NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 4 of 323

te jo". (Barka da zagayowar ranar haihuwarka Yayana. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana masu albarka.) fuskarsa ta ƙara washewa da annuri, ƙwayar idonsa na haskawa da wani ƙyalli na farin ciki. sai ya dangwalo icing cake ɗin ya lakuta mata a hancinta da gefen kumatunta kamar itace birthday girl ɗin, yana faɗin. "Special thanks to you Sweetest". daga nan kuma ya dinga yankar cake ɗin yana sakawa sauran sisters ɗin nasa a baki, suma duk suna binsa da wishing. haka ya gama basu sannan suma kowacce ta yanko ta nufo bakinsa da shi, sai dai bai karɓi na kowa ba sai daya fara amsar na Maama da Zaitoon tukunna. suna haka Kalil ya shigo aka ɗora da shi, gaba ɗaya shi sai ya koma ma kamar shine me birthday ɗin, dan gaban cake ɗin ya zauna yana ta ci. kuma zuwansa wurin sai yau sauya ƙaramin birthday partyn da Maama ta haɗa zuwa babba. cike da murna gami da so da qauna for one another suke ta abinsu, kowa jikinsa ya ɓaci da cream na jikin cake. ** *Ɓangaren Masu Aiki.* *17:40 pm.* "Fillo karki zauna dan Allah". wata ƴar tsohuwa fara ƙal dake zaune a gefen katifa tana cura fura ta faɗa. "Kaka am debbo ba zan jima fa yanzu zan dawo". ta faɗa tana zura hijab kalar c-green wanda ya ɗauki farar fuskarta matuƙa. ta zura siririyar ƙafarta cikin takalmi sannan ta nufi ƙofa tana faɗin,"sai na dawo Kaka". Can bayan gidan ta nufa, kasancewar yamma tayi hayaniya ta ɗan ɗauke ba kamar da safe ko rana ba, mafi akasari a irin wannan lokaci masu hidimar gidan sun tafi don hutawa kasantuwar ayyukan da suke sha tun sanyin safiya. da yake gate ɗin gidan biyu ne, kuma gate ɗin baya ta nan ma'aikatan gida ke shige da ficensu, shi kuwa main gate na masu gidan ne. a bakin bishiyar da Amir ya saba tsayuwa duk sanda yazo anan ta same shi yanzuma, ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa ya jingina da jikin bishiyan yana jiran isowarta. tun daga nesa daya hangota ya kafeta da ido, kuma kamar kullum sai Fillo ta tsaya da tafiya tana ɗan turo baki gaba. ganin hakan yasa Amir ɗauke idonsa daga gareta yana fitar da siririyar dariya a fuskarsa. sannan yasa tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa. bai san da ƙarasowarta wajen ba sai jin maganarta yay acikin kunnensa tace. "ja66ama". (barka da zuwa) tai maganar a hankali. sai a yanzu ya buɗe fuskar ya juyo da fuskarsa zuwa gefen damansa inda ta ke a tsaye, bai ce mata komai ba sai wani sanyayyan murmushi daya ɓalle masa a saman fuska. irin kallon da yake mata yasa taji nauyi ta rufe fuskarta tana ƙara faɗin. "awari jam?". (anzo lafiya?) nan ma shiru yay bai amsa mata ba, itama kuma bata jira ƙara cewarsa ba ta kuma ɗorawa da faɗin. "noi him6e sare?". (ya mutanen gidan?) Amir ya sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya tare da jan leɓensa na ƙasa zuwa cikin bakinsa ya tsotsa kaɗan. a shagwaɓe  tace,"wai yau ba za'a min magana bane?". har yanzu murmushin dake kan fuskarsa bai ɗauke ba yace,"mi tawi on jam?" (na sameki lafiya?) "lafiya lau". ta faɗi hakan tana ƙara yin ƙasa da fuskarta da alamar dai macece ita mai kunya sose. "Inna vi mi hofnuma". (Inna tana gaisheki) "mi ja6i". (ina amsawa) "shine kika barni na daɗe a tsaye haka ko?". ta ɗan cije leɓenta kaɗan tana kallonsa sannan tace,"kayi haƙuri. na tsaya ƙarasa aiki ne, kasan me Martaba baya nan, to kuma duk sanda zai dawo Kaka ake bawa aikin fura, shi ne yau bamu gama da wuri ba sai yanzu. yanzu haka ma na taho na barta tana ƙarasa curawa ita ɗaya. da ta gama zamu tafi can masarautar mu kai". "Allah sarki Kaka…Allah dai ya kawo min arziƙin da zanzo na ɗauke ku nan bada jimawa ba". ta haɗe girarta alamun son ƙarin bayani akan abinda yace. sai ya ɗaga tasa girar yana cewa,"ehh mana, ai idan na aureki ba ke ɗaya zan ɗauka ba. har da Kaka zamu tafi…Halimatu indai na aureki to lokacin hutun Kaka ne yayi". wannan furucin na Amir zuciyarta taji ya ƙara burgeta, ta kuma ƙara yin amanna da shi. muryarta mai sanyin nan ta fito a hankali da cewa,"Allah ya buɗa ya bada arziƙi mai yalwa da albarka. ya kaimu lokacin". "ameen ƴar aljannah". ya faɗi hakan sanda yake sunkuyowa daidai fuskarta. "yanzu bari na barki kije kici gaba da taya Kaka aiki, nasan yana da yawa. gobe in Allah ya kaimu na dawo". "tom shikenan Allah ya kaimu. ka gaida min da Inna idan ka koma". ya sunkuya ya ɗauko wata ƙaramar baƙar leda daya aje a ƙasa ya miƙo mata. "ga wannan. mangoro ne da bai nuna ba irin wanda kike so". tasa hannu biyu ta amsa cike da jin daɗi. "amma kam na gode. dama ranar nan Maijidda ke ce min ta ganshi a kasuwa da suka je, ina ta kwaɗayinsa tun ranar ashe da rabon zan sha". "nima na fito zan taho wajenki naga ni a bakin hanya, nace to ba zanzo haka ba hannu na dukan cinya, sai na siyawa farin cikina wani abun". yatsun hannunta na naɗe acikin ledar tai murmushi da ƙara yi masa godiya. sai data juya ta nufa cikin gida sannan shima ya juya ya tafi. "Fillo! Fillo!!". muryar Maijidda dake fitowa daga nasu ɓangaren ke ƙwal
🏠