a da cup".
ta amsa da,"to Anty". sannann ta sakko ta koma kitchen ɗin, sai da ƙyar ta iya buɗe friedge ɗin saboda bata san yanda ake buɗe shi ba.
drinks ne kala-kala aciki da ruwa na jarka, ta san dai ruwan amma lemun idan aka cire fanta bata taɓa ganin duk sauran ba musamman five alive na kwali. kawai sai ta ɗauka ƙaramin tray ta saka kowanne guda ɗaya tare da faro guda biyu.
lokacin da ta iso wurinsu Turaki ya sauke hannun rigarsa na dama yana nunawa Bello yanda ciwon wurin yayi, babu wanda yasan da zuwanta wurin balle tsayuwar da tayi tana bin ciwon nasa da kallo ganin yacca yay rami, ita bata taɓa ganin ma irin ciwon da yay haka ba.
cikin kaɗuwar ganin ciwon ta sauke idonta ƙasa kawai tayi tsaye a wurin, tafi ƙarfin minti uku kamin Bello ya ankare da ita yace,"bismillah mana". ya faɗa yana kallonta.
ta ƙaraso ta aje tray ɗin saman table ɗin da ke tsakiya, sannan ta tsuguna ta gaida Bello cike da ladabi shima kuma ya amsa mata da fara'a.
tana durƙushe Zaytuna ta iso itama hannunta ɗauke da bowls guda biyu, duka snacks ne aciki.l ta aje kusa da tray ɗin.
idonta na kallon Bello tace,"Hammah Bello ina kwana". shima nasa na kanta yace,"lafiya lau Zaytun, ya kike ya hutu kuma?".
ta amsa mishi da,"lafiya lau wallahi, ya office?".
ya amsa da,"office babu daɗi, aminina ya gudu ya barni ni ɗaya".
Turaki yace da shi,"sai ka jira Maaman ta dawo tunda ƙorafi ya kawo ka gidan".
Bello yay murmushi bai ce da shi komai ba suka shiga taɓa hira shi da Zaytuna. idon Turaki ya kai kan Fillo dake durƙushe a wurin har yanzu, wani haushi ya kama shi, tunda ake ƴan aiki a gidan nan ba'a taɓa bagidajiyar yarinya irin wannan ba, shi bai san ba ma ko hankali ne bata da shi kwata-kwata.
"ke sai ance ki tashi ki tafi sannan za ki gurgura ƙafafunki ki tafi, ko kuwa kin zauna jin hirar da ba taki ba?".
kanta a ƙasa yake, kuma hankalinta ba'a garesu yake ba dan hirar da suke ma bata ji, banda yanzu da maganar tasa ta shigeta, tasan da ita yake, ba tare da ta ɗago ba tace,"ina jira a bani umarnin tafiya ne".
rai ɓace yace,"kiyi ta zama har a busa ƙaho".
ile kuwa yaga ko motsawa bata yi ba, wani sabon haushi ya turnuƙe shi, duk yanda akai ko aji bata taɓa shiga ba.
Fillo dai cikin ranta faɗi ta ke yi akan me zaisa ta tashi ba'ace taje ba salon ace tayi ba dai-dai ba, bata manta da wani lokaci ba lokacin da suka zauna a masarauta, Fulani ta bada aike a kaiwa Yarima Mansur, ita Kaka ta bawa ta kai, ta sameshi a wanjen shaƙatawa shi da abokinsa, data ajiye musu zata tafi ai cikin tsawa ya maido da ita da cewar uban wa ya bata izinin tafiya, akan haka har kusan horar da ita akayi, to dan dai Kaka na da matsayi ne a wurin Fulani.
to ita kuwa yanzu me zai sa ta kuma maimaitawa, ai jini ba wasa bane, shi da Yarima Mansur duk abu guda ne, balle shi wannan ɗin da ta ke ganin yana da girman izza.
"tashi kije kinji, ki zauna ɗakin baya inda abin buƙata za'a kiraki a waya". Zaytuna ta faɗa tana dubanta.
Fillo ta tashi cikin sanyin jiki ta wuce, Zaytuna ma ta fita daga part ɗin zuwa nasu.
Bello yana kallon Turaki yace,"Beb ɗin da ta tashi tana da hankali, itama ƴar'uwarku ce?".
Turaki yay masa wani kallo,"me yasa baka da hankali ne Bello?".
Bello yace,"tambaya fa nayi".
Turaki yaja dogon tsaki yace,"baka iya bambamce ƴan aiki ne kai, ko kaga tayi kama da Baffa ne ko Maama".
ganin yanda yasha murr Bello yace,"sorry maida wuƙar, ban zaci maid bace saboda surarta na kalla ba kayan jikinta ba".
Turaki ya jefa masa wani banzan kallo,"kana nufin muma a rame muke kamarta?".
"thats is not what i mean, kuma itama ai ba rama bace da ita, halittar jikinta ce a haka".
ba tare da Turaki ya sake kallonsa ba yace,"wataran sai ka rasa idonka akan kallon mutane".
Bello yay dariya sosai, daga haka kuma suka ɗora hirarsu ta abokai tare da ƙara tattaunawa akan batun aikinsa da Maama har yanzu ta dage akan ba zai koma ba.
*Dubai, 12:00am.*
Nuratu ce a ɗakin zaune kan kujera, gefenta tarin drugus ne sai ɓallo su take yi tana zuba su a hannu. ta miƙe ta ƙarasa friedge ta buɗe ta ɗakko ruwa mara sanyi ta buɗe, sannan ta ƙarasa wurin gado ta zauna a gefe.
zuciyarta fal da tausayin matar da suka ɗauko a asobiti suna kulawa da ita, ta kai hannu ta ɗago kan matar daga pillon da take kwance. sai a sannan matar ta buɗe nauyayyun idanuwanta ta zuba su kan Nuratu tare da sakar mata murmushi.
"sannu Mommi". Nuratu tace da ita tana sakar mata nata murmushin. kai kawai ta ɗaga mata alamar yauwa.
matar da suke kira da Mommi ta buɗe baki Nuratu ta zuba mata maganin, sannan ta kurɓi ruwan da shima Nuratu ta bata, ta haɗa ta haɗiye maganin.
lokacin Yusuf ya shigo ɗakin, ya ƙaraso ya zauna akan bedside drower, cike da girmamawa haɗe da ladabi ya gaisheta, yana tambayarta sauƙin jikin. kasancewar bata magana sai da ta amsa musu da kai.
Yusuf yace,"Mommi yanzu ina ke miki ciwo?". ya tambaya da tsantsar kulawa, ta kalle shi ta sakar masa murmushi