɗe tana roƙon Allah yayi sanadiyar shigowarta ɗakin, wannan asirin da akace an saka shi a ɗakinsa, ba ɗakin da yake kwana ba, wannan ɗakin da zai koma da kwana bada jimawa ba, yes taga asirin, ta ganshi a inda taji sunce sun ajiye, ƙasan gadon, a mulmule yake kamar yanda taji sun faɗa, sam ba wari yake ba, wani irin daddaɗan ƙamshi yake yi, irin ƙamshin nan da ba
🏠