NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 35 of 323

yanda Ammi tayi yace shi Nuratu kaɗai zai aura, kuma da yake mahaifinsa ba mai takurawa ƴaƴa bane, abunda suke so shi yake so haka dole aka bi abinda Yusuf ke so. Ammi tayi kamar tai hauka a lokacin, ita baƙin cikinta akan me zaisa ya auri jinin kishiya banda yana so ya tozartata a idon duniya. to fa shikenan kuma sai ya jawo ta ɗauki fushin duniya ta ɗora akansa. dama can ana ƴar hakan saboda tana jin haushin shirinsa da Umman. sam Ammi bata son Nuratu, kuma Nuratu yarinya ce me hankali. dan ko sau ɗaya ma bata taɓa nunawa Yusuf rashin jin daɗin tsangamar da ta ke samu daga wurin mahaifiyarsa ba. hasali ma idan yana bata haƙuri sai dai tace masa its matter of time hakan zai zama kamar ba'ai ba. hatta wani lokaci da Ammin taje har gidansu Yusuf baya gari ta wanke Nuratu tass akan sun asirce mata ɗa, da kuma cewar Allah ya isanta da ta aure mata yaro alhalin tasan ita juya ce. Nuratu bata taɓa danasanin auren Yusuf ba sai a ranar, saboda wankin babban bargon da Ammi tai mata na maganganu marasa daɗi da tsayawa a rai. hakanne ma yasa bayan tafiyar Ammin ta kira Umma tace ita kam tasa Yusuf ya saketa bata iya ci gaba da zama da shi, tunda dai haihuwar nan ba itane zata bawa kanta ba. ta kwashe duk abinda Ammi tayi mata ta faɗawa Umman, silar inda faɗan gaba me tsanani ya shiga tsakaninsu kenan. Umma bata biyewa faɗan kishi na Ammi, amma akan wannan abin har sai da Daddy yace shi ba zai iya da jarabarsu ba sai ya maka su a kotu. dalilin samun sauƙi kenan shima kuma dan Umman tana bagararwa ne, amma da saboda Ammi ne har gaba da kotu sai dai akai su. maganar Umma ta katse su Yusuf daga abinda suke ƙoƙarin yi, sai lokacin Yusuf ya farga ya amsa kiran sunansa da tai. "ina Nuratu?". Umman ta tambaya da ɗaure muryarta. "ga ta nan". "to bata". ya cire wayar daga kunnensa ya ɗora akan kunnen Nuratu, ta wani narke tana shagwaɓewan Umman. "ba dai ki da wata matsala ko?". Umman ta tambaya da tsansatar kulawa. tayi kamar za tai kuka tace,"Umma ni so nake mu dawo, anan bana samun duk kayan kwaɗayin da nake son ci". Umma tace,"kai Nuratu". tace,"Allah Umma, nan fa babu irin su goruba, tsamin gaye, kuma fa har Farar ƙasa ma babu Umma, ga shi duk abunda naci ni ba sonsa nake ba sai ya dawo". ta ƙarashe maganar tana fashewa da kukan taɓara. daga inda Umma ta ke tai murmushi. "ai ke kika dage sai kin bisa, amma kiyi haƙuri kinji, haka ƙaramin ciki yake Nuratu. ai kun kusa dawowa, idan kun dawo ma nan gida za ki dawo ba zan barki ke ɗaya ba...yanzu dai zan san duk yanda za'ai na aiko miki abubuwan da kike so kamin dawowar taku, kiyi list sai ki turo min". "tom Ummana. ina su Kursum?". Umma tace,"suna bedroom ɗin su". "kice ina gaida su kuma nayi fishi tunda basa nemana...kuma ko ɗansu yazo ba zan basu shi ba". Umma tace,"ai kina da wayarsu ki kira su mana". sannan ta ɗaure murya tace,"ina Yusuhun?". lokaci ɗaya Nuratu ta nemi hawa bori ajikinsa akan Umma tace Yusuhu, dan ita bata son sunan ana ɓata masa suna ya koma na ƴan ƙauye. ita kuma Umman duk lokacin da Yusuf ya ɓata mata rai ko ya ya ne sunan da take faɗa masa kenan. "bana son iya shege Malama bawa mijinki". tana ɓata fuska tace,"don Allah Umma ki daina cewa Yusuhu idan wasu suka ji sai su ɗauka". Umma tace,"to sai kizo ki faɗawa ubansa ai yay masa sabon yanka". sai around uku na yamma tukunna suka fita outing, Mommi nata jin daɗin fitar tasu saboda yanda suke ta ma ta hira su biyun, kowa so yake ya nuna bajintarsa na ɗebe ma ta kewa tamkar wasu ƴaƴanta. basu suka dawo gida ba sai after isha'i. *Nigeria, Gombe, Dikko resident.* kan Fillo duƙe tana yankan farce suna magana da Kaka, wadda ke ta yabon Turaki saboda mutumcinsa. Fillo dai bata cewa komai, dan ita duk da halin kirkin daya nuna bata jin zai wani burgeta. saboda haushinsa ma ta ke ji gaba ɗaya, har ga Allah ta tsani mutum me ji da kai, wannan yasa tun a wancan ranar da ta fara zuwa aiki ɓangarensu taji ko kaɗan bata ƙaunar ma hanya ta ƙara haɗata da shi ko bisa kuskure. ita bata ma yi tsammanin yana da halin ƙwarai har haka ba da zai iya taimakawa wani, tayi mamakinsa sosai. sai daga baya taga ashe tayi masa bahaguwar fahimta ne, bata san da yaje duba Kaka da jiki ba sai daga baya, tun ranar farkon aikin nan nata daya kira waya a ɗakin baya da akace ta zauna, bata ɗaga ba saboda baccin daya fara ɗibarta. da kansa yazo ɗakin ya sameta tana bacci, yana shirin juyawa ne ta farka, ta tambaye shi akwai buqatar wani abu ne fuskarsa a tamke yace mata babu, sai kawai ya fice daga ɗakin. kuma babu jimawa ya ƙara dawowa ya tambayeta ina tsohuwar da ta samu anan, tace masa ai ko da tazo babu kowa a ɗakin. kamar bai yarda da abinda ta faɗa ba lokacin, saboda ɗan jim yayi kamin ya fice a ɗakin. sai bayan isha'i da ta koma ne ta tarar da uban cartons jere a falonsu, maltina, madarar gwangwani da ruwa da kayan marmari kala-kala, ga kaza gasashshiya, abun ya bata mamaki sosai, duk da zuciyarta ta ray
🏠