a ɗauke da gawarta, a lokacin ya san kallonta kawai yake yi, sai kuma yaji kukan jariran da ke hannunsa na tashi, kukan da ya ƙara haddasa bugun zuciyarsa, kukan da ya kaishi ƙololuwar tashin hankalin da har bai san lokacin da yanke jiki ya faɗi ba, ya san dai tare da yaran ya faɗi, amma bai san wanne hali shi da su suka shiga bayan faɗuwar tasa ba.
don haka tun bayan faɗuwar tasa tsawon minti goma kenan a yanzu, ƙoƙari ake tayi wajen ganin ya dawo hayyacinsa, kuma da taimakon Dr Yusuf ya farfaɗo, sai dai kana kallonsa kasan baya cikin hayyacinsa, idonsa na tsaye ne a waje ɗaya ƙyam ya zama kamar gunki, cikin ransa ji yake ina ma bai farfaɗo ba shi ma ya mutu, har cikin zuciyarsa ji yake ina ma yabi bayan Fulaninsa da Maama, duk da cewa baya so ya rabu da yaransa, to amma bai san ta yanda zai fara rayuwa tare da yaran ba alhalin mahaifiyarsu bata raye, yana tsananin tausayin su, don haka a yanzu babu abin da yake so illa ya mutu shi ma, baya so yaci gaba da rayuwar sam.
kamar daga sama mutanen parlon suka jiyo muryarsa na faɗin,"Wannan wacce irin jarabawa ce ubangiji yake yi min?, laifin me na aikata da za'a jarabce ni irin haka?...".
Baffa yay saurin saka hannu ya rufe masa bakinsa.
"kar ka yi saɓo Muhammad, kar ruɗani yasa ka fita daga imaninka, kayi haƙuri, ka yi tawakkali ka roƙi Allah ya baka dangana, kayi haƙuri komai muƙaddari ne, ka roƙi Alah ya baka ikon cinye jarabawarka".
Turaki ya shiga sauke numfarfashi, ya shiga jan mazaunansa har ya ƙarasa gaban gawar da yake gani, ya ɗaga mayafin ya ruƙo hannunta.
"Fulani Nah! don darajan Allah da Annabinsa ki tashi, na yarda ki tashi ni sai na tafi, ko kuma mu tafi tare, ba zan iya rainon yaranmu ba ni ɗaya, ban san me zan ce musu ba a san da suka tambaye ni ke".
sai kuma ya kifa kansa kan gawar yana ambaton,"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un".
faɗa yake yana ƙara maimaitawa, yana girgiza gawar, gani yake tamkar idan yana hakan zata farfaɗo, kamar zata dawo duniyar su ci gaba da rayuwar su tare, su raini ƴaƴan da Allah yaba su ciki kyakykyawar kula da tarbiya, idan yaji yaran sun yi kuka sai ya shiga girgiza kansa yana faɗin Allah ka sassauta min, Allah tayi min tsauri, Allah kaji tausayina.
duk sai ya koma kamar wani taɓaɓɓe, sai maganganun kawai yake yi, idan aka ce yay haƙuri yay ƙoƙarin cin jarabawarsa sai yace ba zai iya ba, tayi masa tsauri, da farko an ɗauke masa Maama, mutuwarta bata gama sakinsa ba an ɗauke masa Mata, sannan an bar shi da marayu, marayun da ko nonon uwarsu ba su samu damar sha ba, to ta ina zai iya ɗauka?, ta ya ma zai iya cinyewa?
haka akaita rarrashinsa amma inaaaa, a lokacin da ya rasa Maama ganin yake idan aka cire Mum to duk wata mutuwa da zata zo masa zai ɗauketa, zai iya ɗauka, but a yanzu da ya rasa matarsa, uwar ƴaƴansa sai yaga abun ba haka ba ne, da wuya, da zafi, ba zai iya da wannan jarabtar ba me tsayawa a zuciya.
a wannan dare dai waɗanda suka sami yin bacci ƙailan ne, hatta Ilham sai ɓarawon bacci ne ya ɗauketa, domin sosai mutuwar ta taɓata, a ɗan sabon da suka yi Fillo ta shiga ranta, don tun bayan da Allah ya ganar da ita ta koma yiwa Fillo kallon ƙanwa ta jini ba wai kishiya ba.
Hajiya Ramla kuwa na kan ɗanta, idan tayi rarrashin tayi rarrashin sai taji tana taya shi kukan da ya kasa yi. haka suka kwana ba su runtsa ba, yana riƙe da hannun gawar, yayin da jariran ke jikinsa su na bacci, waɗanda aka rarrasa da ƙyar suka daina kuka har baccin ya ɗauke su, waɗanda har gari ya waye ana tunanin wanda zai shayar da su.
washegari ƙarfe goma na safe an gama haɗa gawar Fillo, gawar tana tsakiyar parlon na Hajiya Ramla cikin sutturarta, cikin wannan farin ƙyallan da ke jiran duk wani mai rai, mahaifiyarta da Yayanta da Kaka da Dada su na gaban gawar su na kuka, musamman Ummi wacca ake ta cewa su yi sallama, tayi mata adu'a domin wannan ita ce sallama ta ƙarshe da za su yi.
"Allah ya jiƙanki Halimatu, Allah ya yafe miki kurakuranki, Allah ya baki Aljannatul firdausi, Allah ya karɓi shahadarki, Allah ya karɓi ruhinki cikin daraja, Allah yasa Manzon Allah ya karɓi baƙuncinki, Allah yasa mutuwa ta zamto hutu a gareki, Allah ya lulluɓeki da rahamarsa da gafarsa, haƙiƙa ba ki yi min komai ba, na yafe miki duniya da lahira, abin da kika bari Allah ya kula miki da su, Allah ya basu haƙuri da juriyar rashinki. sai mun taho muma".
aka shigo da Turaki, ya zauna shi ma agaban gawar, yana jin sautuka na shiga kunnensa, sai dai a lokacin babu abin da ƙwaƙwalwarsa ke iya ganewa, har yanzu ya kasa karɓar mutuwar matarsa, ganin komai yake yi tamkar shirin wasa, tamkar shirin film aka haɗa don kawai a girgiza shi, don kawai a gwada irin ƙarfin soyayyar da yake yiwa Fulaninsa.
"Muhammad ka yi mata adu'a, kuyi sallama Muhammad kaji".
tun daren jiya, tun lokacin da labarin mutuwar matarsa ta riske shi, da zaman kwanan da yay agaban gawar, zuwa wayewar garin yau da ya ƙara tabbatar da ya r