ala". abinda tace da Fillo kenan ta kashe wayar. wanda a ɓangarenta azamar tashin ta ke yi saboda tana lissafe ne da lokaci, su kan ɗauki 10-15minutes a dining, kuma buƙatarsu da zarar sun kammala da shi ai clearing wurin.
tana shigowa parlon Hajiya Madina na shirin hawa upstairs, ta kalleta tace mata.
"idan kin gama ki sameni a ɗaki". Fillo ta amsa da,"tou". sannan ta shiga gyara wajen.
komai nata cikin sanyin jiki ta ke yinsa amma kuma nan da nan ta ke gama abu, tana gama wanke-wanke bata tsaya ɗora lunch ba tunda tasan basa nan kuma bai wuce suyo takeaway na dinner ba idan sun tashi dawowa.
zata wuce ɗakin Hajiya Madina Khalil dake parlon a zaune shi ɗaya ya tsayar da ita.
"sojan rana zo nan".
ta tsaya daga hawa saman ta juyo da murmushi fuskarta, abunda ke burge shi da ita fara'arta da tsabtarta, bata da wannan cunkus ɗin irin na sauran ƴan aikin da suka yi a baya.
har ta ƙaraso ta tsuguna a gefen kujerar da yake zaune bai bar kallonta ba, kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace,"Hamma Khalil gani". ta faɗi sunan nasa kamar yanda taji ƙannensa na faɗa masa.
yace,"ai nai zaton ko kina ciwon baki ne". ya faɗa da salon zolaya.
ta murmusa da cewan,"ciwon baki kuma?".
yace,"ehh mana, da na kiraki ai ba ki amsa ba tahowa kawai kika yi".
ta saki murmushi me faɗi da cewar,"Hamma Khalil to ai kaine kake faɗin sunan da ba nawa ba, shisa sai nayi zaton ko bada ni kake ba".
shima murmusawar yay kafin yace,"yanzu ke tsakani da Allah duk wanda ya ganki ranar nan da kika yi ƙeƙam a tsakiyar rana me zai yi zato?, kinga kam dan na kiraki da sojan rana ai ba laifi ba ne".
murmushi kawai tayi bata ce komai ba.
"anyway, wanne class kike before ki taho aikatau?".
furucin da yay yasa ta ɗagowa ta kalle shi kaɗan sannan ta mayar da kanta ƙasa.
"bana zuwa makaranta ai".
da mamaki ya kalleta,"gaba ɗaya ba ki taɓa zuwa makarantar boko ba?".
ta ɗaga masa kai tabbacin hakan.
ya girgiza kansa,"to islamiya fa?".
ruwan hawaye ya cika idonta kafin tace,"nayi islamiya kamin Ummi ta rasu, kuma itama tana yi min a gida".
yace,"wace Ummi?".
sai da tasa hannu ta goge hawaye tukunna tace,"mahaifiyata".
lokaci ɗaya tausayinta ya kama shi. "Allah ya jiƙanta". ta amsa da,"amin na gode, Allah yaja da ransu Baffa". shima ya amsa da,"amin na gode. amma kuma idan baki je makarantar boko ba taya akai ranar nan kika karanta saƙon da Maama ta bar miki?".
taja yatsanta na tsakiya bata ce komai ba. ya katse shirun,"tambayarki nake". murya a hankali tace,"wanda zan aura ne ya fara koya min yanda zanyi karatu, kuma daga baya sai muka daina saboda ayyuka da suka yi masa yawa".
kalmar wanda zan aura ta ba shi mamaki. to amma sai dai aure wa ƙaramar yarinya kamar wannan a wajen ƴan ƙauye ba wani abu bane, wataƙila da ace ba anan suke zaune ba yanzu haka tana da ƴaƴa. ya sauke numfashi yace,"yayi ƙoƙari shi wanda za ki aura ɗin...yanzu yaushe ne bikin?".
tace,"ba'a tsayar ba tukunna amma dai da an kusa wani dalili yasa aka ɗaga". ta faɗi hakan idonta na kawo ruwa sosai, kuka ta ke sonyi a lokacin amma saboda Khalil ɗin ta hana kukan samun ƴancin fita daga bakinta, domin bata so ya gano wani ciwo da rayuwarta ke ɗauke da shi.
ya ɗaga kafaɗarsa ya ajiye wayarsa sannan ya fuskantota gaba ɗaya. "to kin san menene?, mu a gidan nan idan mutum zai yi aiki dole sai yana karatu, kije ki tambayi duk wanda ya taɓa aiki anan, haka tsarin Baffa yake...and dalilin daya sa ma inaga Maama bata yi miki zancen ba kwana biyu aiki ya sha kanta ne, amma yanzu idan kinje ki tuna mata, akwai Malamin da yake zuwa yana yi muku karatu".
ta ɗago ido tana kallonsa, kamar bata fahimci me yake son cewa ba. ya ɗaga mata gira,"ehh idan kinje ki cewa Maama ke ba ki yi karatu ba". ta gyaɗa kai kawai sannan ta miƙe zata wuce. Turaki ya shigo parlon a lokacin yana waya. ta gabansa ta wuce tana ji yana cewa,"me zan yi da yarinyar da bata waye ba, ka bar wannan batun she is not my type...infact ni babu aure ma a lissafin rayuwata".
hannuwan Fillo suka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta buɗe, tayi sallama amma ba'a amsa ba. hakan yasa tasa kai zuwa ciki ƙafafuwanta na luntsumewa cikin tattausan carpet ɗin dake malale a duka ɗakin tun daga bakin ƙofa, kai kace cikin auduga kake sanya ƙafa saboda tsabagen taushi.
tayi tsaye daga nan bakin ƙofar bayan ta maida ƙofar ta rufe, jikinta take takurewa saboda yanda sanyin ac ke ratsata. ta kusan minti uku tsaye sannan Hajiya Madina ta fito daga wata ƙofa da idan ba sani kai ba ba zaka ce ƙofa bace. da sauri ta durƙusa a ƙasa tana kama gefen zanenta ta riƙe. dalilin wani abu da yayi duka acikin kanta sanadin furucin da taji Hajiya Madina tayi acikin wayar da ta ɗauka yanzu da aka kira.
"asiri fa kika ce Lubna, wa ya faɗa miki?". abinda Hajiya Madinan ta fara kenan cikin muryar razani, amma ita a wannan lokacin kalmar asirin ce ke ta maimaituwa acikin kwanyar kanta, lokaci guda kuma hankalinta ya gushe daga cikin ɗakin ta