lula wani wurin can daban da tunanin abinda ya danganci asirin.
"to shikenan Allah dai ya kyauta...ni ma kinga zamu je gidan Alhaji Babba ne akan lamarin Hammansu, sam yaƙi aure kuma ko zancen auren baya so ayi masa, mun rasa kuma dalilinsa dan ko jiya sun fi awa shi da Baffansa kan ya sanar masa da dalilinsa yace shi babu komai haka ɗaya, sannan babbar matsalar duk wannan nacin ibadar tasa yanzu ba yayi, sai kiga ko sallah ake yana zaune...to shine Boɗejo ke ganin abun kamar ba lafiya ba".
Hajiya Madina ta faɗawa ƙawarta Lubna da suke wayar.
daga ɓangaren Lubna ɗin tace,"subhanallah, gaskiya kam dai wannan labari ba lafiya ba a tashi a nemi magani, namiji har namiji kamar Turaki ace baya son aure, ai lamarin akwai duba...Allah dai ya kawo komai da sauƙi".
Hajiya Madina tace,"amin ya Allah...shikenan sai mun ƙara yin waya, dan Allah karki manta da saƙon nan ki bayar akai musu".
daga ɓangaren Lubna ta sake cewa wani abu sannan Hajiya Madina tace,"ina ta ƙoƙarin yin hakan. sai dai ina tsoro Lubna, ban san mutanen dake bibiyar rayuwarsa ba, haka ban san wanne irin shiri suke yi akansa ba, dalilin da yasa na dage akan cewar ya haƙura da kowanne irin aiki zamansa a gida shine kwanciyar hankalinmu, haka kuma shima a nasa ɓangaren wannan ne kaɗai tsaron da zai samu...wallahi ba ki ga munin last accident ɗin da yay ba, Lubna sai dana gama cire rai da shi tukunna ya farfaɗo...amma akan maganar wannan company ɗin da Baffa ke cewa zai buɗe musu wataƙila na yarda ya zama jagoran ciki amma in har bai ɗara daga state ɗin nan ba, amma muddin wani gari ko wata ƙasa ce can daban hakan ba zai yiwu ba".
haka suka ci gama da tattaunawa tsawon mintuna kafin suyi sallama. ta ajiye wayar tana mai cewa da Fillo,"buɗe wancan closet ɗin ki ɗauko min wasu takardu daga sama".
Fillo ta miƙe dan cika umarninta, tana ɗauko takardun tana mamakin irin jama'ar da Allah ya bawa Hajiya Madina, ko da yaushe acikin yin waya ta ke, inda take gani da itace gaskiya ba zata iya ba, domin idan kunnenta bai ciwo ba to bakinta zai yi. yanzu fa ta gama waya ko minti biyu ba'a ƙara ba amma har an kuma kiranta.
"zan bar su a gida, akwai yarinya idan kazo zata baka". abinda ta ke cewa dana wayar kenan, kuma lokacin da Fillon ta ƙaraso ta durƙusa ta bata takardun.
"alright sai ka zo".
daga haka wayar tasu ta yanke, ta dubi Fillo tace da ita,"gobe za ki fara ɗaukar karatu a gidan nan, ba ke ɗaya bace akwai wata sabuwar ƴar aiki da za'a kawo anjima za kuci gaba da aiki tare. bana son fitina Halima, bana son kuskure, ki kula da hakan. karatun boko da arabiya zai ke yi muku. ki tsaya ki maida hankali, domin akwai aikin da nake so kiyi min, aiki ne na masu ilimin boko, idan kin mayar da hankali, idan har kinyi nasarar samunsa Halima za ki sha mamakin yarda zan mayar da ke, duniyarki zata sauya, za ki zama abar kwantance, bayanki zai zama tarihi, idan kuma akasin hakan, tabbas ina mai tausaya miki da asara mafi girma da za kiyi a rayuwarki".
Fillo so ta ke ta ɗago ta kalleta amma ta kasa, jan yatsunta kawai ta ke. "ungo wannan". sai a sannan ta ɗago tasa hannu biyu ta karɓi takardun.
"ki adana su, zuwa ƙarfe biyar na yamma akwai wani zaizo ya karɓa, baƙi ne dogo yana da ƙasumba...ba shi kawai nace kiyi, kije masa da fuskar mutumcinki Halima...nasan kin gane lissafina".
Kan Fillo a ƙasa tace,"tom Hajiya".
"bani lafayata fara".
Fillo ta miƙe ta ɗauko ta kawo mata. ta cikin mudubi Hajiya Madina ke ta kallonta, zuciyarta na me jin so da tausayin yarinyar.
bata bar kallonta ta cikin madubin ba tace,"zo ki saka min wannam fil ɗin". Fillo ta matso zuwa bayanta ta karɓi fil ɗin a hannunta sannan ta saka mata kamar yanda taga Zaytuna nayi mata a duk sanda ta saka lafaya.
ita ta ɗaukar mata jakarta suka fito a ɗakin, suna saukowa ta ke faɗa mata,"akwai key ɗin ɗayan bedroom na Hammansu acikin drower na mirrow, idan mun fita kije ki gyara masa. dan Allah ki gyara me kyau, ki kaɗe duk wata ƙura".
"tom Maama, sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya ya dawo daku lafiya"
har bakin mota tai mata rakiya, Khalil ne zai ja motar dama, ta shiga tana tambayarsu,
"ina Hammanku da Nihal?".
Sameer yace,"Hamma ba lallai yasan mun fito ba, amma naga Nihal tayi wajensa da nake fitowa".
"kira min shi".
Sameer ya ɗauki waya ya kira shi, sai dai kamin ta kai ga yin magana ma yace gashi nan fitowa.
Fillo kuwa tana komawa key ta ɗauka ta fito ta wuce ɓangaren Turaki, ɓangarensa dake jikin na Baffa. tana shiga parlon taji maganarsa na tashi a parlon.
tayi saɗaf ta ɓoye ta wajen wani corrido, dan har ga Allah ita ba so ta ke suke haɗuwa ba saboda bata son wannan tsawar da yake sakar mata, yana sakata tana tunawa da moment ɗin da ba son tunawa da shi ta ke ba.
kuma har zuwa wannan lokacin tana ƙyale shi ne kawai saboda darajar mahafiyarsa, banda haka da tuni ta nuna masa tafi ƙarfin ya dinga zaburar da ita dan kawai tana aiki ƙarƙashin arziƙinsu.
shi da Nihal ne wadda taji ta