urin Mai Martaba da suke jin basu da tamkarsa.
hakan kuma ya haifar da aƙida ta girman kai da gadara a wurin Yarima Adam, har ta kai ga yana nuna ƙasƙanci ga na ƙasansa, hatta ga hadiman dake kewaye da Sarki kuwa.
tun kamin ayi masa ƙanne ya haddace wani furuci dake fitowa daga bakin al'umma na kirarin da suke yi masa da Yarima Sarkin Gobe, kai ɗaya ne Yariman da akai babu irinsa, bayanka sarauta gabanka sarauta.
amma tun daga lokacin da mahaifiyarsa ta ƙara haihuwa sai yaji salon wannan kirarin ya sauya, kuma bai gyaru ba har zuwa lokacin da ta tsaya da haihuwa, kirakiran ya tashi daga kansa shi ɗaya ya koma har ga sauran ƴan'uwansa.
dalilin da yasa zuciyarsa tayi baƙi kenan akan ƴan'uwansa, dan yana ganin silarsu zai iya rasa wasu tarin nasarori daya rubuce su a tafin hannunsa. da tafiya tayi tafiya sai ya zamana sam Yarima Adam baya ko da raɓar inda ƴan'uwansa suke, tsakaninsa da su nisantar juna, basa samun fuska a wurinsa matsayinsa na babbansu.
tun zuciyarsa na raya masa wani abu wai shi ƙiyayya har hakan ta tabbata akan ɗan'uwansa Yarima Lateef, wanda ya ƙwace duk wata fada da yake da ita a wurin mahaifinsu, wannan soyayyar da gata da dukkan komai da ya samu lokacin da yake shi ɗaya daga wurin mahaifinsa gaba ɗaya sai ta koma kan Yarima Lateef, hatta da soyayya da girmamawar da al'umma suke ba shi.
kuma hakan ya samo wuri ne dalilin banbancin halayya, cikin kaf su takwas ɗin da Mai Martaba ya mallaka babu wanda ya ɗauko kyawun halayyarsa da ɗabi'unsa sai Yarima Lateef, shine yasan darajar mutane, saɓanin sauran da suke nuna ƙasƙsanci ga mutane, haka shine kaɗai mai sauƙin kai amma kaf sauran suna da mummunar ɗabi'a ta girman kai, kuma shi ɗaya ne mai son mutane da yi musu fara'a, gaba ɗaya Yarima Lateef kan manta da cewar shi ɗin jinin sarauta ne kasancewar ba'a gabansa take ba, amma ƴan'uwansa sarautar itace abar alfaharinsu da tunƙahonsu, a karan kansu sukan ji tamkar su mutstsuke juna saboda girman izza, kowannensu mulki da muƙami kawai yake wa hari a rayuwarsa amma banda Yarima Lateef.
shakarun Yarima Lateef 24 a duniya mahaifinsa ya aura masa ƴar gidan wazirinsa me suna Rumana, itama kuma sai ta samu matsuguni na soyayya a wurin Mai Martaba ta dalilin ɗansa da take aure, dan tunda akayi auren Mai Martaba da Sarauniya Falmata suke kiranta da gimbiya.
a wannan lokacin Yarima Lateef yayi auren biyayya ne kawai ba don yana son Rumana ba, sai bayan auren kuma ya gane cewar zaɓin mahaifinsa kyakykyawan zaɓi ne a gare shi, kuma dama abinda yasa baya son auren ganin cewar yayyansa Yarima Adam da Yarima Ishaq basu yi aure ba, sai yake ganin kamar babu dacewar ace shi ya riga su yin aure.
wannan aure na Yarima Lateef shi ya ƙara janyo masa baƙin jini a wurin ƴan'uwansa musamman Yarima Adam.
kuma auren nasa babu jimawa shima Yarima Adam ɗin ya bijiro da nasa inda ya kawo ƴar gidan gomnan garin gombe a matsayin wacce zai aura, bayan zugo shi da Jakadan Sarki yayi akan cewar muddin yana son kujerar mahaifinsa to yayi aure tun mahaifinsa na raye, idan kuwa ba haka ba wannan burin mulkin nasa da saurautar zasu ta shi a tutar babu ne, dan zai kasance abu me wahala a ba shi saurauta alhalin baida iyali.
shi kuwa a sanda Jakada ke ba shi wannan shawarar ji yake da zai iya kashe Lateef ba tare da kowa ya sa ni ba da babu abunda zai hana shi, to tsoronsa ɗaya ne, ya riga ya sa ni abu ne me sauƙi Mai Martaba yasa shima a kashe shi ko kuma ya kashe shi da hannunsa.
dan Mai Martaba kan mance da kowa da komai akan Yarima Lateef, kuma yasha tarasu ya faɗa musu cewar zai iya yin komai akan Lateef.
kuma bayan rasuwar Sarki Hashim Bukar anyi tata ɓurza wajen naɗa magajinsa, don har sai da ta kai ta kawo duka Yaran sun fito da abunda yake zuciyoyinsu ƙiriƙiri, rigima ta ɓarkewa junansu kowa na ganin ya cancanci a basa wannan sarautar. majaifiyarsu Sarauniya Falmata ta shiga tashin hankali mara misaltuwa akan babban yaƙin dake shirin ɓarkewa, Lateef shi ɗaya ne me ƙoƙarin ganin ya kwantar mata da hankali domin har sai da ta kai ga ya ɗauketa daga ƙasar ya fitar da ita da matarsa me jaririn yaro a lokacin, saboda komai zai iya faruwa hatta ga rasa rayuka kuwa.
to amma dai yake Allah ya tsara cewar Lateef shi zai hau kujerar mulki, duk irin yanda Adam ya kai ruwa rana wajen ganin ya hana faruwar hakan shi da muqarrabansa amma Allah bai ba su iko ba. daga ƙarshe haka dole suka haƙura suka zubawa sarautar Lateef ido wadda yake gudanar da ita cikin gaskiya, tausayi gami da jin ƙan al'umma kamar yanda mahaifinsa ya aiwatar a lokacin nasa mulkin.
Sarki Lateef ya gaji mahaifinsa ne wajen auren mace ɗaya tun auren da mahaifinsa yayi masa na Rumana, kuma lokacin da Sarauniya Rumana ta haifi ɗa na uku Allah ya yiwa Sarauniya Falmata rasuwa.
bayan rasuwartata ne wannan ɗan guntun haɗin kan dake tsakanin ƴaƴanta wanda yake na dole a gare su saboda ganin idonta sai ya ƙarasa rugujewa, don tana rasuwa kowa ya kama gabansa, da yake da