NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 317 of 323

amu je wurin sarkin ɗori da Aliyu ne". "Allah ya sauƙe". "to amin Zainabu, na gode. amma ke ma dai sai kin rinƙa kulawa, in ba haka ba wataran tsaf zata jeho ki daga saman bene, tun naga aljanunta masu wurgi ne". zata fita a ɗakin Maama ta buɗe baki, cikin ƴar ƙaramar muryarta tace,"a dawo lafiya Inna, Allah ya bada lafiya". "amin in ma ba har zuci kika faɗa ba. ƴar banza da wofi me suffar ƴaƴan aljanu, kina fama da ƙaramar murya sai kace kukan mage, Allah ɗaya ma yasan manufar da yasa yayo ki a makauniya, sanyin tafiyar da aka ba ki ai ba'a banza ba, idan kin cuceni kin tsira kika cuci wani kafin kiyi taku biyu ai ya danƙo ki yaci ubanki. Allah dai ya jiƙan Uwarki ya gafarta mata, amma wannan halin dai ba nata ba ne sam". ta fita tana ta zazzaga masifa, Maama da Farha kuwa sai dariya suke yi, bayan fitarta sai ga Ayan ya shigo, ya zauna kan kujera, bayan sun gaisa da Ammi take ce masa,"ni ai fushi nake da kai, yaushe rabon da kazo ka gaida ni?". yana murmushinsa me kyau yace,"Ammi tare da Abie muke zuwa office shiyasa, kuma yau ɗin mun makara wajen zuwa gun Ummi ne shiyasa ban shigo ba a lokacin". sai ya kalli Maama yace,"ki taso mu tafi". Ammi tace,"da wuri haka?, ba zai bar min ku sai dare ba?". "Ammi zamu je dubo Maman su Antynmu ne". Ammi tace,"Allah sarki wannan mata dai tana shan wuya, Allah ya kawo mata sauƙi". "amin". Ammi ta rako su har bakin gate, Farha kuwa sai da ta raka su har bakin motarsu, har sai da suka gaisa da Turaki sannan ta juya ta koma gida, su na yiwa juna bye bye ita da Maama. "Abie kun gaisar min da Ummin?". Maama ta tambayi mahaifin nata a lokacin da motar su ke hawa kan titi. Turaki ya dubeta ta cikin mirror yace,"mun faɗa mata Maama". sai kuma yace,"Maama ko dai muje asibiti?". ta bar abinda take yi ta kai dubanta gare shi tace,"saboda me Abie?". yay ɗan jim kafin yace,"ina ga kamar ayi miki aiki a maƙogoronki, Maama muryarki tayi ƙanƙanta da yawa, wanda ya saba da ke ne fa kaɗai yake iya jin me kike cewa farat ɗaya". tayi knodding kanta tare da cewa,"Abie idan hakan yana damunka ayi min duk abin da kake so". ya numfasa kafin yace,"ba komai zamu ci gaba da zuwa gaban ka'aba muna roƙon Allah". tafiyar tasu tayi nisa acikin motar, yayin da suke hira jefi jefi, har sanda Turaki ya tambaye su,"ina da ina zan kai ku?". da yake duk friday haka yake kai su gidan ƴan uwa da abokan arziƙi ziyara, ko kuma wani lokacin su yini shi da Ayan a maƙabarta wajen Fillo da Maama, sai in yamma yayi yaje gidan su Yusuf wajen Ammi ya ɗauko Maama da suke sauketa acan tun safe. Ayan yace,"Abie muje gidan Anty Maijidda, kwana biyu bamu je ba, kuma last zuwa da muka yi mun barota bata da lafiya". Turaki ya amsa masa da to, sai da suka fara tsayawa a hanya suka yiwa ƴaƴan Maijidda siyayya kafin suka ɗauki hanyar gidanta. Turaki ya ba su kuɗi masu yawa su kaiwa Maijidda kamar yanda ya saba duk sanda ya kawo su. sai da yaran suka shafe kusan rabin awa kafin su fito tare da Maijidda wacca ta rako su. hangota yasa Turaki fitowa daga mota, ya ƙarasa ƙofar gidan suka shiga gaisawa da ita, tana ta yi masa godiya akan irin aiken da yake bayarwa akawo mata ita da yara. Maama na kama hannunsa ta riƙe yake tambayar Maijidda yaranta, ganin yau bai ga ko muutum guda ya rako su Ayan ba, da kuma ɗan ƙaramin ɗanta da ya zama kamar abokinsa, kasancewarsa irin yaran nanne masu saurin sabo. Maijidda tace,"wallahi kaga wata tahfeez aka buɗe a bayan layin nan, shine aka kaisu can". "har friday suke zuwa kenan?". Turaki ya tambaya. tace,"ehh juma'a zuwa lahadi, tun safe sai yamma". "masha'Allahu, Allah ya bada ilimi me albarka". ta amsa da,"amin amin". "to bari mu wuce, a gaida min da abokina". tayi ƴar dariya tana faɗin,"Musaddiq sarkin magana, zai ji insha'Allahu, da sun samu hutu ai zan kawo muku su, sai su yini". sai ta saka hannu tana share ƙwallar fuskarta tace,"Allah ya jiƙan Fillo". Turaki da Ƴaƴansa jiki a sanyaye suka amsa da,"amin ya Rahman". tukunna suka yi mata sallama suka wuce, inda suka ɗauki hanyar gidan Me Martaba domin zuwa duba Fulani Azima, wacca har yanzu ta nan kwance rai a hannun Allah, gaba ɗaya halittarta ta sauya ta koma tamkar ta ƙadangare, sai ka rantse da Allah ba mutum ba ce tun asali, wasu gashi sun tsatstsafo mata a jiki, idanunta sun yo waje ƙwayar kamar zata faɗo ƙasa, bakin da hancin sun shafe a waje ɗaya, kai abun dai babu kyan gani da kwatance. ga duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata ya zubar mata da hawaye idan bai san abun da ta shuka ba, wanda kuwa yasan me ta aikata muddin ya ganta sai jikinsa ya mutu gaba ɗaga, tsoron Allah ya ƙara shigarka, kaji gaba ɗaya duniyar ta fita a ranka, balle kuma kaji kana son sha'awa ko mallakar abun da ke cikinta. Maama da ke kallon bakin titi tace da Turaki,"Abie don Allah zan bayar da sadaƙa". Turaki yay parking a gefen hanya, ya zaro ɗari biyar a aljihunsa ya miƙa mata ta karɓa sanna
🏠