n wannan zafin zuciyar taka, idan ƙanwarka bata taɓa abinka ba na wa kake so ta taɓa?".
Ayan na faman huci yace,"to Abie ita ce komai ta ɗaukar min sai ta lalata, kalla fa yanda ta fasa min sabon bluetooth ɗina, kuma shekaranjiya da Uncle Bello yazo ya ban shi".
yay maganar yana nunawa Turaki.
"kuma shi ne saboda rashin tunanin akan abun duniya zaka ɗaga hannu kace zaka mareta?, ranar da bana raye a haka zaka kula da ita?".
Ayan yay shiru bai ce komai ba, ya kumbura yayi fam yana tunanin abin da zai yiwa Maama ya huce.
"garin ya kika fasa masa abun sa?".
"Abie ba na sane Allah, nazo sakkowa daga upstairs na zame shi ne ya faɗi daga kunnena".
Turaki ya jefawa Ayan key ɗin motarsa yace,"ka je mota ka ɗauko nawa".
yana rufe baki Maama ta ce,"Abie ni fa?, Farha ta karɓi nawa kuma ba zan iya cewa ta ba ni ba".
"ki bari zan siyo miki wani Maama".
washe gari da safe wajen ƙarfe takwas hayaniyar yaran nasa ta tashe shi daga bacci, ya tashi ya shiga toilet yay wanka, bayan ya fito yazo ya tsaya jikin window yana hango su.
a field suke su na buga basket ball, Ayan na ta yawo da ball ɗin yana dariya, ita ma Maama na ta yawo wajen ganin ta kare ball ɗin daga shiga cikin raga, sai dariya take yi tana cije leɓenta, motsi kaɗan sai ta gyara zaman glass ta karyar da wuya alamun ta fara gajiya.
duhun garin kuma ya fara hanata gani sosai duk da medical glass ɗin da ke sanye a idon nata.
ta durƙusa tana nishi, Ayan ya jefa mata ball ɗin ta ƙwalu a saman kanta, ya kwasa da gudu yana faɗin,"idan kin isa ki biyo ni ki rama ƴar makauniya".
haka yake yi mata sau tari, sai su na waje su na wasa sai ya tsokane ta ya gudu in dai yasan akwai hadari.
zafin ƙwala ball ɗin yasa Maama miƙewa ta ɗauka ball ɗin, ta ƙanƙance ido ta cikin glasses ɗin sannan ta saita Ayan da ya juyo yana yi mata gwalo, ta ɗaga ball ɗin ta jefa masa, ai ko cikin sa'a sai ga ball ɗin a fuskarsa, ta buga tsalle tare da ihu tana faɗin,"wooo ai dai na rama".
shi kuma ya dafe goshi yana faɗin,"yasin sai na faɗawa Abie ciwon idon ƙarya kike yi, ya daina asarar kuɗinsa a siyan glass kina gani tarr".
lokacin kuma hadari ya ƙara ɗinkewa, lokaci ɗaya garin yay baƙiƙƙirin, sai ya zamto Maama bata iya ganin komai hatta da gabanta, hankalinta ya tashi ta ɗaga hannu ta shiga laluben gabanta tana kiran Ayan.
"Ayan please ka zo, kar ruwan ya sauko, bana gani fa".
tana rufe bakinta taji ana yi mata cakulkuli ta baya, tai saurin juyowa don kama shi, sai dariyarsa ta jiyo yana ƙara yi mata cakulkuli ta bayanta da ya ƙara zagayawa.
"yarinyar ki bar min agogon da Ummi ta bar miki sai in taimaka in yi miki jagora".
"to ai tace nawa ne ni ɗaya".
"to shikenan sai ki taho da kanki".
taji yayi shiru babu motsinsa, taita ƙwala masa kira yana gefenta a tsaye yay mata shiru, sai kawai ta fashe da kuka tana ta ƙwala masa kira.
Turaki dake hango su yana murmushi, ya faɗa tunanin wani moment na su shi da Fillo.
kamar haka su na tare a field ɗin su na yin wasan ƴar burin burin, ya ɓace mata tana ta kiran sunansa yay shiru yaƙi amsawa, kuma a sanda ta kunce ɗaurin idon taga bata gansa ba sai ta saka kuka.
kamar dai yanda Maama ke yi a yanzu, sai ya tuna yacca ya dinƙa jin sautin kukan nata na dukan zuciyarsa a lokacin, amma duk da haka bai fito daga ɓoye mata ɗin da yay ba sai da ta shiga parlo.
ta hau upstairs ta gama lalubensa a can baya nan sai ta dawo ƙasa, shi kuma a lokacin ya shigo parlon, su na haɗa ido da ita ya kwashe da dariya sosai ganin yacca hawaye duk ya ɓata mata fuska.
kuma ganin nasa yasa ta ɗauki pillon kujera ta biyo shi, suka shiga zagayen kujerun parlon tana faɗin,"Allah ni ka tsaya in ƙwala maka".
ya tsaya daga bayan babbar kujera yana haki yace,"saboda me to?, wannan ai mugunta ce, kawai sai ki kama ƙwala min pillow bayan kin san da zafi".
"ni dai sai na ƙwala maka".
ta faɗa tana turo bakinta gaba cikin shagwaɓa, tare da dukan ƙafafu a ƙasa hawaye na sakkowa ta ido ɗaya.
sai ya kama ƙugunsa yana kwaikwayon yacca take yi da idanu, hakan ya daɗa tuzurata ta sa kukan shagwaɓa sosai.
cikin dabara ta dinƙa matsawa zata zagaya ta bayan kujerar da yake tsaye, fahimtar hakan yasa shi barin wajen da gudu dariyarsa na ƙaruwa sosai.
"to wai me nayi miki za ki ƙwala min abu?".
ta ɗage gira duka biyu ta ce,"ba kai ba ne ka gudu ka barni ka saka ina ta nemanka ban ganka ba".
"to sai ki bari naki turn ɗin yazo sai ki rama, amma ni dai ba za ki ƙwala min wannan pilon me zafi ba".
"ni dai Allah sai na ƙwala maka ko kuma ka ban haƙuri".
"tabɗijam sannu sara me baƙar takashi, kawai sai in kama ba ki haƙuri kina ƴar ƙarama da ke, bayan in da nayi haihuwar ƙauye da nayi jika da ke".
abin da ya faɗa yasa ta cije leɓe tana tunanin abun da zata yi masa, bata ankara ba taji ya ƙwalo mata pillow a saman ka.
ai kuwa sai ta ƙara fyallawa da gudu zata kamo shi, suka ci gaba da zagaye parlon cikin guje gujen