i shima Yarima Adam Allah ya rubuta dole zai riƙi sarauta haka ya zuba uban dukiya aka ba shi sarautar yankin Funakaye, yankin da Babban ɗansa ke mulka a yanzu tun bayan rasuwar Sarki Adam.
sai a wannan lokacin Sarki Lateef ya samu lafiya, aka sarara da bi masa ta ƙarƙashin ƙasa, kwanciyar hankali ta samu a gare shi.
Allah ya azurta Sarki Lateef da yara huɗu, babban ɗansa Abubakar wanda yaci sunan Kakansa Sarki na biyu a wancan zamanin, suke kiransa da Yarima Babba, sai dai a yanzu Ƴaƴa da Jikoki na kiransa da Alhaji Babba, kuma a yanzu shi ne Hakimin Kaltungo.
sai ɗansa na biyu da yaci sunan mahaifinsa Hashim suke kiransa da sarki na uku, kuma Hashim shine wanda ya gaji sarautar mahaifinsa Sarki Lateef tun bayan rasuwarsa.
a lokacinsu ba'ai wannan tashin hankalin ba na nuna son mulki ga kowannensu, hasalima mahaifiyarsu Sarauniya Rumana ita ta bada zaɓin cewar shine zai maye gurbin mahaifinsu, kuma daga wannan maganartata babu wanda yaja balle a tsaya ja'inja aka tsaya akan abinda tace.
sai ɗansu na uku Habib suke masa alkunya da Dikko, wanda yake babban alƙali a cikin ƙasa da wajenta, wanda gwamnatin tarayya ke ji da shi, kuma mahaifiyarsa ke alfahari da shi saboda gaskiyarsa.
Falmata(Faɗima) itace autar Sarauniya Rumana(Boɗejo), wacca aka haifeta bayan rasuwar mahaifinsu daya tafi ya bar Rumana da cikinta. ya kuma bar wasiyyar cewar indai an haifi mace a saka mata sunan mahaifiyarsa Falmata, kuma kar a ɓoye mata suna a dinga kiranta da wannan sunan. hakan kuma akayi sai dai Ƴaƴa na sakayawa suce mata Inna Falmata, mahaifiyarta kuma tace mata Sarauniya.
bayan biyo ɗan shirun da aka samu a falon na Hakimi wato Alhaji Babba, akan faɗan da yake ta yiwa Turaki na batun ƙin amincewarsa akan auren da iyayensa suke so yayi, yaci gaba da cewa.
"to mu ba mutanen banza bane ya kamata kasan da hakan Turaki, babu yacca za'ai ace mu ƙyaleka akan ra'ayinka na cewar kai ba zaka yi aure ba, wannan ma zancen banza da wofi ne...idan ka manta to ka tuna su waye mu, saboda haka wallahi ƙaryarka ka bar mana abin kunya a tarihin sarautarmu...na san idan ta ra'ayin mahaifinka ne sai da ya zuba maka ido, to mu ba zamu zuba maka wannan idon ba kaji ni da kyau".
A wannan lokacin idanuwan Turaki a kulle suke, kansa a duƙe yake, yana zaune ne a gefen ƙafafun macen da duk duniya baida kamarta Hajiya Madina. itace ta kawo ƙararsa ba kowa ba, aure take so yayi ya riga yasan da wannan batun ba tun yau ba, ya sa ni shine burinta akansa. to amma me yasa?, me yasa a matsayinta na wadda ta isa da shi bata gindaya masa umarnin hakan kai tsaye ba sai dai ta kawo ƙararsa gaban wanda cin mutumci shine abin yinsa?.
wani dunƙulallan abu yaji ya tsaya a maƙoshinsa, zuciyarsa ta katse da raya masa abubuwa a sanda Hakimi ya ƙara yin magana.
"Turaki ko dai baka da lafiya ne?, idan kasan akwai wannan matsalar a tare da kai to ka faɗa tun wuri a maganceta, duk da cewar abu ne da kamar wuya namiji kamarka ace yana da matsala makamancin hakan".
Boɗejo dake gefe tace,"ah tou dai nima shi na gani. wannan zance dai na batun ba shi lafiya ma ƙarya ne, ni nafi ga wani algungumin ne ya jefe mana shi, tunda dai kaga maitar ibadar nan da yake ma yanzu fa duk ya daina, kuma wallahi ko waye Allah ya isa bamu yafe ba...yanzu duk wani dogon zance ba shi bane, a tashi tsaye a nema masa magani kawai idan aka biye ta uwar tasa da uban nasa ba zasu yi masa wannan abin arziƙin ba".
Turaki ya buɗe idanuwansa ya zube akanta, magana ta ke tana ƙara kambaba zancen asiri ne akansa. bai san lokacin da bakinsa ya buɗe ya katseta da faɗin,"Boɗejo ke kuma komai ya faru shikenan sai kice aikin asiri asiri".
tayi masa wani kallo ɗaya sannan ta maida kallonta kan Hakimi tace,"me na faɗa maka Yarima Babba tun kamin ayi zaman wannan kotun?, ai sai dai idan ban faɗa ba amma yaron nan sai ya tanka, baka ga kallon da yake min bane kamar ma zai tashi ya rufeni da duka...haka fa ubansa ya koya masa kuma alhalin ni ba irin rainon da nayi muku ba kenan, wallahi duk irin son da yake ma yaransa bai kama ƙafar wanda Ubanku Allah ya jiƙan rai ya nuna muku ba, amma ku dai baku san wani abu wai shi raina na gaba ba, hasalima wallahi baku san babba na magana ku saka baki ba, amma su dai Ƴaƴan Dukko halinsu kenan Babba na magana su nuna bai kai ba...to alhamdulillahi daɗin abin Turaki bani na kawo ƙararka ba Uwarka ce gata nan a kusa da kai, kuma billahillazi da ace lokacin da nake sarauniya ne sai kasan na faɗa ka saka baki".
Turaki yay ɗan guntun tsaki, ya ɗago kai ya kalli Hajiya Madina, suka yi ido huɗu da ita. a kallon da yay mata ya gano expression ɗin dake tare da ita.
sai yayi saurin kai hannu wuyansa ya shafo shi, ɗabi'arsa ce hakan. yawanci Boɗejo kance wani ƙullin yake shafowa.
ya sauke numfashi, muryarsa ta fito a hankali, cikin girmamawa da biyayya yace da Hajiya Madina. "Maama ba sai kin kai ƙarata wani wurin ba. kin isa da ni, kin isa ki bani umarni na bi ko ina so ko bana so, kin isa