NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 32 of 323

an. zata faɗa ko aina ne he is very simple Man, abu biyu ne kawai a duniya masu rikiɗar da shi, su saka ya fusata har ya aikata wani mummunan abun ba'a cikin hayyacinsa ba. sai dai mamakin da ta ke taya Fillo ta fama masa ciwon dake zuciyarsa, ko kuma garin ya ta taɓa abunda zai iya aikata kisan kai akansa?. tana kallon Fillo tace,"me kika yi masa?". tana girgiza kanta tace,"ni ban masa komai ba. abinci yace sai na cinye kuma ni na ƙoshi". "an kira shi a waya ne?". "ni ban sa ni ba". Zaytuna tayi shiru, dole cikin biyun abunda ke haddasa masa ƙunci zuci ya faru. tasan ko menene baida alaƙa da mahaifiyarsu tunda Fillo bata san komai ba akai, amma duk yanda akai bisa kuskure ta taɓa Maama, shi kuma ɓangaren da baya ɗauka kenan. idon Fillo na kan Turaki, tsab zata iya lissafa adadin jijiyoyin da suka fito raɗau ajikinsa, tun daga kansa har hannayensa da wuyansa. fahimtar da tayi masa mutum ne shi da ba'a sanya mahaifiyarsa acikin kowanne lamari saboda muhimmancinta. kuma ita sai a yanzu take ganin rashin kyautarwarta, bai kamata dan yace taci ƙazantarta ba ta buɗi baki tace ai Hajiyarsa ce ta dafa, kenan jagwalgwalon ba nata bane na uwarsa ne, matsayinsa na wanda tasan ya bata shekaru da yawa bai kamaci irin wannan maganar daga gareta ba. ko babu wannan ma yaci ace ta darajarta shi duk da jin kai da ta fahimci yana da shi, tunda ita da Kakarta a ƙarƙashinsu suke rayuwa sama da shekaru biyar, ba'a taɓa haɗasu da mara kyau sunci ba matsayin su na ƴan aiki, haka kuma ba'a basu makwanci mara kyau ba. idan ba zata manta ba me gidan da kansa na shiga ɓangarensu ya gaida tsofaffi, Hajiya Madina ce ma bata taɓa gani amma ta taɓa ji ance ta shiga sau ɗaya. kawai sai tayi ƙasa da idonta tana jan yatsun hannunta, maganar Kaka na dawowa cikin kunnenta na wani lokaci can baya da ta taɓa faɗa mata. "Halima dan Allah ki rage jin kai domin ke ba ɗiyar kowa bace, ki rage zafin zuciya, ki zama me haƙuri, ki zama mai sadda kai ga wanda duk kika san ya shiga ɓacin rai ta sanadiyarki, karki ce ba za ki bada haƙuri ba domin tsugunawa wada ba gajiyawa bane, ka zama me haƙuri ma da iya bada haƙuri wani babban arziƙi ne gare ka...bada haƙuri babu abinda zai rageki da shi sai dai ma ya ƙareki da abubuwa da dama...zai iya sawa aga mutumcinki, zai iya zama silar ɗaga darajarki". Fillo ta rufe ido ta haɗiye wani busashshen yawu, a hankali ta shiga sauke gwiwoyinta har ta kaisu kan ƙasan tiles ɗin. muryarta ta fito da amon rashin jin daɗi tace,"dan Allah kayi haƙuri". hannunsa na cikin na Zaytuna ya damƙe da kyau, ya waigo yana mata wani irin kallo kamin yace,"cinye abincin nan shine zai wanke ki". itama sai ta ɗago ido ta kalle shi,"to idan na cinye zaka haƙura?". "kurma ce ke da ba kiji me nace ba". faɗin hakan yasa ta miƙe ta zauna kan kujerar, har yanzu hannunta bai bar rawa ba ta ɗauki spoon ta fara tura abincin bisa dole. kuma har lokacin suna tsaye shida Zaytuna idanunsu duk akanta, daga yanda ta ke ci yasan cin dole kawai takeyi, sai dai shi babu ruwansa ko zata amayar sai ta cinye. sai da tacinye tass tukunna ta ɗago da kanta ta kalle shi idonta na zubar da hawaye, yay saurin rumtse idonsa yana kauda kai gefe, idan da abinda baya son gani a rayuwarsa shine hawayen mace. yana jin zata miƙe ba tare daya kalleta ba yace,"wa zai shanye miki tea ɗin?". jin hakan yasa tasa hannu ta ƙara goge wani hawayen, sannan ta kalli Zaytuna tace,"Anty na ƙoshi idan na kuma cin wani abu amai zanyi". Zaytuna tace da shi,"Hammah ai mata afuwa". ya wurgawa Zaytuna wani kallo sannan yace da Fillo,"kin zuba kinsha ko sai na barki da Allah akan zagar min Uwata da kika yi". tai saurin girgiza masa kai. yace,"to zuba rabin kofi ki shanye". tana zuba tea ɗin tana hawaye haka ma har ta shanye bata bar kuka ba. sai a sannan yay ƙasa da murya yace,"aikin da aka kawoki shi kawai za ki dinga yi, duk ranar da kika ƙara gigin saka hannu a abinda zanci sai kin cinye shi ta hanci". yana faɗar hakan ya bar wurin, yana fiddo waya daga aljihunsa yay picking call ɗin Bello Ƙaraye dake shigowa. a bakin ƙofar parlo ya tsaya yana cewa,"bana part ɗina ina part ɗin Maama". da faɗin hakan ya katse wayar ya maida aljihu sannan ya nufi kujera ya zauna. Zaytuna ta wuce upstairs bayan tace da Fillo idan baƙo ya shigo ta kai masa ruwa da lemu. ta amsa da tou, sannan ta miƙe ta kwashe kwanukan abincin da aka tursasa mata ci ta kai su kitchen, ta dawo ta gyara wurin ta goge ya zama fess sai ƙyalli glass ɗin yake. a kitchen ma kusan duk wani abu da ake cin abinci acikinsa sai da ta fito da shi ta wanke, wannan koyarwa Kaka ce gareta, kwanukansu kullum sai sun wanke su ba iyaka wanda suka ci abinci ba kaɗai. a hankali ta ke yin komai gudun kar ta fasa wani abun tunda komai tangaran ne. bayan ta gama gyara kitchen ɗin ta fito ta hau upstairs ta tambayi Zaytuna aina zata ɗauki lemun. Zaytuna tace,"ki buɗe friedge za ki gansu aciki, amma karki manta ki haɗ
🏠