NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 36 of 323

a mata ko Amir ne ya kawo, to amma iya ƙoƙarinsa dai tasan baida kuɗin wannan uban sayayyar. tana tambayar Kaka tace mata ai Zaytuna ce suka zo ita da Yayanta suka kawo mata, a lokacin bata kawo cewar Turakin ba ne dan haka kawai godiya tayi tana daɗa faɗawa Kaka kirki irin na Zaytuna da Hajiyarsu, Kakan itama na ƙara faɗar nata kirkin da ta san Zaytunan da shi a ɗan tsukukun zaman jinyar Turaki da tai. Sai da Fillo ta shiga ɗaki taga ledar drip da tarin magani akan katifarsu sannan tai saurin fitowa daga ɗakin, tsayawa tayi kawai tana kallon Kaka kafin ta iya buɗar baki tace,"Kaka wa akaiwa ƙarin ruwa?". Kakan tace,"ni ce, ai da suka zo dubani ɗinne sai shi Yayan Zaytunan ke cewa ina da buqatar asamin ruwa domin na samu ƙwarin jikina. yana zaune anan ya kira likita yazo ya dubani shine har ya biya kuɗin waɗannan magungunan, ina ji likitan yana lissafin kusan dubu takwas Halimatu...ai yaran nan sunyo halin iyayensu". a lokacin hannu Fillo tasa ta goge hawayenta bata ce wani abuba. kuma tun daga ranar kullum sai Turaki yazo ya duba jikin Kaka sati guda kenan. ita bata ma san shine Turakin da tai kasada akansa ba sai ranar da Hajiya Madina ta aikata ɓangarensa tace tai gyara. anan ne tana shiga taga lafcecen enlergment ɗinsa a jikin bangon bedroom ɗin wanda daka shiga shi zai fara maka maraba. kuma a sannan babu hoton abinda ya shiga haskawa a idonta sai na sunansa dake jikin wannan farar takardar da ta ƙona, kamar yanda akai rubutun manya ajikin hotonsa haka ma yake a jikin takarda. tarin tambayoyi da mamaki suka maƙale a kwanyar tunaninta. tambayoyin da ta ƙudurcewa ranta son sanin su nan kusa bada jimawa ba in har taci gaba da zuwa aiki, tunda Hajiya Madina tace ko da Kaka taji sauƙi ba zata dawo ba ita zata ci gaba da aikin. dan sosai Hajiya Madina ke sonta, tunda ko da akace za'a ƙaro wasu ƴan aikin tace a'a a barsu ita Halimatunta kawai ta isheta yanzu, inma zaa ƙaro to a ƙaro ɗaya saboda kar aikin yay mata yawa, kullum cikin yabonta take tace bata taɓa ganin yarinya me hankali da natsuwa ba irinta, hakan yasa ta ke jin daɗin aikin sosai. ko a ƴaƴanta ma da Samha ne kawai basa wani ɗasawa amma ko Khalil idan ya ganta ya dinga tsokanarta da Sojan Rana. kuma sau tari indai Hajiya Madina na parlo sai tace itama ta zauna ayi kallon tare da ita, Turaki ne ma ta fuskanci kamar baya so talaka ya raɓe shi, shi yasa fuskarsa kullum ɗaure ta ke akanta, ko da yake ba ita ɗaya ya kewa hakan ba har ƙannensa idan aka cire Zaytuna da Khalil. saurin da ta ke yanzu ta gama yankan farcen ta wuce don taji Hajiya Madina na faɗin yau zasu unguwa duka gida. Kaka ta katse shirunta da cewar,"kin kuwa ɗauki namanki?". ta ɗago tace,"aina?". Kaka tace,"a'a na aje miki nama cikin farar robar nan, da za ki wanke-wanke ba ki gani ba?". "ni banga komai aciki ba, ƙila Maijidda ta shigo ta wawashe shi...wa ya kawo miki nama dama?". Kaka ta dire wani hijabi da ta ke linkewa tace,"Yayan Zaytuna ne ya shigo jiya da daddare, ba ki jima da kwanciya ba lokacin...nace masa ai ma na gama warwarewa lafiya ta samu dan jibi ma zan dawo aiki shine yace a'a nai zamana na ƙara hutawa tunda akwai me taimaka min, koma da babu a nemo wata". Fillo ta miƙe ta ɗauko tsintsiya tana share wurin da ta ɓata tace,"an gode masa...yana ta abu na masu kirki alhalin ba haka yake ba". Kaka dai shiru tayi, ita kuma ta ɗauki hijabi tana ce mata. "zan tafi Kaka. yau babu kula da buƙatun ɗan gwal da wuri zan dawo dan naji Hajiya tace zasu je unguwa". Kaka tace,"sai kin dawo ki gaida Hajiyar". tana fitowa haraba sukai kiciɓis da Maijidda, Fillo ta tsaya tana kallon yanda ta ke jera hamma daga gani kaga wadda ta taso a bacci. Maijidda tace,"yauwa dama wajenki za ni". ta faɗa tana miƙa mata wayar hannunta tace,"Amir ne ke kira tun asuba". Fillo ta kallesu ita da wayar kafin tace,"kuma ai sai kice masa bama tare". Maijidda tayi hamma sannan tace,"ai yaƙi gane wannan bayanin, ni dai ungo idan kin gama kya kawo wallahi mugun bacci ke idona". ba tare da Fillo ta karɓa ba tayi gaba abinta da cewar,"sai ki faɗa masa kinzo ba ki sameni ba". Maijidda tabi bayanta da kallo tana faɗin,"ni ban iya ƙarya ba, Allah haka zan faɗa masa kince idan yazo ya sameki acan". a parlo ta samesu kaf ɗinsu, ita kam rayuwarsu na burgeta. ta durƙusa ta gaida Hajiya Madina. Hajiya Madina ta ajiye hisnul muslim ɗin dake hannunta a gefenta, sannan ta zare medical glass ɗin dake a idonta ta saka shi cikin box ɗinsa. ta kalli Fillo da fara'a tace,"Halimatu kin shigo?". kan Fillo a ƙasa tace,"ehh Hajiya, Kaka na gaishe ki". tace,"ina amsawa, jikin nata da sauƙi dai ko?". "ehh taji sauƙi ai, tama ce zata shigo gaida ki zuwa anjima". "a'a ita da ba ƙwarin jiki ba, zan shiga na dubata insha'Allahu...yanzu maza ki fito da break fast naga already Zaytuna ma ta kammala komai". ta amsa da,"tou". sannan ta miƙe ta wuce kitchen din bayan duk ta gaida yaran. a kitchen ta sami Zayt
🏠