ikita, ba zai ce ga lokacin da ya miƙe ba, ya dai tsince shi ne tsaye akan ƙafafunsa yana kallon jariran dake hannun nurses ɗin, bai san me yake ji a zuciyarsa ba, amma dai ya san bakinsa ya kasa rufuwa, ya miƙa hannu ya fara karɓar namijin, sakanni uku yana kallon yaron me kama da shi sak kafin ya miƙa shi ga Dr Yusuf da ke tsaye a kusa da shi, sannan ya daɗa karɓar macen da ita ce ƙarama, kuma a lokacin da ya ɗora idonsa akanta a lokacin Doctor ɗin yace da shi,"I am very sorry to tell you that your wife is no more, Allah yayi mata cikawa, ina yi maka ta'aziyya Allah yaji ƙanta da rahamarsa".
a maimakon rufewar da idanun Turaki ke shirin yi sai yaji sun maƙale akan jaririyar da ke kuka a hankali, jaririyar da yake hasko fuskar mahaifiyarta a fuskarta.
sai kawai yaji furucin likitan na maimaituwa acikin kansa,_"your wife is no more"._
sai yaji kalaman likitan su na ƙara tafiya a hankali, yayin da yake ji su na barin cikin kunnensa har zuwa cikin kansa da zuciyarsa in da suka samu masauki, don ya kasa gane ta yadda zai karɓe su balle har su yi ma'ana a cikin ƙwaƙwalwarsa.
Fulani ta mutu?, yana nufin Fulaninsa ta mutu, Fulani ta mutu!, Fulanin da suka yini tare yau, to ta ya zai yarda da hakan?.
sai kawai ya kutsa ta tsakiyar mutanen da ke gabansa ya faɗa cikin tiyata room ɗin still yana riƙe da jaririyar, yana shiga ya hangota an rufeta, rufewa tana nufin lulluɓewa har fuska, irin lulluɓewar da ya gani akan Maamansa sati biyu da suka wuce, irin lulluɓewar da yasan mamaci kawai ake yiwa, irin lulluɓin nan da ake yiwa gawa kaɗai.
Turaki ya tsaya cak tamkar mutum mutumi, idonsa na kallon gawar, yaji guiwoyinsa sun yi sanyi ƙalau, irin sanyin da suka kasa cigaba da ɗaukar sa, don haka sai ya nemi bango ya dafe gudun kar ya faɗi jaririyar da ke hannunsa ta cutu, haka ya dinƙa jan ƙafa yana dafe da bangon har ya ƙarasa gaban gawar, a lokacin ƙafafunsa suka kasa ci gaba da ɗaukarsa ya zube a wajen, ya damƙi mayafin da aka lulluɓeta da shi, a hankali ya shiga adu'ar.
"Allah ba yanzu ba, Allah ko don waɗannan jariran, zuwan su duniyar kenan Allah, Allah ka sauya musu wannan ƙaddara ya zama ka ɗauke ni ba mahaifiyar su ba, sun yi kaɗan da irin wannan jarabawar, Allah don Allah ka dawo da Fulani ka ɗauke ni, Allah kar kasa Fulani ta tafi ta barmu, Allah ka tausaya mana ba zamu iya ɗauka ba,Allah ka tausaya mana don masoyinka fiyayyan halitta, Allah don son da kake yiwa Annabi Muhammadu SAW".
sai ya kalli jaririyar da kukanta ya fara yawa yace,"Allah'n mu ka tausaya mana, don Allah Allah ka juya wannan ƙaddarar, ka ganta Allah tana buƙatar nonon mahaifiyarta a halin yanzu, idan kace ka ɗauketa bata da me bata abincinta, Allah ko ba don ni ba, don jariran nan Allah ka tausaya mana, Allah jarabawar tayi mana girma, a sauya mana, a dawo da Fulani a ɗauƙe ni Allah".
sai yayi ƙarfin halin miƙewa ya hau kan gadon ya zauna, zama sosai har da miƙe ƙafa, ya ɗaga mayafin da aka rufeta da shi ya buɗe fuskarta, da farko daskarewa yayi a yanda yake, sai kuma yayi blinking idonsa, saboda ganin kamar likitocin sun yi makuwar saƙon da suka faɗa masa, domin wannan ba fuskar gawa ba ce, wannan fuskar ta me bacci ce, gata nan fess da ita, ta ƙara yin wani irin kyawun da bata taɓa yi masa ba, fuskarta ta ƙara yin doguwa, hakama hancinta kamar ba nata ba, ya ƙara yin tsaho sosai, fuskarta sai annuri take.
a sanda ya lura da rashin motsin bugawar zuciya a ƙirjin matarsa, a sannan ya kamo hannunta ya ƙanƙame a ƙirjinsa ya haɗa da jaririyar, yana jin irin yanda zuciyarsa ke huci tana huda ƙirjinsa tana neman fashewa.
shi musulmin ƙwarai ne ya san mutuwa, ya yarda da ita, so dole yay accepting jarabawarsa, dole ya yarda da ƙaddadararsa, yanzu ya tabbatar da likitocin ba ƙarya suka yi masa ba, ta mutu, ta tafi in da Maama ta tafi, ta tafi in da ba'a dawowa.
sai kawai ya kwantar kansa akan ƙirjin gawar tare da rufe idonsa, yana jin wani irin bala'in kaɗaici ya lulluɓe shi, yana jin mugun tausayin kansa, yana jin tamkar shi ɗaya ne ɗan Adam ɗin da yay ragowa yanzu a duniya, sai yaji ina ma shi ma tasa zuciyar ta daina motsawa tamkar ta Fulaninsa, shi ma ya koma gawar ko ya daina jin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa, yana jin kamar ya zama gawar ya bi bayan matarsa masoyiyarsa, ya bi bayan macen da ta dinƙa kasada da ranta domin ceto rayuwarsa.
a haka yay kissing ƙirjinta, tabbas wani tashin hankalin yafi gaban kuka, domin a yanzu ya kasa yin kukan, alhalin kuma kukan yake so ya yi.
wacewar mintuna ashirin da biyar, a lokacin ƙarfe ɗaya da rabi na dare, acikin parlon na Hajiya Ramla, gawar da aka rufe na shimfiɗe akan carpet, in da a hankali sautin wasu muryoyi ke fita da kuka wajen sanar da mutuwar da akayi.
a wannan lokacin Hajiya Ramla da Baffa da Boɗejo da Ilham na kan Turaki, wanda ya sume tun a dawowar su, tun a lokacin da suka dawo gida yake tsammanin zai ga Fulaninsa ta fito da ƙafafunta, amma sai yaga an fito daga mota wasu n