NOVEL SHARES -
tare da girgiza kai alamar babu komai.
ya ɗan lumshe idonsa sannan yace,"masha'Allahu, Allah ya ƙara miki lafiya". ta jinjina kai alamar ta gode, sannan ta kamo hannunsa ta riƙe cikin nata, tana shaking nasu alamar nuna godiya a gare shi mara iyaka.
ya dubi Nuratu yace,"Mar'atussaliha ki shirya Mommi mu fita outing ta samu taga gari, zaman wuri ɗayan zai isheta haka".
Nurata tace da shi,"tom ur excellency". har ya miƙe tsaye zai fita kukan da Mommi ta saka ya dakatar da shi, wannan fashewar kukan nata ya haifar musu da tashin hankali. inda ya koma ya zauna shi da Nuratu suna aika mata tambayar me ya faru.
sai dai shiru bata ce komai ba illah hawayen dake daɗa sakko mata, kuka biyu takeyi, kukan baƙin ciki da farin ciki. abunda Yusuf da matarsa suke yi mata iyaka abunda Ƴaƴan cikinta zasu yi mata kenan.
_su waye su?, aina suka tsintota?, ina ne nan wurin da ta ke sabuwar rayuwa?._ tambayoyin da suke yawo cikin kanta kenan tun daga ranar data farka a asibiti zuwa ranar da suka ɗaukota suka dawo da ita gidansu. so ta ke tasan amsar waɗannan tambayoyin sai dai ba ta da bakin da zata yi magana, haka kuma bata san ta yanda zata gwada musu ba har su fahimceta.
tunawa da wani lokaci yasa ta ɗora hannu a kunnuwanta ta toshe. domin tana jin faruwar abunne kamar a yanzu da ta ke zaune.
*LULLUƁIN BIRI*
*©️Halima h.z*
*11*
"Mommi dan Allah kiyi shiru". Nuratu ta faɗa idanuwanta na kawo ruwa, zuciyarta cike da tsananin tausayin matar.
Yusuf yace,"Mommi hawayenki babban tashin hankali ne a wurinmu, dan Allah ki daina, ko menene kike tunawa zai zama tarihi da izinin Allah...and ina da yaƙinin 100% komai naki ya kusa daidaituwa duk da cewar bamu san me ya faru dake ba har kika zo ƙasar da babu wani naki acikinta, fatanmu Allah ya baki lafiya domin musan ta inda zamu fara".
shima ɗin maganar yake cike da tausayinta.
Mommi ta sake su daga rungumar da tayi musu, tasa hannu zata goge hawayenta Yusuf ya riƙe hannun nata tare da saka handky ɗinsa ya goge mata.
ta sakar musu murmushi, irin murmushin da ake kira na ƙarfin hali, sannan ta jinjina musu kai na ƙara godiya a gare su tare da nuna jin daɗin kasancewarta tare da su.
su biyun suka taimaka mata ta sauko daga kan bed, Yusuf ya fice ita kuma Nuratu tayi mata rakiya zuwa toilet. bata wani jima a wankan ba ta fito dafe da bango.
Nuratu na ajiye mata kayan da zata saka tai saurin bari ta taho tayi mata jagoranci suka ƙaraso ta zauna kan wata kujera.
Nuratu ce tayi mata komai, tun daga kan shafa cream har saka kayan. abaya ce white da adon stones masu ƙyalli. sai hijab ɗin peach ta ɗora mata akai wanda yake daidai ƙirjinta. kasancewar Mommi fara ce sosai sai kayan suka amsheta matuƙa, idan ba wanda ya sani ba sai ka iya rantsewa balarabiyar ƙasar ce dan tayi kama da su sak.
"Mommi ending this week zamu wuce Saudia muyi Umarah for 1 week daga nan sai mu wuce naija, Excellency ya gama gudanar da aikin daya kawo shi, aikinsa zai koma can nigeria gaba ɗaya".
Nuratun ta faɗa tana bata kubza a baki haɗe da black tea, Mommi taunar ta ke yi da ƙyar saboda jin wani nauyi a ƙirjinta kamar an ɗora dutse.
magana Nuratu ke tayi amma hankalin Mommi gaba ɗaya ya bar jikinta, tunaninta ya tafi can wata duniya ta daban, ita ɗaya ta san me ta ke tunani, kuma ita ɗaya tasan me zai iya faruwa. halin da mahaifiyarta ke ciki shi tafi so ta sa ni kamin azo kan kowa da komai.
ta rufe ido kaɗan ta buɗe ta ɗorasu kan Nuratu, sai tayi dauriyar maida ƙwallar data cika idonta sannan ta matso ta sumbaci Nuratu a goshi.
Yusuf na parlo zaune da waya kare a kunnensa yana sauraron maganganun da Umma keyi masa. tsawon lokaci kafin ya numfasa yace,"Umma please don't let Ammi knows munyi waya dake".
daga inda Umma ta ke ta galla harara kamar yana gabanta, tai shiru kamar ba zata ce komai ba, tana shirin yin magana ya rigata.
"please Umma". tayi hanzarin katse shi,"tana part ɗinta ina part ɗina how will she know?, ko da yake aini ce aku sarkin surutu".
yanda yaji muryata yasa shi sosa kai tare da cewan,"ba haka nake nufi ba Umma". dai-dai lokacin Nuratu ta ƙaraso wajen ta zauna saman cinyarsa tare da kwantar da kanta bisa kafaɗarsa, shi kuma ya zira ɗayan hannunsa acikin rigarta yana shafa cikinta, har zuciyarsa ji yake tamkar babynsa yake shafawa a zahiri. Nuratun ma ta ɗora nata hannun akan nasa suna shafa cikin tare.
komai na ubangiji ne, kuma komai lokaci ne, shekararsu biyu da aure Nuratu bata taɓa ɓatan wata ba, maganganu har sun fara tashin ai bata haihuwa, ya kamata ya ƙara aure tun kamin ya mutu baiga ɗansa ba. cikin masu maganganun harda Ammi mahaifiyarsa, da yake dama ita ba ƙaunar auren ta ke ba, kasancewar Nuratu ƴar Yayar kishiyarta ce wato Umma.
lokacin daya gama service ɗinsa ta aika shi har abuja yaje yayi kwanaki a gidan best friend ɗinta Hajiya Habiba don yaga yarinyarta. amma Yusuf na dawowa a lokacin ya tarar da Nuratu da tazo hutu shikenan sai yace shi fa ita yake so, duk