NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 316 of 323

a tura ni a keken guragu". tayi shiru tana girgiza kai alamun takaici ya isheta."sam yarinyar nan bata da mutunci wallahi, ka duba fa Aliyu ka gani an fi ƙarfin awa guda da watsar da ni da tayi a ƙasan tiles ɗin nan, amma kalmar haƙuri ta gagara fitowa daga bakinta. alhalin tun duku dukun safiya aka baro gidan uba aka taho gidan ɗana cin arziƙi, to da yake ma dai ɗan Adam butulu ne, amma babu komai akwai Allah ai". Maama tace,"kiyi haƙuri Inna Wuro". "a'a wallahi ba zai yiwu ki cuce ni ba ki bani haƙuri, ke dai je ki kawai da mugun halinki". Maama ta fice daga ɗakin tana dariya. Aliyu yazo ya kama Inna Wuro don ɗagata, ta miƙe tana faɗin,"ba abin nace zan bawa Zainabu shawara ba tace zata ƙullace ni, ko kuma ta zage ni, amma da sai in ce ku kai yarinyar nan gidan ruƙiya zance na domin Allah kenan". Aliyu yay guntun tsoki,"zancenki kenan aljanu". "to kaji ba, ina kuma ga uwarka na faɗawa. yanzu in ace jikar Falmata ce wallahi kaina tsaye zanje in bata shawarar nan. yanzu kai Aliyu ban da kai ma dai halin uwarka ka yo na rashin son gaskiya tsakani da Allah ai ka san wannan ƴa dai tana da iskokai". yay mata wani kallo yana nufar kujera ya zauna,"babu wani zancen gaskiya tun da ba gani kika yi ta tayar ba". "to Aliyu har sai ta tayar za'a san tana da aljanu, ina batun watsota da suke yi a guje fa?, haba a duba lamarin nan dai. ni ko da kaji na faɗi haka ba wai sonta ne bana yi ba wallahi". Aliyu ya ɗauki remote yana dannawa yace,"to ba wasu aljanu, kije ki duba ɓarna tayi miki". yana yin shiru tai hanyar ɗakinta cikin hanzari tana maganganu. kuma tana shiga ɗakin ta tarar da plastic bucket ɗinta yashe a tsakiyar ɗakin, murfinsa a tsakiyar gado yayin da aka yashe rabin dubulan da alkakin da ke cikin botikin. ta ɗora hannu a saman ka kafin ta zube a gefen gado ta zabga salati. "Jikar Zainabu ko masifa, to wallahi ba zai yiwu ba dole ma ƴar nan ta bar gidan nan yanzu babu ɓata lokaci, tun da dai gida Ɗana ya gina shi ba Zainabu ba, ina dalili jarabar sata har cikin ɗakina". Aliyu na tsaye bakin ƙofa ta kalle shi tace,"ashe kasan hali shiyasa kace in zo in duba dukiyata, to kuwa dai ban yafe ba ka faɗawa Zainabu da shi uban yarinyar". bai kulata ba ya sauke wayar kunnensa ya nufi gadon don tashin Farha, wacca ke ta bacci bama ta san wainar da ake toyawa ba. yasa hannu ya shiga tashinta, ta buɗe ido a hankali, ganinsa yasa ta miƙe zaune babu shiri tana murza idanuwa. Inna Wuro da ke gyara bokitinta tana lissafa dubulan da alkakin da ke ciki tace,"da yake kai ne ai kaga ta tashi, ni kuwa da nake ƴar iska idan na tasheta ai sai dai ta yarfo min zagi. ba abin na bawa iyayenta shawara ba su ƙullace ni, amma wannan ƴa ai da gani ta narki ruwan mahaifa, ya kamata kuma a fita da ita ƙasar waje su fasa kanta su kwashe shi, shi Yusufun da ike karatun likitancin banza da wofi yay ai ya kasa gane ƴarsa ta kwankwaɗi ruwan mahaifa". Farha ta sakko akan gadon tana ƙunƙuni ta fita daga ɗakin. direct part ɗin Ammi ta wuce, tana shiga parlo ta tarar da Ammi na cewa da Maama. "wa ya faɗa miki ana taɓa kayan Inna Wuro, salon dai kija min jarfa. yanzu idan ta fara mita ta dinƙa yi kenan har sai an biyata kayanta, duk abin da kika ga tsohuwar nan ta ajiye a lissafe kayanta yake". Maama ta turo ɗan ƙaramin bakinta, ta warware mayafin jikinta tana fito da uban dublan da alkakin da ta kwaso, ta buɗe leda tana zubawa aciki tana faɗin,"Ammi to ba ita bace nace ta bani sai ta ɗau guda ɗaya tal ta ban, ni kuwa tana fita na ɗauki rabona". Ammi ta girgiza kanta,"to ai kuwa sai kiyi ki zuba a ledar ki ɓoye kafin ta biyo bayanki, don wallahi tazo wajen nan sai dai ku yi asararsa". cikin sauri kuwa ta juye shi cikin leda ta saka a jaka. kuma kamar jira sai ga Inna Wuro ta faɗo ɗakin tana faɗin,"to ina Zainabun?". su ka haɗa ido da Ammi da ke kan kujera tana danna remote wurin sauya channel. Inna Wuro ta banka ma ta harara kafin tace,"ban ce fa lallai sai kin gaishe ni ba. saƙon Amadu nazo isar miki, yace wannan aljanar jikar taki ta tattara komatsanta ta bar masa gida kafin ya dawo, idan kuma kika yi kuskuren da yazo ya sameta acikin gidansa to sai dai kotu ta raba shi da iyayenta, saboda shi dai bakin uwa bai bishi ba da za'azo har gida aci mutuncin uwassa". Ammi tace,"ai dama ba kwana zata yi ba, anjima kaɗan za'a zo a ɗauketa". "to shi yafi dai, yauwa ta bar gidan nan tun ba'a ƙure haƙurin ɗana ba, yo me ma na haɗa da ita da zata zo ɓangare na tayi min sata?, da ike ma dai ina da bala'in haƙuri shiyasa, don ma ban faɗa miki ba ne Zainabu, amma ƴar nan ƙafafuna biyu duk ta karya min, ban da Allah ya kawo Aliyu akan lokaci da ban san wa zai jona ni ba in samu in miƙe, amma dai na dai barwa Allah kawai". Ammi tace,"kiyi haƙuri Inna". "yo haƙuri ai dole tunda ni ba fitinanniya ba ce, kawai dai kija mata kunne kar ta ƙara zuwa gidan nan tunda batta da gado". Ammi tace,"to". "yauwa to sai anjima, z
🏠