NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 40 of 323

na roƙonsa akan dan Allah ya bawa Maama haƙuri. maganar ta ke tana karyewa saboda kukan dake fita daga bakinta. ta leƙo taga Turakin na tsaye ne ya harɗe hannayensa ta baya yana fuskantar gabas, kansa a sama kamar me tunani. ita kuma Nihal gwiwoyinta na zube a ƙasa a gabansa. kafin ya juyo gareta yaci gaba da magana bayan shirun da tayi. "arziƙi da talauci duka na Allah ne, idan Allah ya baka arziƙi ba yana nufin kafi kowa bane acikin bayinsa, kuma ba wai an baka dama ba ne dan ka wulaƙanta wanda bai da shi ba, shima idan Allah yaso yana iya ba shi nasa rabon, ko kuma ya ƙwace daga hannun kai da kake wulaƙanta talaka ya bawa wanda ka raina...but kin san me nake so ki fahimta?". Nihal ta ɗago da kanta tana kallonsa, sannan ta girgiza kanta alamar a'a. shi kuma yaci gaba,"Mama uwa ce da yau ba zata so ace ƴarta ta shiga gidan da zata wahala ba, wannan haka yake ga kowacce uwa...burin iyaye ne ace ƴaƴansu sunyi aure sun zauna a inda zasu ji daɗi, dan haka Maama bata hana alaƙarki da shi ba ne saboda yana talaka ba...". tun bai kai ga ƙarasawa ba ta katse maganarsa,"Allah Hammah tace makusarsa a wajenta shine talaucinsa, banda haka babu abinda zai hana ta barina mu'amala da shi...kuma ni wallahi Hammah ina sonsa, shi kaɗai zuciyata ke da muradin aure". ya kai hannu ya shafo wuyansa yana mai lumshe ido ya buɗe. "ba za'a hanaki aurensa ba dan kawai yana talaka, idan har na gari ne to ba shi da wani aibu a idon Baffa...saboda haka ki kwantar da hankalinki, ta shi muje". ta miƙe ya kama hannunta suka fita. Fillo ta sauke ajiyar zuciya, duk yacce ta ke tunanin mutumin nan ba haka yake ba. shi ɗin me kyau ne, kuma ta fahimci yana da kyan zuciya. Da yawan masu business suna so advertisemnt ɗinsu yazo da wani salo da kai kanka zai burge ka. *LOGO* tactics ne na janyo hankalin customer. Now mutane da yawa will think haɗa logo na d wuya but in truth indai mutum zai dage its simple like ABC. android phone kawai kuke buƙata da Knowledge n graphic design. abunda ake samun kuɗi da shi yanzu shine graphics design, kuma the minium abinda ake samu per desgn 500 ne...Imagine idan a kowacce rana zaku yi aikin mutum 5...500×5=2500 to d zaman banza ba gwara ki koyi abinda ko da ₦100 ne kike samu kullum b akan babu. Students da ke zaman ASUU you can leverage on it before resuming school. this 2500 na kullum abinda zai yi making a month is 75k. to ko d wannan 75k b kya ja jari ba? now if ace kina son koya and we are ready to teach u this graphic design a kuɗi ƙalilan? Normal Price is 2k wanda zasu biya da wuri is 1500. Special Class is 5k. lecture wll commence on 27th of this month...start making your payment before loosing this big oppurtunity. contact 08024976578 *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *13* Hakimi wato Alhaji Babba zaune akan royal chair ɗin dake tamfatsetsen parlon da ya gaji da tsaruwa da kayan alatu, duk wani kayan jin daɗi na mo re rayuwa an zuba a wannan parlon, haka idan har kai farin shiga ne a zuwa gidan, to tabbas zaka iya rantsewa ba'a ƙasar nigeria kake ba. farin rawani ne akansa, kana masa kallo ɗaya zaka san jinin sarauta ya gama ratsa shi. kamar yanda tarihi ya gabatar, an kafa Masarautar Gombe a shekarar 1804 a lokacin jihadin Fulani wanda Buba Yero mabiyin Usman ɗan Fodio ne. Buba Yero ya mai da Gombe (Abba) hedikwatarsa ​​domin yaƙin da ake yi da matsugunan Jukun na Pindiga da Kalam, daga nan kuma yayi ta kai hare-hare har zuwa Adamawa da ke gefen kogin Benue. a lokacin sarki Alhaji Bukar Dukku shi ke riƙe da sarautar garin gombe, bayan rasuwarsa ne kuma babban ɗansa Hashim Bukar Dukko ya karɓi sauratar, wanda ya riƙe sarautar tsawon shekaru masu yawa. Sarki Hashim Bukar ya ajiye ƴaƴa a ƙalla guda takwas kuma dukansu maza, kuma duk su takwas ɗin sun fito ne daga tsatson mace guda ɗaya Sarauniya Falmata, wacca a lokacinsu ne aka kafa tarihin sarkin daya zauna da mace ɗaya tal a karagar mulkinsa har rayuwarsa ta ƙare ba tare daya mallaki ko da ƙwarƙwara ba. cikin ƴaƴa takwas daya bari sune Adam, Ishaq, Lateef, Harun, Ibrahim, Yusuf, Isma'il, Shu'aib. akaf cikin yaran babu wanda ya samu kulawa me girma da gata daga wurin mahaifinsa irin babban ɗansa Adam, kasancewar tunda Sarauniya Falmata ta haife shi sai da ta shafe shekaru shida kafin ta ƙara samun wani cikin, lokacin har sun yanke tsammani da samun wani rabon, kuma daga haihuwar Yarima Ishaq shikenan ta shiga jero haihuwar ƴaƴa har sai da ta jera 8 gaba ɗaya. duk da ƙarancin shekaru da Yarima Adam ke da shi a wancan lokacin, hakan bai gaza fahimtar cewar shi wanene ba, ya san daga tsatson daya fito, domin a ko da yaushe mahaifinsa na faɗa masa cewar gaba da bayansa shi ɗan sarauta ne dan ko mahaifiyarsa ma ƴar sarki ce. bayan tarin ƙauna, soyayya, gata da kulawa wadda Yarima Adam ya samu a wurin mahaifinsa da mahaifiyarsa, sai kuma na ɓangaren al'umma. waɗanda suke ƙasƙan da kansu a gare shi matsayinsa na ɗa ɗaya tilo a w
🏠