NOVEL SHARES -

TSUTSAR NAMA BOOK 1 One

Page 314 of 323

asata, sai a yanzu da ake cewa yay mata adu'a suyi sallama ya ji idonsa ya cika, saɓanin jiya da yake a bushe, har yana jin kamar ba zai taɓa zubar da ruwa ba, amma a yanzu tarin ruwan da ya cika a idonsa ba ya jin zai iya dakatar da su, saboda haka sai kawai ya kifa kansa akan ƙirjin gawar, hawayen ya ƙwace, kukan ya kubce, ya shiga rero kuka tamkar ƙaramin yaro, yana kukan jikinsa na girgizawa kamar yanda zuciyarsa ke yi. adu'ar da ake ta cewa yayi ya kasa yi, sai da ƙyar aka iya raba shi da jikin gawar, aka miƙar da shi aka riƙe shi, yana kallo aka ɗauki gawar aka fita da ita, da sauri ya bi bayan su, ya tarar da su su na saka gawar a cikin makara. abinda ya saka shi ƙara rikicewa, sai ya tsinci kansa da yiwa Allah godiya da ƴaƴansa ba su tsinci ganin wannan lokacin ba. ƙarfe sha ɗaya dai-dai aka yiwa Fillo sallah, a cikin ƙaton compound ɗin gidan Alƙali Dikko, bayan gama sallar gawar aka ɗauƙi makarar aka fita da ita daga gidan, Turaki na sahun gaba, ƙafafunsa ke jansa ba shi ne yake tafiyar da su ba, yayin da hannunsa guda ɗaya yake cikin na Bello ya riƙe shi da kyau, saboda gudun faɗuwarsa. a lokacin da aka isa maƙabartar, Hamid da su Yusuf da Baffa su ne suka fito da gawar daga cikin makara, Bello ya kama hannun Turaki ya kama kan gawar sannan aka sata a cikin ramin ƙabarinta, yana kallo ana fuskantar da fuskarta zuwa ɓarin gabas, yana kallo aka ɗauko fasassun tukwane aka jejjera a saman gawar, kafin daga bisani yaga ana zuba ƙasa ana toshe ko'ina, yana jin muryoyin da ba zai iya tantacewa ba na faɗin a toshe kowacce ƙofa, yana kallo bayan an gama rufe gawar ruf da ƙasa aka yayyafa ruwa a samanta, sannan aka ɗauko allon shaida aka dasa a wajen kan, allon da yake iya karantawa, komai yana faruwa kamar dai sati biyu da suka wuce. sunan da ke jikin Allon ɓaro ɓaro, sunan matarsa, sunan abar ƙaunarsa, wannan Fulanin tasa, wannan Fulanin da yake jin ba zai iya rayuwa ba a duk san da babu ita a tare da shi, yau shi ne a gaban ƙabarinta, da shi aka kawota, yana kallo aka sakata cikin rami bai iya hanawa ba, bai iya buɗar baki yace a'a ba, bai iya motsawa ba balle ya riƙe gawar. *Marigayiya Halima Muhammad Hayyo(Fulani), Allah ya jiƙanki da rahamarsa, 03/10/2022.* kamar hakan allon ke ɗauke da rubutun cikin manyan baƙi, ji yake kamar ya fincike allon ya jefar. a hankali ya dawo da tunaninsa ɓangaren da yaji ana doguwar adu'a, sai ya fara kallon kowa ɗaya bayan ɗaya, kowa a tsugune yake ya ɗaga hannunsa, sannan Dr Yusuf da Hakim da Khaleel idanuwan su na hawaye, sai Baffa da Daddy(Baban su Dr Yusuf) fuskarsu fayau, sai ya mayar da kallonsa kan ƙabarin, shi ma ya ɗaga nasa hannun, ya shigo jero tarin adu'a wa ruhin matarsa, yi yake yi yana maimaitawa, har zuwa lokacin da yaji takun tafiya alamu na ƙafafu sun fara barin wajen. yana ji mutanen da ke kusa da shi su na tashi, kuma kafin kowa ya tafi sai an zo an dafa kafaɗarsa ance masa,"Allah ya jiƙanta, Allah ya bada haƙuri". da haka da haka sai da ya tsinci babu kowa a kusa da shi, sai shi kaɗai da yake zaune yana kallon ƙabarin ya kasa sauke hannunsa, har sai da Bello ya zo ya dafa shi yace,"kayi haƙuri ka tashi mu tafi". sai yaji Khaleel ma na ce masa,"Hammah kayi haƙuri". kawai sai ya saki kuka me ƙarfin sauti, ya kai hannunsa ya ɗora akan ƙabarin, a hankali yace,"insha'Allahu zan yi duk abin da kika ce, zan kula da yaranmu, zan ba su tarbiyya, zan saka su a makarantar da kika faɗa, ba zan bari su yi kuka ba, ba zan sa suyi kuka ba, ba zan bari su shiga cikin ƙunci ba, ba zan bar su suyi maraici ba, zan riƙe amanar da kika bar min, nayi miki alƙawari, zan kuma cika miki shi tabbas. don Allah ki yafe min da duk laifin da nayi miki, don Allah Fulani Nah, ki ce ina gaida Maama". Bello da Khalil suka kama shi ya miƙe. suka riƙe shi suka fara tafiya domin barin cikin maƙabartar, sai da suka zo bakin ƙofar fita ya juyo yana daɗa hango kabarin, yana faɗin,"zan dinga zuwa kullum ina gaishe ki, zan dinga zuwa kullum ina yi miki adu'a, idan Aayan ya girma zan dinƙa kawo miki shi kina saka masa albarka, na gode Fulani Nah, sai anjima kinji ƴar aljannah". komawar su gida suka tarar da ɗumin dandazon jama'a acikin rumfunan tanfol ɗin da aka yi kusan guda biyar, kai tsaye cikin gidan ya wuce bai tsaya a waje ba, yana shiga ya fara karɓar gaisuwar ta'aziyya daga mutane, ba wani ganin su yake yi ba, don ba ya gani da kyau. ya ratsa ta cikin falon Mum ya haye sama, daga ƙofar ɗakin nata ya tsaya yana kallon Nihal da Ilham da ke goye da marayun jariransa, sai ya shiga ciki ya kunto yaran daga bayan su da kansa, ya fito ya bar ɗakin, ya kuma ratsa mutanen dake parlon ƙasa ya fice daga sashin gaba ɗaya. kai tsaye ɓangarensa ya nufa, ya buɗe ɗakinsa ya shiga, ya zauna akan gado tare da jinginar da kansa jikin gadon, ya kwantar da macen a ƙirjinsa, namijin kuma ya ɗora shi a kan ƙafafunsa. "your mum is no longer with us, she is gone and she is never coming
🏠