su, shi yana ƙyalƙyala dariya ita tana cewa Allah sai ta rama, har sai da ta koma roƙonsa da Allah ya tsaya ta rama.
sai ya tsaya yana haki yace,"to naji za ki rama, amma kar kiyi min da zafi".
"ehh naji a hankali zan maka".
ta faɗa tana jijjiga ƙafa ɗaya.
sai ya sake yin dariya yace,"habawa yarinya ni za ki yiwa wayo".
yana faɗar hakan iska tayi blowing laluben parlon ya rufe masa fuska, kafin ya buɗe tayi tsalle ta dira akansa, ta cukwikwiye shi suka faɗa kan kujera tana ƙwaƙwƙwala masa pilon, sai da ƙyar ya iya kama hannayenta ya riƙe a cikin nasa.
"sai ance kin iya mugunta kice ke ba haka ba".
"ai har sai ka ban haƙuri zan ƙyaleka".
"ni fa ba zan bawa ƴar ƙaramar yarinya haƙuri ba".
suka shiga kokayawa har sai da tayi nasarar gantsara masa cizo a kunne, zafin cizon ya ratsa shi ya ƙwala ƙara yana faɗi,"i am sorry".
ta ƙara kai masa cizo a hanci tana cewa,"ba haka ba, sai kace don Allah".
ai kuwa ya ƙwalla ƙara da ƙarfi yace,"Don Allah kiyi haƙuri Fulani Nah, haba Fulanin Turaki ƴar albarka".
"waye yay nasara?".
"kece Anty Fulani".
ta ɗaga shi tana dariya sai haki take yi, tana tafa hannu tana cewa,"yau na zama Anty Fulani".
sai kuma ta faɗa saman ƙirjinsa ta tura hannu cikin rigarsa tana yawo da shi akan ƙirjinsa.
cikin muryarta mai sanyi da ratsa dukkan jijiyoyin jiki tace,"Jannaty idan muna wasa karka ƙara ɓace min irin haka, tsoro yana kama ni, bana so in ji bana tare da kai".
ta faɗa tana kifa kyawawan idanuwanta cikin nasa, idanun da suke ɗauke da guntun ruwan hawayen kukan da tayi.
"ba zan ƙara ba insha'Allahu Fulani nah, am sorry kin ji, i will always be with you".
sai ya rumtse idonsa yana tunawa da kyakykyawan murmushin da ta sakar masa a lokacin, ya tuna yacca ta shigar da jikinta jikinsa ta ƙanƙame shi tare da faɗa masa kalmomin da a duniyarsa yafi so yaji sun fito daga bakinta.
"i love you Jannaty, ina yi maka son da har bar san irinsa ba Jannaty, Allah ya barmu tare har abada".
lokaci ɗaya yaji idanunsa sun cika da ruwa, ya dafe saitin zuciyarsa da yaji tana yi masa zafi.
ya tuna bayan rasuwar Fulani sai da yay watanni kafin ya dawo cikin hankalinsa, hatta deppression sai da ya kama shi, ban da ma Allah yasa ta bar masa yaran nan da tuni zuciyarsa ta buga shima ya mutu.
a hankali ya furta,"I have missed you, I am always missing you Fulani Nah, i am missing you like crazy".
Muryarsa ta fito kamar zai fashe da kuka, duk da cewar hawaye tuni sun sauka saman kuncinsa masu zafi.
muryar yaransa da ya jiyo su na nufowa ɗakinsa yasa yay saurin saka handky ya goge hawayen.
suka shigo ɗakin su na zama kan kujera, ya juyo yana kallon su, yaji wani sanyi ya ratsa ƙasan zuciyarsa, a yanzu kaf duniya baya tunanin akwai wani abu da yake ƙauna sama da yaransa, sama da su biyun nan, babu shi.
ya taka ya ƙarasa ya zauna a tsakiyar su, yaran suka sarƙafo da hannayensu ta wuyansa. "good morning Abie".
sai Maama ta miƙe ta tsaya a gaban su.
"this way! good morning Mr Sir".
ta kwatanta gaisuwar a irin yanda suka taɓa ganin wani vedion Fillo da Turaki ya nuna musu, lokacin su na honeymoon a Ausburg, hakan yasa suka ƙyalƙyale da dariya dukansu, har sai da Turaki yaji damuwar dake ƙasan ransa na bin iska.
lokaci ɗaya dariyar ta su ta mutu a san da suka jiyo sautin muryar Fillo ya karaɗe cikin ɗakin, ta cikin audio record ɗin da ta taɓa yi tana karatun alƙur'ani.
Maama tasa hannu a laptop ɗin ta kashe, ta juyo tana kallon mahaifinta da ya tusa hannunsa cikin sumar kansa, Ayan kuma na hawaye, sai kawai ita ma hawayen ya sakko mata, ta kifa kanta akan laptop ɗin da hoton Fillo ya bayyana akan screen ɗin.
muryarta ta fito gwanin ban tausayi da cewa,"Allah ya jiƙanki Ummina".
Ayan ma yace,"Allah ya gafarta miki Ummi".
Turaki yace,"Allah yasa kina aljannah Halima".
ya faɗi sunan nata da zai ce karo na biyu kenan da ya taɓa kiranta da shi.
"Abie when zamu je taraba mu gaisar da Granny?".
Ayan ya tambaya yana kallon mahaifin nasa.
"yaushe hutun ku zai ƙare?".
Maama tayi karaf ta ce,"2weeks reamaning".
ya sauke numfashi kafin yace,"ku haɗa kayan ku sai mu wuce in Allah ya kaimu gobe".
"photocopy of me".
Turaki ya jiyo sautin muryar Maama na faɗin hakan, ya ɗaga kansa yana kallonta, ta kafa hoton Fillo a gaba tana kallo.
"Abie ka taso muyi break fast". cewar Ayan da ke tsaye bakin ƙofa.
"takeaway zamu yo ko mu tafi wurin Mum? tunda Anty bata nan".
Maama tayi saurin tashi tana cewa,"Abie mun dafa ni da Ayan, tun saven o'clock muka gama, mun dafa maka favorite naka kunun shinkafa da ƙosan bread".
da sauri Turaki ya miƙe cikin tsananin farin ciki, yana ta sakawa yaran nasa albarka, daga bisani suka fita cikin farin ciki zuwa downstairs domin yin breakfast.
_Sauran rayuwar Turaki da Yaransa, Da rayuwar Amir, da Rayuwar Fulani Azima duka na barwa tunanin ku._
*THE END*
*Alhamdulillah!Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!*
_*A y