NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 319 of 323

ƙarfin ko kaɗan, hatta ruƙon da yaron yay masa ji yake kamar an jona masa electricity. zuwan police wajen suka ƙwace Ayan da ga kan Amir wanda yake ƙoƙarin kaiwa ƙasa. banda haki babu abin da Ayan ke yi, idonsa yay jawur kamar bana ƙaramin yaro ba, police suka kama hannun Amir suka saka masa ankwa, sai a yanzu idonsa ya kai kan Turaki, yaji gabansa yay mugun faɗuwa, ya wurga ido ya ƙara kallon Ayan, jini ba banza ba, don lokaci guda ya tuna da mugun dukan da ya sha lokacin da suka yi kidnapping Fillo. don haka tsananin tsoro ya kama shi, ya tabbatar yanzu idan Turaki ya gane waye shi to sai dai waninsa, dan haka gwara yabi ƴan sandan, duk runtsi zai fito ya sani. police su ka kama Amir suka saka shi a mota suka tafi. bayan su Turaki sun dawo daga dubiyar Fulani Azima, direct gidan ya wuce da yaransa, in da anan suke cin abincin dare duk friday. ana jin tsayuwar motarsu Boɗejo tace,"to ga kajin nan sun iso". Mum na zaune kan kujera, da jaririyar Nihal a hannunta ta gama yi mata wankan yamma, tayi murmushi da jin furucin Boɗejon. Turaki ya shigo tare da yaransa, waɗanda sai da suka fara zuwa ɓangaren Baffa suka gaida shi. jikokin gidan duk suka yi wajensa su na yi masa sannu da zuwa, ya ɗauki ƴar gidan Zaytuna me suna Aisha. Maama tayi jikin Boɗejo tana cewa,"nayi kewar tsohuwa". Boɗejo tace,"kinga ni kuwa yau ba wanda nayi kewa a cikinku, ko babu komai bakina da na Kakarku luff babu rabon faɗa". "ai kuwa tun da kika faɗi haka ba zan ba ki abin da na taho da shi ba". Boɗejo da a yanzu ta ƙara zama tsohuwa tukuff ta janyo Maama jikinta tana faɗin,"haba ƙawata ƴar mutunci yi haƙuri, ai yanda bana iya fita inci ni ɗaya ban rage miki ba haka kema na sa ni". Maama ta dubi Turaki da ya zauna akan kujera su na gaisawa da Mum, tace,"Abie ka ɗauko min leda ta?". ya kalli gefensa yay mata nuni da ledar, sannan ta miƙe taje ta ɗauko, tazo ta zauna ta buɗe ta ɗauko dublan ɗin ciki tana bawa Boɗejo, wacca ke tambayar aina suka siyo shi, ita kuma tana bata labarin yacca ta kwaso shi a ɗakin Inna Wuro. da daddare bayan sun gama cin abincin dare, suka fara haramar tafiya gida. Mum ta juye musu sauran teba da miyar gandar da akayi a flask tace su tafarwa da Ilham. ko da suka koma gida Turaki ajiye su yay ya ƙara fita, ya tafi siyo magungunan da likita ya rubutawa Ilham, wacca likitoci suka yi iyaka bincikensu akan rashin haihuwarta, suka tabbatar da cewa da wuya idan ta haihu sai in kuma wani iko na ubangiji. tana zaune a parlo tana kallo su Ayan suka shiga, tayi musu kallo ɗaya ta ɗauke kanta taci gaba da kallon film ɗin da ake yi a mbc action. ganin bata kula su ba Ayan yace,"Anty daga wurin Maminki mu ke". furucin nata yasa ta mayar da hankalinta gare shi tana jin cewarsa. "ya ku ka ƙara samun yanayin jikin nata?". Ayan yace,"ba sauƙi, sai tsanani da ya ƙara. yau da muka je jini yana ta zuba ta duburarta, sai botiki aka tara mata ma a wajen, ta ƙara motsewa babu kyan gani". Ilham ta saka kuka sosai tana kifa kanta akan ƙafafunta, tsawon minti biyar tana kuka kafin ta ɗago tare da ɗaukar wayarta ta shiga kiran lambar Turaki, sau kusan sau biyar kiran yaƙi shiga, ana ta faɗa mata not recherble. ta kalli agogo taga ƙarfe tara da rabi a lokacin, ta miƙe ta wuce ɗaki, ba jimawa sai gata ta sakko sanye da hijab. ta kalli yaran tace,"idan Babanku ya dawo kuce masa na tafi wurin Mami. ku faɗa masa ina ta kiran wayarsa taƙi shiga". su ka amsa mata,"to, a dawo lafiya". "Allah yasa". ta faɗa tana nufar ƙofar fita, maganar Maama ta dakatar da ita,"Anty ko za ki tafi da tebar?". ta kalleta tace,"Mum ce tayi?". "ehh". "Maama ba zan iya ci ba, ku cinye idan kuna so. akwai pancake a kitchen na ajiye muku, ba kwa buƙatar wani abu?". suka haɗa baki wajen faɗin,"ba ma buƙatar komai Anty". ta kalli Ayan tace,"saura ka sakata kuka". yay ƴar dariya yace,"Anty wai haka kawai nake sakata kukan?, sai fa tayi min ba daidai ba". tayi murmushin ƙarfin hali kawai ta fice ba tare da ta ƙara ce musu komai ba. sai wajen goma Turaki ya dawo gida, yana shigowa parlo ya tarar da Ayan akan Maama yana zazzaga mata masifa. "dilla Malama bani abu na, na rantse da Allah daga yau ma kika ƙara taɓa min kaya sai na faffasa miki baki, kin dai ji na faɗa miki". ya faɗa yana sakin ƙwafa me ƙarfi, sai kuma ya saka hannu ya dungure mata kai glass ɗin idonta ya faɗi, a rikice ta durƙusa tana neman glass ɗin. ta lalubo shi da ƙyar ta saka, ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tana hura hanci tace,"kuma wallahi idan Abi ya dawo sai na faɗa masa". tana ƙoƙarin raɓawa ta gefensa ta wuce, ya fincikota yana faɗin,"ɗauko min kayana ki bani". ta fizge tana faɗin,"ba zan ɗauko ba ɗin". a zuciye Ayan ya ɗaga hannu zai mareta muryar Turaki ta dakatar da shi. "Ayan!". ya kira sunansa da ƙarfin sauti wanda hakan yasa Ayan ɗin nutsuwa. "me ta taɓa maka da ma?, kai da baka da haƙuri, na faɗa maka bana so
🏠