NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 37 of 323

una tana ɗauraye hannunta, ta ƙarasa tana yi mata sannu da aiki. Zaytuna tace,"yau kinyi late". Fillo tai ɗan murmushi tace,"na tsaya yima Kaka aiki ne zata yi baƙi". "oh Allah sarki, jikin nata dai da sauƙi ko". "ehh taji sauƙi sosai". "to Allah ya ƙara mata lafiya". "amin ya Allah". ta nufi drower ta taka kujera ta ɗauko babban tray, Zaytuna na goge hannu a towel tace,"na kammala komai fito da su kawai za ki...kiyi da jiki dan Allah zamu fita ne har da Baffa". "tom Adda". Zaytuna ta dakata daga fitar da zata yi ta tsaya tana kallonta, ta girgiza kai kawai sannan tace,"wannan jiki naki Fillo anya ba sai mun nemi magani ba, komai kike salalo salalo kamar mara jini ajiki". tana faɗar hakan ta juya zata fita ta bar Fillo da ƴar dariya. Turaki ya shigo kitchen ɗin ko maganar da Zaytuna ma ke yi bai tsaya sauraro ba. ya wuce kai tsaye wajen drink trolly ya ɗauki mug, Fillo na shirin ɗaukar tea flask ta ɗora akai muryarsa ta tsayar da ita, ita bata ma san da shigowarsa ba. yo ita me ta sani da wani wait ɗinsa da zai ce mata wani wait, mutumin da ba zai yi hausa zalla ba dole sai ya haɗa da yaren da ita bata iya shi ba, ko da yake taga duka haka suke, shi yasa wataran suke shanyata a tsaye idan suka faɗi abinda bata sani ba, banda late da Zaytuna ta saba faɗar mata shi har ta fahimci me hakan ke nufi to me ta sani bayansa. dan haka kawai sai ta kuma yunƙurin ɗaukar tea flask ɗin, Turaki da idonsa ke kan hannun Flask ɗin da zata kama yace,"Wae ankam a iri 6iddo toi kam a nanako volwanego?". (wai ke wacce irin yarinya ce da ba'a faɗar magana kiji ne?) kakkausar muryarsa a sama ya doka mata tsawar da ta saka ta ture flask ɗin ba tare da saninta ba, ya zamo zai faɗi ƙasa yay saurin isowa ya tare shi. kamar yasa hannu ya bibbigeta don haushi, shi haushinsa da yarinyar saurin rikicewarta akan abindai bai kai ya kawo ba. ga shi ya tsana yaga da anyi magana jikinta ya hau rawa, shi yasa ya cewa Maama su kaita asibiti a binciki lafiyarta. ta ɗauki tsawon 2mints jikinta na rawa kamin ta daidaita, ta buɗe idonta da ta rumtse gam ta sauke kan dogayen yatsun ƙafarsa, sannan ta sauke hannunta daga kare fuskarta da tayi. sai lokacin ta ɗago ido ta kalle shi, ita yakewa wani irin kallo da bata son gani a wannan ƙwayar idon nasa da bata kama da ta mutane. muryarta kamar zata yi kuka tace,"Wadu munyal mi anda be min a vondi on". (kayi haƙuri ban san da ni kake ba). ya zabga mata harara ya bar wajen, ya ƙarasa ya buɗe coolers ɗin da Zaytuna ta zuba kayan soye-soyen da tayi, ya zuba chips a plate sannan ya zuba tea a mug ya fice. Fillo tabi bayansa da ido kawai, ita bata tasa ta ke ba, burinta yanzu bai wuce ta sami damar ahiga ɗakinsa ba, ba tare da sanin kowa ba ta gudanar da abinda zata yi. shi yasa ta ƙagu suyi-suyi su fice. *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *12* bayan ta gama jera komai a dining tazo ta tsuguna gaban Hajiya Madina. "Maama ko mai ya kammala". sunan da yaranta ke kiranta da shi itama da shi ta ke kiranta, Hajiya Madinar ta faɗa mata haka a watarana, sanda ta ke ce mata. "Fillo ban taɓa ƴar aikin da nake jinta tamkar ƴar cikina ba irinki, saboda haka daga yau Hajiya ya fita daga bakinki, ki dinga kirana da Maama kamar yanda kika ji ƴaƴana nace min kinji". Hajiya Madina ta shiga kallonta ta wutsiyar idonta ba tare da ta amsawa maganarta ba, Fillo kuma dai har yanzu tana nan durƙushe bata motsa ba, kuma tunaninta bai bata ko Hajiya Madinar bata ji ba ne, a'a tasan taji kawai dai a jininsu ne basa amsa maka nan ta ke sai sun ɗan ɗau lokaci. "oak tom, kije ki zuba naki kici". abinda Hajiya Madina tace da ita kenan. Fillo ta miƙe ta wuce, sannan suma suka nufa dining, by the time Turaki har ya gama nasa, yana zaune wajen yana aikin danna waya. suna cikin yin breakfast ɗin ne wayar Nihal tayi ƙara, ganin sunan dake yawo jikin screen ɗin wayar gabanta ya faɗi, jikinta na rawa ta kai hannu tana gyara zaman medical glass nata, ta cikinsa ta ke kallon Hajiya Madina wacce ta dakata da cin abincin tana yi mata wani duba ta ƙasan ido. duk ta dabarbarce, tsoronta Allah tsoronta kar tace ta miƙa mata wayar. saboda haka tayi saurin kai hannu tai mute na ringing ɗin, sai dai kamin ta ɗauke hannunta daga kan wayar sabon kira ya ƙara shigowa. babu shiri ta haɗiye wani dunƙulallan yawu tare da rufe ido. sai dai kamin ta buɗe maganar Hajiya Madina ta shiga cikin kunnuwanta. "give me the phone". kamar zata yi kuka ta ɗauki wayar hannu na rawa ta miƙa mata. Hajiya Madina ta kashe wayar gaba ɗaya sannan ta miƙawa Khalil, ya karɓa ya saka a aljihunsa. har suka kammala breakfast ɗin babu wani wanda yay motsi na hira ko kuma tsokanar juna kamar yanda suka saba da mahaifiyar tasu, saboda yanayin da ta tashi da shi yau sun kasa gane kanta, ga shi Nihal ta ƙara dagula musu ita. Samha ta ɗaga landline en dake gefensu ta kira wayar ɗakin ma'aikata. bugun da bai wuce 2 ba Fillo dake can ta ɗaga. "ke kizo mun kamm
🏠