n ta buɗe mota ta fita. "na gode Abie".
ƴar tafiya kaɗan tayi daga inda motar tasu ta tsaya, ta tsuguna agaban almajirin ta saka masa kuɗin acikin robarsa tare da faɗin,"Baba kayi adu'a Allah ya kai ladan ƙabarin mahaifiyata".
tsohon ya shiga kwaranyo mata adu'a iya adu'a, daga mahaifiyartata har ita kanta da sauran ahalinta. ta ɗaga glass ɗinta tasa tissue ta goge hawayen da ya cika mata ido, kafin ta yunƙura ta miƙe jiki a sanyaye ta bar wajen nasa.
tana cikin tafiya tayi karo da mutum, ba wai don bata ganin gabanta ba, sai don hankalinta da ya bar jikinta a lokacin.
ta sunkuya ta lalubo gilashinta ta saka, sannan ta kalli mutumin da ta tsorata da ganin nasa, tayi saurin matsawa gefe tana ce masa,"kayi haƙuri don Allah".
muryartata ƴar ƙarama kuma ƴar siririya me zaƙi ta fito ta shiga kunnen Amir ta ratsa jikinsa, ya kasa ƙifta idonsa akanta, kallon mamaki kawai yake yiwa yarinyar gabansa, wacca gaba ɗaya yasan bata kai shekara sha bakwai ba.
abun da ya sani shi ne ya san wannan halittar, sai dai bai yi tsammanin zai sake ganinta a haka ba duba da tsawon shekarun da aka ɗauka, ya sani Fillo na da ƙaramin jikin da ba lallai shekarunta masu yawa su nuna a jikinta ba. to amma duk da haka abin da matuƙar mamaki ace ita ce a gabansa haka, babu wani alamar girma a tare da ita, after all shekaru goma sha bakwai ɗin da ya ɗauko bai ganta ba.
jikin Maama na rawa ta daɗa ce masa,"zan wuce".
Amir yay ajiyar zuciya bayan ƙare mata kallon tsab da yayi, tabbas wannan ba asalin Fillon da ya sani ba ce, wannan me kama da ita ce sak babu wani banbanci, sai dai in ace banbancin halayya, me hakan ke nufi kenan?, wata ce photocopy of her ko kuma ƴarta ce?.
lokaci ɗaga matacciyar zuciyarsa da babu tsoron Allah acikinta taji ta kwaɗaitu da yarinyar, yaji sha'awarta ta ratsa duk wani ɓargo na jikinsa, take kuma ya fara tunanin ta yacca za'ai ya shiga rayuwarta a irin matsayin da ya saba shiga rayuwar sauran ƴan mata?, ya shiga rayuwarta kamar dai yanda ya shiga rayuwar me kama da ita.
_(hmm Allah ya kyauta, ya kuma kiyashe mu daga sharrin zuciya, dama haka abun yake, ance wasu ko zasu je lahira su dawo halinsu ba zai taɓa canjawa ba, sai dai muyi adu'ar Allah ya tsare daga sharrin mugwayen mutane.)_
sai ya sauke idonsa akansa yana kallon jikinsa, wannan sam ba wancan Amir ɗin ba ne me ji da tashen ado da ƙwalisa a zamanin baya, wannan wani Amir ɗin ne na daban, wanda halittarsa ta sauya tun yana cikin prison, ya dafe ya zama mugun baƙi, yay wata muguwar rama kamar me cutar S, ya haɗa uwar ƙasumba a fuska kamar dodo, haka kansa ma ya tara uban gashi kamar mahaukaci, duk yayi duƙunduƙun kayan jikinsa duk a yayyage, ga uban ɗoyi da ke tashi a jikinsa kana ji kasan kwanan bola yake yi.
warin jikin nasa ya doki hancin Maama, take ta duƙa a ƙasa saboda aman da ya taho mata, ta shiga kyalaya amai kamar hanjin cikinta zasu fito.
Amir ya duƙa a gaban nata shi ma, zuciyarsa na harbawa kaɗan kaɗan, abu ɗaya yake tunani wanda yake jin har in ya rasa zai iya shiga wani hali, halin da yafi wanda yake ciki muni, muddin bai samu ya kusantu da yarinyar ba zai iya rasa lafiyar jikinsa.
don haka zuciyarsa na ingiza shi ya kai hannu zai taɓa Maama tayi saurin miƙewa tana ja da baya.
"mene haka?, na fa baka haƙuri".
ya miƙe yana lashe leɓe, a hankali yace,"Ki tsaya na taɓa jikinki don Allah ko ya ya ne, idan na taɓa zan haƙura na barki ki tafi".
Maama ta shiga girgiza masa kai tana ja da baya, yanzu kam ya gama tabbatarwa ba Fillon da ya sani bace, kuma ko da ace ita ɗin ce ma ba zata taɓa gane shi ba, don kwatakwata ya fita a Amir ɗin da mutane suka sansa, shiyasa har yanzu ma Ƴan sanda suka kasa kama shi bayan wani laifin da ya ƙara aikatawa lokacin da ya fito a prison.
"sau ɗaya yarinya, sau ɗaya kawai za ki barni in taɓa ƙirjinki, ki tausaya min wallahi a bola nake kwana".
yayi maganar da kana ji kasan ƙwaƙwalwarsa ta fara taɓuwa, lokaci kaɗan ya rage ya fara hauka tuburan.
san da Maama ta kai ƙarshe ajikin wani ƙarfe, lokacin Ayan da Turaki suka iso waje, tana ganinsu ta ƙwala kiran Abie, Ayan yasa hannu ya juyo da Amir, da yake irin tsayin mahaifinsa yayo sai ya zamana tsayinsa yay daidai da na Amir ɗin.
cikin zafin nama Ayan yasa hannu ya wanke fuskar Amir da zazzafan mari, ya damƙi ƙwalarsa yana jijjiga shi har sai da ya kai Amir jikin ƙarfen da ke bayansu ya buga kansa a jiki.
"kai ba mahaukaci ba ne zuciyata ta faɗa min hakan, ubangiji yayi min baiwar gane mutane a kowanne hali suke ciki. sai na kasheka tun da ka yi yunƙurin taɓa min ƙanwata".
ya faɗa yana ta buga kan Amir ajikin ƙarfen, Turaki kuwa na gefe rungume da ƴarsa a jiki zuciyarsa sai zafi take yi masa, idan har yace zai kai hannu ya taɓa Amir to bai san me zai ya faruwa ba, don wataƙila kafin ƴan sanda su iso wajen ya kashe shi.
ɓangaren Amir kuwa abu guda ɗaya ya sani, ba zai taɓa iya ƙwatar kansa ba a hannun Ayan, bai da wannan